Tabar Kolarado Ta Kashe Budurwa A Anambara

Wata budurwar ta mutu bayan ta yi wa tabar kolarado shan Allah tsine uwar mai ƙarya. Budurwar, wadda har yanzu ba a bayyana sunanta ba ta mutu bayan shan tabar ce a karshen mako a Awka, babban birnin jihar Anambra. Wani bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna gawar budurwa a yashe a […]

Tabar Kolarado Ta Kashe Budurwa A Anambara

Wata budurwar ta mutu bayan ta yi wa tabar kolarado shan Allah tsine uwar mai ƙarya.

Budurwar, wadda har yanzu ba a bayyana sunanta ba ta mutu bayan shan tabar ce a karshen mako a Awka, babban birnin jihar Anambra.

Wani bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna gawar budurwa a yashe a gefen titi.

Shaidu da ke tare da ita lokacin da abin ya faru sun bayyana cewa da farko bayan ta sha tabar ta suma.

A dalilin haka jama’a suka ba ta garin rogo da yawa ta sha ta farfaɗo, daga bisani ta ƙara zuwa ta sha tabar.

Sha tabar da ta kara yi ne ya birkita ta, inda har ta riƙa tuɓe kayanta tana watsarwa, mutane suka riƙa bin ta suna rufe mata tsiraici kafin daga bisani ta kwanta ta ce ga garinku nan.

Da aka tuntubi kwamandan hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a Jihar Anambra, Daniel Onyishi, ya bayyana irin wannan lamari a matsayin daya daga cikin manyan illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma yadda suke halaka matasa.

A cewarsa, tabar kolorado na da hatsarin gaske ga lafiyar al’umma, da suke lalata rayuwa, su mayar da mutum mara amfani a cikin al’umma.

Ya bayyana cewa ‘kolorado’  tana zama wani irin bala’i da in mutum bai sha ba, sai ya ji kamar zai mutu.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja