Ta’aziyyar Sarkin Keffi Alhaji Chindo Yamusa II

Allah Ya yi wa Sarkin Keffi Alhaji Muhammadu Chindo Yamusa II rasuwa a daren Alhamis ta makon jiya, fadarsab da ke Keffi.Sarkin ya rasu ne bayan doguwar jinya da ya yi fama da ita, bayanai na cewa kwana daya kafin rasuwarsa ya samu sauki sosai, har ana tunanin lafiya ta samu ke nan. Cikin dare […]

Ta’aziyyar Sarkin Keffi Alhaji Chindo Yamusa II
Ta’aziyyar Sarkin Keffi Alhaji Chindo Yamusa II

Allah Ya yi wa Sarkin Keffi Alhaji Muhammadu Chindo Yamusa II rasuwa a daren Alhamis ta makon jiya, fadarsab da ke Keffi.
Sarkin ya rasu ne bayan doguwar jinya da ya yi fama da ita, bayanai na cewa kwana daya kafin rasuwarsa ya samu sauki sosai, har ana tunanin lafiya ta samu ke nan. Cikin dare da misalin karfe 2:00 sai ciwon nasa ya yi tsanani, har ya kai ga rasuwarsa.   
An yi jana’izarsa ne ranar Juma’a, bayan Sallar Juma’a, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, a cikin babban masallacin Juma’a na Keffi, fadar masarautar. An yi Sallar, inda limamin masallacin, Malam Muhammed Auwal ya jagoranta, bayan sallar an binne shi a cikin fada.
Galadiman Keffi Alhaji Abdul Usman ya shaida wa wakilinmu cewa marigayin, wanda kafin rasuwarsa shi ne Shugaban Jami’ar Jihar Nasarawa ,ya hau karagar mulki yana da shekara 33, a ranar 11 ga Mayu, 1978;  shekara 37 ke nan da suka gabata. Marigayin ya rasu ne yana da shekara 70 a duniya.
Galadiman Keffi ya kara da cewa marigayin ya rasu ya bar ’ya’ya 27 da mata biyu a duniya.
Jana’izar Sarkin ta samu halartar manyan baki da suka hada da sarakuna da attajirai da kuma wasu masu rike da mukaman siyasa daga sassa daban-daban na kasar nan.
Alhaji Ibrahim Jibrin Usman, Ministan Kula da Muhalli shi ya wakilci Shugaban kasa Muhammadu Buhari. A jawabinsa, ya ce: “Mai girma Shugaban kasa Mahammadu Buhari ya so ya hallarci wannan jana’iza amma hakan bai samu ba saboda wasu dalilai da suka sha karfinsa, don haka ya umurce ni da in zo a madadinsa kuma in mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi,n Alhaji Muhammadu Chindo Yamusa II da kuma  al’ummar masarautar baki daya. Da fatan Allah zai ba mu hakurin rashi. Shi kuma Allah Ya gafarta masa zunubbansa baki daya.”
Shi ma Gwamnan Jihar Nasarawa, Alhaji Umar Tanko Al-Makura ya samu halartar jana’izar, inda ya ce: “Rashin Sarki Chindo Yamusa ba rashi ne na mutanen Keffi kadai ba, a’a wannan rashin ya shafi kowa a Jihar Nasarawa da Najeriya baki daya, domin marigayi mutumin kirki ne mai son bin doka da kuma rikon amana a zamanin rayuwarsa.”
A karshe Gwamnan ya shawarci al’umma baki daya da su yi wa marigayin addu’ar dacewa da makoma mai kyau.
A nasa bangaren, Sarkin Lafiya, Alhaji Mustapha Agwai, ya ce: “Marigayi Sarki Chindo Yamusa babu shakka adali ne, domin zai yi wuya a samu Sarki mai kwatanta gaskiya irin sa, kuma yana son jama’a sosai. Da wannan dalilan ne suka sa Sarkin ya yi farin jini matuka a lokacin rayuwarsa kuma kyawawan halayensa lokacin da yake raye su suka sa ya samu dubban mutane a lokacin jan’izarsa. Don haka muna masa fatan dacewa da Aljannatu Fiddausi gare shi.”
Kwamishinan kananar Hukumoni da Masarautu na Jihar Nasarawa, Alhaji Tijjani Aliyu Ahmad, ya shaida wa wakilinmu irin yadda ya ji a zuciyarsa, lokacin da ya jji an ce Sarkin ya rasu. “Da ma Allah Ya ce ‘kullu nafsi za’ikatil mauti’ wato duk mai rai zai dandani mutuwa. Gaskiya rashin wannan Sarki babban rashi ne a Najeriya baki daya, domin shi mutum ne mai son gaskiya da guje wa karya kuma mutum ne mai son ci gaban al’umma baki daya ko a ina suke. Hakan ya sa marigayin ya samu daukaka kwarai da gaske a zamanin mulkinsa. Saboda haka ina yi masa fatan Allah Ya jikansa da rahama, in tamu ta zo, Alla Ya sa mu cika da kyau da imani.
Manyan baki da dama daga sassa daban-daban na kasar nan, wadanda suka hada da Shugaban Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara da tsohon Ministan Abuja Jeremiah Usaini da tsohon Minisatan Abuja Bala Muhammad kauran Bauchi duk sun kai ta’aziyya ga iyalan Sarkin. Sauran sun hada da Sanata Philip Aduda da tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Ahmad Adamu Ma’azu da sauransu.