Ta’aziyyar Malam Uba Ahmad Ibrahim Jos
Hakika dukkan mai rai mamaci ne, kamar kuma yadda masu hikimar zance suka ce kowane mahaluki ba ya wuce lokacinsa. Ma’ana, babu wanda zai mutu sai lokacin mutuwar tasa ta zo, duk kuwa da cewa babu wanda ba zai mutu ba. Haka al’amarin ya faru a ranar Juma’ar da ta gabata, wato 11 ga watan […]
Hakika dukkan mai rai mamaci ne, kamar kuma yadda masu hikimar zance suka ce kowane mahaluki ba ya wuce lokacinsa. Ma’ana, babu wanda zai mutu sai lokacin mutuwar tasa ta zo, duk kuwa da cewa babu wanda ba zai mutu ba. Haka al’amarin ya faru a ranar Juma’ar da ta gabata, wato 11 ga watan nan, ranar da mashahurin dan jarida kuma malamin Islama, Malam Uba Ahmad Jos ya koma ga mahaliccinsa.
Marigayin dai ya rasu ne yana da shekara 51 a duniya, shekarun da al’ummar da suka san shi suka tabbatar da cewa babu shakka ya gudanar da su cikin tawali’u da bautar Allah, tare da hidimar kyautata wa al’umma.
Kamar yadda tarihinsa ya nuna, marigayin mutum ne shi wanda ya daure wa harkar ilimi gindi. Ta kai ga duk rayuwarsa cikin neman ilimi take, domin kuwa idan ma ba ka same shi yana karatu ba, to kuwa za ka same shi yana karantarwa.
Babbar alamar da ta kara tabbatar da cewa shi mutumin ilimi ne ciki da waje, shi ne yadda tun da farko ya tsallake Najeriya, ya tafi kasar Sudan domin neman ilimi. Ya tafi ne a cikin shekarun 1980, inda daga bisani ya kara yin tafiyayya zuwa Jami’ar Al-azhar da ke kasar Masar.
A lokacin da yake dalibta a Masar, jarumin dan jaridar bai zauna haka nan ba, domin kuwa sai ya kama aikin da ke da nasaba da fadakarwa da nusarwa, wato aikin jarida. A can ne ya yi aiki da Gidan Rediyon Alkahira, sannan kuma ya zama dan rahoton Sashen Hausa na DW da ke Jamus. Ta hanyar wannan tasha ce ma ya shahara kuma ya yi suna, musamman wajen kwarewarsa ta fannin sanin al’amuran Gabas Ta Tsakiya.
A lokacin da ya kammala zamansa a Masar, bayan ya kammala karatunsa na digirgir (Phd), da ya dawo gida, sai ya fara aikin koyarwa a Jami’ar Jihar Nasarawa. Daga bisani kuma ya koma Jami’ar Jos, inda ya yi aikinsa na koyarwa a Tsangayar Larabci da Ilimin Addinin Musulunci. Aikin da yake kan yi ke nan, a lokacin da mai rabawa ta raba.
Kamar yadda Muhammad Tanko Shittu Jos ya ba da shaida kan marigayin, a lokacin da yake rubuta ta’aziyyarsa gare shi, ya nuna yadda Uba Ahmad ke kishin gaskiya da mai gaskiya. Ya bayar da misalin abin da marigayin ya taba fada masa a kan haka; inda ya ce masa:
“A matsayinka na dan jarida, ya zama wajibi ka yi iyaka kokarinka wajen fadin gaskiya kuma a matsayinka na dan jarida ta bangaren takarda, dole ne ka tabbatar ka fadakar da al’umma.”
Marigayin, kamar yadda shaida ta tabbatar, ba ya gajiya idan dai harka ce ta ilimantarwa. Yakan shiga makarantun yankinsa ya koyar kyauta, kamar kuma yadda yake gabatar da jawabai ko laccoci ga al’umma kan abin da ya shafi darussan addinin Musulunci ko na fadakarwa game da al’amuran yau da kullum da sauransu.
Marigayin ya rasu ne ya bar mata biyu da ’ya’ya takwas. Uwargidansa, A’isha, wacce suka yi zaman aure na tsawon shekaru talatin, ta bayyana cewa: “Tun lokacin da marigayin ya dawo Najeriya da zama, babu abin da ke burinsa sai na yadda zai tallafa wa al’ummarsa ta hanyar da Allah Ya hore masa. Ba ya da lokaci na kashin kansa, a kullum za ka same shi ko dai yana karatu ko kuma kan hanyarsa ta zuwa makarantu domin karantarwa kuma kyauta. Muna godiya ga Allah bisa haka kuma tun da ya rasu muna addu’ar Allah Ya jikansa da rahama.”
A yayin da yake bayani a lokacin jana’izar marigayin, Shugaban Al’ummar Musulmi na Jami’ar Jos, Farfesa Muslihu Tayo Yahaya ya bayyana cewa shi mutum ne wanda ya kasance babban jari ga jami’ar da kuma al’ummar Musulmin duniya gaba daya.
“Mun amshi labarin rasuwarsa cikin jimami, musamman saboda kokarinsa da sadaukarwar da yake wajen yi wa jama’a hidima. Allah ne kadai Ya san irin gudunmowar da ya bayar ga al’ummar Musulmi. Muna rokon Allah Ya saka masa sannan ya lullube ruhinsa da rahama.” Inji babban malamin.