Tabarbarewar Arewa: Wasika zuwa ga Wada Nas
Amincin Allah ya tabbata a gare ka da sauran bayin Allah nagari da kuke tare.Ranka ya dade na dade ban rubuto maka wasika ba, ba don na manta da kai ba ne sai don abubuwan da ke faruwa a Najeria sun wuce hankalin mai hankali. Ka yi hakuri, ban zo don in tada maka hankali […]
Amincin Allah ya tabbata a gare ka da sauran bayin Allah nagari da kuke tare.
Ranka ya dade na dade ban rubuto maka wasika ba, ba don na manta da kai ba ne sai don abubuwan da ke faruwa a Najeria sun wuce hankalin mai hankali. Ka yi hakuri, ban zo don in tada maka hankali ba sai dai na zo na sanar da kai irin tabargazar da ake yi a kasarmu.
Na san kana sane da lokacin da Allah Ya kaddara za ka bar mu, ana shirin wani taron kasa da shugaban wancan lokaci (Obasajo) ya shirya don biyan bukatar kansa. Na san ka fara shirya-shiryan yadda jama’armu za su je wurin taron da bukatun yankin namu. Kwatsam sai Allah Ya yi kiran ka. Allah Ya kara kyautata maka makwanci.
Wannan karon ma shugaban wannan lokacin ya zo da irin waccan bukatar ta neman ya kau da hankalin mutane daga tabargazar da ake yi zuwa shirin ya sake dare kujerar mulki da taimakon kannenka da abokanka da suka juya wa Arewa baya. An dai fara taro kuma jama’ar Arewa sun tafi taron ba a shirye ba kuma kadan ne daga cikinsu ke da sanin abin da ya kai su wajen taron.
Babban abin takaici shi ne wai yanzu an gane cewa Kiristocin Najeria sun fi Musulumin yawa, don Musulmi na da 183, Kiristoci na da sama da 300. Na san za ka iya kintato abin da muke fuskanta a halin yanzu. Ba ma wannan ne ya fi damuna ba sai kisan kare dangi da ake wa ’yan Arewacin. Ba a kisan mutum daya yanzu sai dari ko ma abin da ya wuce haka, a lokaci daya. Kwanan nan aka yi irin wannan a mahaifarka ta Katsina da Kebbi, ban da wanda ke faruwa a Jos, Bauchi, Maiduguri da Adamawa, Yobe. Tun da gwamnatin nan ta hau mulki jama’ar yankin ba su sami kwanciyar hankali ba. Mutanen Arewa suna ganin tashin hankali da kaskanci iri-iri!
Na san wannan zai bata maka rai kwarai ranka ya dade, sai dai ka yi hakuri. Mutanen Arewa sun yi wata irin lalacewa ta rashin kishin jama’armu da yankinmu, duk da wadannan abubuwan da ke nuna mana rashin kaunar da ake wa yankin da addininmu, wasunmu ko a jikinsu; don su suna samun abin sa wa a cikin miya. Ko ka san kanenka da ke Sakkwato kuma tsohon gwamna ya shiga rundunar durkake Arewacin Najeria tare da tsohon malamin makarantar nan da Buhari ya daga hannunsa Allah Ya aminta ya zama gwamnan Kano. Shi ma ya shiga cikin waccan kungiyar karya al’ummar Arewa. Bari na rage murna na gaya maka halin da Sunusi Lamido Sanusi ya shiga, da ya bayyana cewa wasu na kuruciyar bera da dukiyar ’yan Najeria, yana nan yana cikin wulakanci da tozartawa; duk da na ga Malam Nasir el-Rufai na taya shi jaje amma duk Arewa kowa ya kama bakinsa ya yi shiru kuma kowa ya san gaskiya. Ina ka taba jin barawo ya shiga gida amma aka kasa cewa ga barawo sai barawon ya nuna maigidan ya ce ai shi ma dan fashi ne, sai mai gida ya kuma cewa ga darawo? Kai, wannan rainin wayon ya yi yawa kwarai!
Ranka ya dade, ba ka da magaji yanzu a Arewa, duk tsofaffin nan sun zama ’yan kasuwar bukata, in dai za su samu shi ke nan kowa ma ya mutu. Wannan shi ne abin da muke ciki, ka san shugaban dan asalin yankin da ake samun man fetru ne, yana da kudin sayen mutanen namu.
In za ka iya tunawa, tun lokacin da Umaru Musa ’Yar’aduwa ya ware kudi don yashe Kogin Kwara da fadada shi amma Jonathan na hawa ya dakatar da aikin, ya ce zai mai da kudin zuwa yankinsa na Neja-Delta kuma hakan ta tabbata babu wanda ya ce komai.
Duk da wadannan alamu da ke nuna dan yatsa ga duk mutumin Arewa amma za ka yi mamaki yadda ’yan Arewa ke goyon bayan wannan dakilewar da ake mana, don su za su sami abin sa wa a aljihunsu. Yau Bafarawa, Tanko Yakasai, Buba Marwa da Shekarau duk suna jin dadin halin da Arewa ta wayi kanta a ciki. Babban abin takaici ma shi ne matsayin da matsanmu suka wayi kansu a ciki na rashin kishi, rashin sanin mutuncin kai, rashin ganin kimar al’ummar mu.
Ranka ya dade, a yau tsofaffin shugabannin kasa da tsofaffin gwamnoni da ministoci da sarakunan gargajiya ’yan Arewana, duk sun koma ’yan amshin Shata; babu mai cewa komai a kan wulakancin day a samu Arewa. Na san wannan ka sha fadar cewa mafiya yawansu karyar kishin Arewa suke yi.
Bari na dan tsegunta maka halin da Janar Buhari ke ciki yanzu. Ya aminta da wani kawance da Kudu-Maso-Yammacin kasar nan, don ganin ko Allah zai sa a dace wajen ceto al’ummarmu amma fa yana fama da munafukai daga cikin gida kuma ’yan uwansa ake amfani da su don gurgunta tafiyar. Kamar yadda na fada a sama, zan ba ka cikakken bayani a wasikata ta gaba in sha Allahu.
Zan dakata a nan sai na dawo na gaya maka yadda aka shirya tsaf, aka kai hari a kan ’yan makaranta a nan Arewa kuma jahar da ke kakkashin jami’an tsaro ba tare da an kama ko gano wadanda suka yi hakan ba.
Ranka ya dade, dole na shaida maka cewar akwai wasu kannenka da ke kokari gwargwadon hali, kamar Dokta Aliyu Aliyu U. Tilde, yana kokarin nusar da al’umma. Zan dawo nan gaba don karasa bayanan da nake son sanar da kai. Allah Ya kara kyautata makwancinka. Na bar ka lafiya.
Ghali mai lambar waya 08023702045