Ta’aziyyar Marafan Sakkwato Alhaji Umaru Shinkafi
Na dade ina jin labarinka, na kuma karanta wasu daga cikin rubuce-rubucen da ya shafe ka, ka dade kana burge ni, musamman yadda na ga kana girmama na gaba da kai, kamar yadda na ga a gabana kana yi wa marigayi Alhaji MD Yusufu, Tsohon Sufeto Janar na ’yan sanda. Ban matsa kusa da kai […]
Na dade ina jin labarinka, na kuma karanta wasu daga cikin rubuce-rubucen da ya shafe ka, ka dade kana burge ni, musamman yadda na ga kana girmama na gaba da kai, kamar yadda na ga a gabana kana yi wa marigayi Alhaji MD Yusufu, Tsohon Sufeto Janar na ’yan sanda.
Ban matsa kusa da kai ba sai lokacin da shirye -shiryen kaddamar da littafin rayuwar MD Yusufu na Hausa ya taso, wanda kai ne mataimakin shugaban shirye -shiryen, ni kuma ne na zama sakatare yayin da Alhaji [Dokta] Ibrahim Coomasie, Shugaban kungiyar Tuntuba ta Arewa. [ACF] ya kasance shugaba.
Mun rika tattaunawa da kuma waya a kan yadda taron ya kamata ya kasance. Wannann ya kulla dangantakarmu da kai, har lokacin da Allah ya sa ka bar duniya. Wanda kafin rasuwarka mun shaku shakuwar da ta kai ga har akwai lokacin da ka ce ina ma mun san juna tsawon lokaci, saboda yadda muka fahimci za mu iya amfanar juna.
Na sanka a matsayin wanda komai kake son ganin an yi shi tsaf yadda yake, kuma yadda ya dace. Kuma kana son a samu kusan kashi casa’in da doriyar na makin din duk abin da aka sanya a gaba. Kana kuma da takatsantsan ga duk abin da za ka yi..
Ka taba rike ni awa uku ana bugawa da gyara wata takarda mai shafi uku kacal. Don kana son lallai kafin ta fita sai ta samu tabbacin inganci. Ina iya tunawa na zo gidanka a Abuja daga gidan MD Yusufu da niyyar ka duba takardar, kuma ka sa mata hannu daga gidanka niyyata in wuce Kaduna.
’Yan gidanka suka shaida mini cewa, in dai har na zo da takarda in soke maganar barin Abuja yau. Tabbas abin da ya faru ke nan. Sai da na yi awa uku zuwa hudu.
Kana da sha’awar a magana a rika bambance maka tsakanin ra’ayi da fahimta da sharhi da kuma gaskiyar labari. Me ya faru, ya aka yi ya faru? Ya faru yadda ya faru. Kafin mai bayar da labari ya yi nazarin duk abin da zai fada a karin bayaninsa.
Kana sauraren magana atsanake, kuma in za ka yi tambaya. Tambaya ce. Wadda amsarta za ta kasance dole ka fadi gaskiya. In ma ka yi wa gaskiyar kwaskwarima to za ka gane mutum. Wani lokaci kana mayar da tambaya ga duk amsar da ka samu.
Idan mutum ya fahimci abu ba daidai ba, ka kan gyara masa. Ka ce a’a, ba haka yake ba, sai ka fada masa gaskiyar yadda abin yake. In kuma ka ga bai cancanta ya sani ba sai ka ce, abin da ka sani ba haka ba ne.
Kana da taka tsantsan wajen yarda da kowa. Kodayake ka taba fada mini wata magana da na ji dadinta. Ka ce na yarda da kai ne saboda wanda yarda da kai nasan bai yarda da mutumin banza, shi ne MD Yusufu. Na tuna muna yin wata magana ne da ta shafi kasar da halin da take ciki. Ka fada mini. Wasu zantuttuka da ka ga na yi mamakin da ka yarda ka shaida mini su. Sai ka ce ka da ka yi mamaki. Malam kamar yadda kake kiran MD Yusufu ya yarda da kai, nima shi ya sa na yarda da kai.
Ina mamakin yadda kake da kokarin mayar da amsar duk wani sakon waya da ya shigo wayarka. Za ka karanta kuma za ka bayar da amsa. Daka buda waya kamar yadda naga kana yi a gaba na . duk wani sakon waya sai ka karanta shi. kuma duk wani kiran da ba ka amsa ba, sai ka duba shi, wani ka kira,wanda ba ka gane mai kiran ba, kuma ka kyale.
