Ta’aziyyar marubuci, dan jarida, marigayi Bello S. Tangaza

Allah (SWT) Yana cewa: “Kullu nafsin za’ikatil maut.” Ma’ana: Kowane rai sai ya dandani mutuwa.A wannan rubutu, nufina ne in yi ta’aziyya ga marigayi Bello S. Tangaza, wani sanannen dan jarida da ke Jihar Sakkwato, wanda a bana ya cika shekara goma sha daya cif-cif da rasuwa.Idan aka ce dan jarida, ba wai ana nufin […]

Ta’aziyyar marubuci, dan jarida, marigayi Bello S. Tangaza

Marigayi Bello S. TangazaAllah (SWT) Yana cewa: “Kullu nafsin za’ikatil maut.” Ma’ana: Kowane rai sai ya dandani mutuwa.
A wannan rubutu, nufina ne in yi ta’aziyya ga marigayi Bello S. Tangaza, wani sanannen dan jarida da ke Jihar Sakkwato, wanda a bana ya cika shekara goma sha daya cif-cif da rasuwa.
Idan aka ce dan jarida, ba wai ana nufin mai aiki a gidan rediyo ne kawai dan jarida ba. A’a, aikin jarida ya kunshi abubuwa kamar haka: talabijin, jarida, rediyo, mujalla da dai sauransu. Duk wanda mutum ya sami kansa a daya daga ciki, lallai shi ma dan jarida ne. Aikin jarida wani nau’in aiki ne da yake fuskantar kalubale sosai a duniya. Ana samun rahotannin duka, kisa, wulakanci da dauri a gidan yari ko tozartawa daga ko’ina a duniya a kan ’yan jarida, wanda muhimmancinsu yana da yawa sosai. Wanda a duniyar yau, yana da wahala a wayi gari, rana ta fadi ba tare da an ambaci ’yan jarida ba, wala’alla ta wadannan hanyoyin ko kuma ta wasu hanyoyin daban.
Aikin jarida yana fadakar da masu yinsa da kuma masu saurare ko kuma karanta jaridu a ko’ina a duniya. Marigayi Bello S. Tangaza, kamar yadda wadanda suka san shi ke kiransa da suna (BST) a takaice, an haife shi a karamar Hukumar Mulkin Tangaza, a Jihar Sakkwato, a shekarar 1952. Ya yi karatun addinin Islama kamar yadda aka san ’ya’yan Musulmi da yi, sannan kuma ya shiga makarantar zamani. Bayan ya kammala, ya fara aiki da gidan rediyon NBC, wanda daga bisani ya rikide ya koma gidan rediyon Rima, a 1973. A matsayin karamin ma’aikaci ya fara, sannan kuma a shekarar 1988 ya je Legas wajen kwas na sanin makamar aiki, inda sannu a hankali ya ci gaba da samun ci gaba a wurin aikinsa har ya kai matsayin “Babban Furodusa,” wato babban mai shirya shiri. A nan dai gidan rediyon Rima yana rike da wannan matsayin har ranar da Allah (Swt) Ya yi masa rasuwa a shekara ta 2002.
Kamar yadda aka san ayyukan kafafen watsa labarai, misali gidan talabijin, yana da nasa shirye-shirye da yake gabatarwa ga masu kallonsa. Haka kuma gidan jarida, yana da nasa shirye-shirye da kuma rahotannin da masu karanta jarida ke bukatar sani. Gidan rediyo kuma shi ma ba a bar shi a baya ba wajen faranta ran masu saurarensa a ko’ina suke a duniya, duk da cewa yawancin wadanda suke sauraren rediyo suna zaune ne a yankunan karkara. Marigayi Bello S. Tangaza ya gabatar da muhimman shirye-shirye masu kayatarwa a gidan rediyon Rima, wanda jama’a da dama sun amfana da su a lokacin rayuwarsa da kuma ma bayan rasuwarsa. A lokacin da yake a raye, ya kirkiro tare da gabatar da shirye-shirye guda takwas, wadanda shi ne ya shirya su da kansa kuma ya gabatar, bayan wadanda yake ba da gudummawarsa a ciki.
1-A lokacin da yake a raye, ya gabatar da shirin “Tsaka Mai Wuyar Sani.” Wani shiri ne wanda ake yin hira da masu nakasa da marasa galihu, uwa uba da kuma hira da mahaukata tuburan. Yadda yake gabatar da shirin, har jama’a na tambayar ya aka yi yake hira da mahaukata masu dukan jama’a? Wannan wata baiwa ce daga Allah (Swt) da ya yi wa bawansa kawai.
