Ta’aziyyar Marubuciyar Afirika Ta Kudu Gordimer

A maraicen ranar Lahadin da ta gabata ce marubuciyar nan da ta yi suna wajen yaki da wariyar launin fata, ’yar kasar Afrika Ta Kudu, Nadine Gordimer ta rasu, kamar yadda iyalinta suka tabbatar da haka ga manema labarai a Litinin da ta gabata.Marubuciyar, wacce ta taba samun kyautar Nobel a 1991, wacce kuma ta […]

Ta’aziyyar Marubuciyar Afirika Ta Kudu Gordimer
Ta’aziyyar Marubuciyar Afirika Ta Kudu Gordimer

A maraicen ranar Lahadin da ta gabata ce marubuciyar nan da ta yi suna wajen yaki da wariyar launin fata, ’yar kasar Afrika Ta Kudu, Nadine Gordimer ta rasu, kamar yadda iyalinta suka tabbatar da haka ga manema labarai a Litinin da ta gabata.
Marubuciyar, wacce ta taba samun kyautar Nobel a 1991, wacce kuma ta yi fice wajen rubuce-rubucen gyara dabi’a, kamar kuma yadda ta kasance mai yaki da danniya da zalunci, ta rasu ne a gidanta da ke birnin Johannesburg kuma a gaban ’ya’yanta Hugo da Oriane. Ta rasu ne tana da shekara 90 a duniya.
“Babu abin da ta fi damuwa da shi kamar kasarta Afirika Ta Kudu, da al’adunta da al’ummarta kuma ta kasance mai fafutuka domin ganin sabuwar dimokuradiyyar kasarta ta dore,” kamar yadda takardar sanarwar mutuwar tata ta bayyana.
Gordimer ta kasance wata jigo a fagen rubuce-rubuce, wacce ake darajawa a kasarta da sassan duniya, ta samu suna a fagen rubuce-rubucen da suka hada da kirkirarrun labarai da ke bayyana tsantsar rayuwar al’umma da kuma wadanda ke bayyana salon mulkin tsirarun farar fata da suka yi mulkin wariyar fata a kasarta. Mace ce wacce ke kyamar rashin gaskiya, mai tsattsauran ra’ayi kan tarbiyya.
Mafi yawa daga labarun littattafanta suna dauke da jigogin muhimmancin soyayya, illolin kiyayya da gaba, kamar yadda haka suka faru a yayin mulkin wariyar launin fata a kasarsu, da ya kawo karshe a 1994, shekarar da marigayi Nelson Mandela ya samu nasarar kawo canji, ya zama bakar fata na farko da ya zama Shugaban kasar Afrika Ta Kudu, a karkashin jam’iyyar ANC (African National Congress).
A matsayinta na memba a jam’iyyar ANC, jam’iyyar da aka haramta a lokacin mulkin wariyar launin fata na Turawa, Gordimer ta yi amfani da alkalaminta wajen yaki da wannan dabi’a ta wariya, kamar kuma yadda ta yi fada da mulkin Turawa a kasar tasu na tsawon shekaru, wanda haka ya sanya Turawan suka dora mata karan tsana kuma ta yi bakin jini a idanunsu.
Wasu daga cikin littattafanta da suka hada da A World of Strangers da kuma Burger’s Daughter, duk an haramta su a Afrika Ta Kudu a zamanin mulkin Turawa na wariyar launin fata. Amma duk da haka ba ta girgiza ba, domin kuwa ta ci gaba da gwagwarmayarta ta hanyar rubuce-rubuce a wuraren da ta san za ta yi tasiri.
“Ba zan iya yin shiru game da mulkin wariya ba, a yayin da al’umma ke fuskantar zalunci da rashin gaskiya.” Abin da ta fada ke nan ga kafar watsa labarai ta Reuters, jim kadan kafin ta amshi kyautar Nobel da ta samu a 1991.
A shekarun baya, ta kasance jigo wajen gangamin yaki da cutar kanjamau, inda ta rika yekuwar samar da tallafin kudin magani ga masu fama da cutar. Ta kuma yi yunkuri da dama a wannan fanni, inda ta ja hankalin gwamnatin kasarta domin ta dauki nauyin samar wa majinyatan magani kyauta.
Gordimer, Baturiya ce amma ’yar Afirika. Mahaifinta Bayahude ne, mai kera agoguna, mutumin kasar Lithunia. Ta fara rubuce-rubuce ne tun tana ’yar shekara tara a duniya. A yanzu da rayuwarta ta kawo karshe a tsawon shekaru 90, za a dade ana tunawa da ita.