Ba ka wasa da addini, ba ka kuma wasa da hakkin mutum. Ka taba bugo mini waya karfe daya na dare. Ka ce in bai wa wani da ya yi mana wani aiki kudinsa, kafin tara na rana:”Ka kira shi ka biya shi cikin iko ka yi maganar.’’ Da wajen biyu na rana kuma in ga sakon ka a waya ka rubuta cewa, ‘ka yi abin da na ce. Kuma na gode.’
Hirarka ta karshe da ka yi da jarida, ni na roke ka. Kuma ka amince. Bayan ka yi mini tambayoyi na ba ka amsa. Daga baya ka ce. To kar tattaunawa ta wuce a kan Marigayi Sardauana. Ita ce hirar da aka yi, kuma aka buga a jaridar BLUEPRINT. Da hirar ta fito ka shaida mini cewa. lallai ka ji dadi ba inda aka samu matsala a wajen rubuta rahoton.
Allah sarki. Yanzu ba zan kara jin wayarka ba, wadda ka kan bugo mini cikin dare, wadda dana ganta zan sa ruwan shayi da lifton na san hira kake bukata wani lokaci. In mun gama sai dai in dasa da sallar dare zuwa asuba, sai safe, har na saba al’amarin da ya zamar mini jiki.
Kana Ingila kana son ka bugo mini ka ji me kasarka ke ciki. Wata waya da ka bugo ka ce cikin bacin rai, ‘wai Alhaji danjuma da gaske ne an kashe mutane da yawa a Zariya?’ Kafin in ba ka amsa ka ce ina son ka je Zariya ka samo mini tabbacin haka. Tunda ka ce kai kana Katsina.. kana magana cikin mamaki. A maganarka ka rika yin nazarin tsaro a kan wannan al amarin.
Na rika karfafa maka gwiwar ka rubuta tarihin rayuwarka ko na kasar nan, na daga abin da ka sani a tarihinta. Ka taba shaida mini cewa komai naka yana a rubuce a tsanake. Don haka ka da in damu, in lokaci ya yi cikin lokaci kankane za ka iya fitar da shi ga al’umma don su karu da ilmin da ka taskance.
Abubakar Ado mijinyawa, ya shaida mini katafaren mallakin dakin karatunka, wanda Allah bai sa na samu ziyarta ba. Ya fada mini cewa gida ne, wanda wasu dakunan cike suke da littafai, inda wani masanin ilmin dakin karatu ke kula da su. Wasu dakunan kuwa duk jawabai ne naka, wadanda ka yi, tare da rubutunka tun kana dan makaranta. Har zuwa lokacin suna a tsare a ciki.
Wani dakin kuma kyaututtuka ne da aka taba ba ka. Duk an tsara su an jera da rubutun shekara da lokaci da wanda ya ba ka. Wani kuma dakin kaya ne. na tarihi, wadanda suka shafi rayuwarka. Hula da riga da takalmi da zobe da sauransu.
Allahu Akbar; wannan ya sa na gane dalilin da ya sanya ka damu. Kuma ka so ka ga an yi da kammala aikin ginin dakin karatu da ajiye kayan tarihi na MD Yusufu. Ka sha fada mini cewa in aka gama shi.za ku mayar da wajen abin misali da kuma zuwa a yi bincike a duniya.
Kwana uku kafin ka bar duniya, na kira waya in yi gaisuwa, sai daya daga cikin masu jinyarka, ya dauka, ya ce kana barci, ya ce ina cikin ’yan kadan da ka bayar da umurnin in na bugo a dauka, an fada mini cewa kana samun sauki.
Na je Sakkwato ta aziyyarka. Na kuma ziyarci kabarin ka. Ka ji dadi, an rufe ka kusa da mutanen ne da ke kyautatta zaton na kirki ne a wajen Allah. Makabarta wadda ke samun maziyarta sosai. kuma ana yi wa wadanda ke kwance addu’a, wato Hubbaren Shehu Usman dan Fodiyo, Alhaji Umaru shinkafi Allah ya jikanka. Allah ya dayyaba zuriyarka. Amin.
Danjuma Katsina . marubuci / dan jarida. Shi ne Sakataren Cibiyar Bincike da Tattara bayanai ta MD Yusufu, (MD Yusuf Research and Decumentation centre). 08035904408. Email. [email protected].