2-Ya gabatar da kasaitaccen shirin nan na “Noma Tushen Arziki,” wanda a dalilinsa ya karade jihohin Arewacin Najeriya da kuma wasu kasashe na Afrika, kamar su Nijar da Jamhuriyar Benin. Kuma wannan shirin ya samu karbuwa sosai, musamman ma a yankunan karkara kuma ta dalilin wannan shirin jama’a da dama suka san cewa Arewa ce tushen noma a Najeriya.
3-Ya gabatar da shirin “Abin Aljihu Na Mai Riga Ne.” Wannan shirin ya zama tsani tsakanin talakawa da masu mulki, inda ake gayyato masu mulki ana karanta masu koken talakawansu, wato karanta maso wasikunsu, su kuma suna ba da amsa kai tsaye; da zummar share masu hawaye kuma gwargwadon hali an samun biyan bukata.
4-Ya gabatar da shirin “Yau Da Gobe,” shiri ne na was an kwaikwayo da Hausa, ake gabatarwa a gidan rediyo, domin fadakar da dubban masu saurare saboda a samu gyaran gurbacewar tarbiyya a tsakanin al’umma. An fadakar da jama’a ta hanyoyi da dama a yayin gabatar da wannan shiri.
5-Sai kuma shirin “Tsarabar Sakkwato,” wannan wani nau’in zabe ne wanda ake gabatarwa a gidan rediyon Rima. Wannan zaben, ana yinsa ne da Sakkwatanci zalla. Misali, ba a karya halshe yanda Bakano ko dan Kaduna ko Bakatsina zai gane kai tsaye, sai dai Sakkwatanci zalla.
6-Ya gabatar da shirin “Zomo Ba Ya Kamuwa Daga Kwance,” wanda yanzu ya koma “Hannu daya Ba Ya daukar Jinka.” Wannan shirin hadin gwiwa ne tsakanin Rima Radiyo da Hukumar Bunkasa Ayyukan Gona Da Taimakon Kai Ta Majalisar dinkin Duniya (IFAD). A lokacin nan, Jabbi Kilgori ne yake shugabantar hukumar a Jihar Sakwato. Shirin ya koyar da samari da jari ga jama’a, musamman ma na yankunan karkara kuma ya ziyarci Jamhuriyar Benin ta dalilin wannan shirin.
7-Ya gabatar da shirin “Zabi Sonka.” Wannan shiri yana da matukar farin jini ga jama’a har yanzu kuma gidajen rediyoyi a nan Najeriya da kuma wasu kasashen duniya suna gabatar da irin wannan zaben, saboda ana sadar da gaishe-gaishen ’yan uwa da abokan arziki kai tsaye a ta gidajen rediyon.
8-Sannan kuma ya gabatar da wani shiri na musamman, wanda ake gabatarwa duk daren kowace karamar Sallah ko kuma babba. Sunan shirin shi ne “Yau Take Sallah Gobe Jajibir.” Ana yin hira da ’yan kasuwa da kuma masu saye domin sanin halin da kasuwannimu ke ciki da kuma halin da masu saye ke ciki, musamman a lokutan Sallah.
Kuma duk yawancin wadannan shirye-shiryen, shi ya shirya su kuma ya gabatar. Wani abu kuma, yawancin shirye-shiryen nan, tare da ni yake yawon hada su, shi ya sa nake da masaniya a kai.
Marigayi Bello S. Tangaza ya koma ga mahaliccinSa a ranar Alhamis (04/07/2002), a kan hanyarsa ta zuwa wajen wani aikin da aka tura shi. Ya rasu ya bar matan aure da ’ya’ya 20, maza 15 mata 5.
Babban dansa, Nura Bello yana aiki a nan inda marigayi ya yi aiki, wato Rima Rediyo, sai Shebatu Bello, wanda shi kuma malamin makaranta ne. Sai ni marubucin ta’aziyyar nan, Bilal Bello, ina aiki tare da Gwannatin Jihar Sakkwato. Sai Suleman Bello, shi kuma jami’in Hukumar Shige-da-fici ne. Sai Shafi’u Bello, dalibi Sokoto Polytechnic. Mata kuma dukkansu suna gidan aure amma daya ta rasu.
Daga karshe, mu iyalan marigayin muna mika kyakkyawar godiyarmu ga mamallaka da kuma ma’aikatan wannan jarida mai albarka, Allah (Swt) Ya saka masu da alherinsa kuma Ya daukaka wannan jarida. Amin.
Bilal, ya aiko da sakonsa ne ta adireshinsa na I-mel: [email protected]

Wakar Gizagawa

Malam Sulaiman Mai Bazazzagiya (08067917740), ya gabatar da wannan waka a ranar Asabar da ta gabata (17-08-2013), a yayin rantsar da shugabannin kungiyar Gizago na kasa da kuma na jihohi, wanda aka gabatar a dakin taro na Muhammad Maccido, Kwalejin Barewa, Zariya
                                   ***
1-Ya Rahamani Rabbana Makadaici,
Kai na rika ni ban rikon bayinka.

2-Rabbi Ta`ala yanzu ga rokona,
Gobe kiyama kai ni gun Manzonka.

3-daha Rasulu shugaban manzanni,
Ka ji na karshen daukacinsu Ma`aika.

4-Wannan rana yau ina yin murna,
Na ga fa baki sun cika mani fuska.

5-Ga su a Zazzau to a nan fa Barewa,
To makaranta ga ta mai albarka.

6-’Ya`yayenta to ciki da Tafawa,
Ga su Gawon ga Murtala ba shakka.
 
7-Ga Shagari duk suna ’ya`yanta,
Har Sardauna gamji ya dara kuka.

8-Baba Ahamad Malami ne nasu,
Nan a Barewa tabbaci ba shakka.

9-Mai yaba kyauta kun ga zai yi tukuici,
Ko fa kadan ne in ya so zai ba ka.

10-Ga fa gizagawa mazansu da mata,
Kowa murna in ka kalli fa fuska.

11-Sun zo taro ne na dai rantsarwa,
Jagororin to gizago naka.

12-Kyawun roko to a dai tuna baya,
Mai ma roko zai tuno kakanka.

13-Ka Bashir to ai Yahuza namu,
Ka ji gizago mai fa yin sassaka.

14-Ka ji silar to kungiyar fa Gizago,
Duk a kasa yanzu ana ta yabon ka.

15-Kai da jaridarku fa kun cirri tuta,
Kai da Aminiya Jaridar taka.

16-Baba Ahamad Jarimi ba tsoro,
To Muhamud ka gaji dai babanka.

17-Bai da kasala ba ya tsoron kowa,
Mun yabi kishinka na al`ummarka.

18-Yanzu Arewa ta zame ’yar bora,
Shi Muhamud Mowa Arewa ya dauka.

19-Dr. Bala dattijo bawan Allah,
Ka ji gizago yau yana gaishe ka.

20-Kun ji masoyin kungiya ta Gizago,
Dr. Bala Allah ya dai kare ka.

21-Can a Kano shi ne ya daidaita su,
Sun yi sahu siffarsu tamkar dirka.

22-Sai Ibrahim kun ji dai Farfesa,
To na Malumfashi muna gaishe ka.

23-Shehin Malam mai fa kwankwancewa,
Kan ilimi sannan a kowace harka.

24-Ka ga a can ai Sakkwato muka sadu,
Mun yi karatu mun fa gogu a gunka.
 
25-Kai mana tarbiyya irin ta yabawa,
Yau Farfesa ga amon shukarka.

26-Wannan shukar yanzu ta yi yabanya,
Ta ji fa taki to zubin hannunka.

27-Rabbi Ta`ala to ya kara fa girma,
To ka zame bC a jami`arka.

28-Ga Farfesa Yusufu Adamu,
Ka ji Gizago yau yana gaishe ka.

29-Ka zo taron nan a birnin Zazzau.
Mun yi ta murna yadda dai muka gan ka.
 
30-Mun yabi aikinka na harshen Hausa,
Rabbi ya kare ka ka kara hazaka.
 
31-Yanzu gizagawa gare ku na juyo,
Masu fa kwazo har rawa sun taka.

32-Yanzu ina dai Muntaka mun gode,
Dabo a kullum dai muna ta yabon ka.
    
33-Ka ji damo shi ba ya cizon kowa,
Dabo a kullum kwanciya gun shuka.

34-Kai ne farkon shugabanmu gaba dai,
Sai Falala yanzun yana bayanka.

35-Shi fa Yunusa mai rikon kwarya ne,
Kun mana aiki Rabbana fa ya saka.

36-Sai fa Kabiru to Sakaina namu,
Kai Sakatare ba kasala gunka.

37-M. K. Adam Gombe na gaishe ka,
Kai mana kwazo lokacin aikinka.
 
38-Yanzu Awal Sharif kasa muka zaba,
Yau jagora duk kasa na bin ka.
 
39-Yau Falala sai dai ka gode Allah,
Tun da Gizagawa suna bayanka.

40-Sai fa ka dage kar ka yi fa kasala,
Ka ga Gizago to tsare hannunka.
 
41-In ka tsare to babu mai damun ka,
In ka sake to za ya sassare ka.

42-Awwal L.K.shi kadai aka zaba,
Can na Ibadan to matemakinka.

43-Malam Awwal sai ka jajirce fa,
Tabbas na san babu wasa gun ka.

44-Sai sakatare yau kana fa ina ne,
danlabaran yanzun na juyo gunka,

45-Ka ga fa ruhin kungiya na gunka,
Sai ka zage ya jarimi na san ka.

46-Na san Zazzau ba rago sha-sha-sha,
Sai dai gwarzo Jarimi ba shakka.

47-Zariya birni ne garin dai Shehu,
dan Idirisu duk muna bayanka.

48-Zariya ilmi ba kamar ta a Hausa,
Har fa Kano ta zo bidan albarka.
 
49-Kun ji Sulaiman Mai Bazazzagiya ne,
Sai wata rana yanzu na gama waka.    

50-Sai wata rana to Gizagawana,
Mui ta zumunci ko`ina fa a san ka.

Bin diddigi: Gaskiyar batun kai hari a Bankin CBN

NAJERIYA A YAU: Lakurawa muka kai wa hari a Sakkwato —Sojoji

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano