Tabarbarewar dabi’a: Duniya ina za ki da mu ne?

Bari ma in kara maimaita wannan tambaya ta sama, shin wai duniya ina za ki da mu ne? Na yi wannan tambayar ne a sakamakon wani tsokaci tare da labari mai tada hankali da na samu a wannan  makon. Malam Rabi’u Yusuf Yawale, Gama-Kano (08065273401) ne ya aiko mini da shi. Bayan na karanta shi, […]

Tabarbarewar dabi’a: Duniya ina za ki da mu ne?

Bari ma in kara maimaita wannan tambaya ta sama, shin wai duniya ina za ki da mu ne? Na yi wannan tambayar ne a sakamakon wani tsokaci tare da labari mai tada hankali da na samu a wannan  makon. Malam Rabi’u Yusuf Yawale, Gama-Kano (08065273401) ne ya aiko mini da shi. Bayan na karanta shi, sai na ga cewa ya kamata a yada shi saboda ya zama darasi ga al’ummarmu. Kafin in ci gaba da sharhina, bari in ba ku labarin, kamar yadda ya aiko mini shi; inda yake cewa:
“Malam Gizago, ko ka san cewa bakar dabi’ar nan ta kunno kai a kasar Hausa? Muguwar dabi’ar nan da ke wakana tsakanin mata ‘yan boko da kuma hamshakan mata har ma da ‘yan ku-ci-ku-ba-mu ‘yan matan da ke karatu a makarantun kwana da ma na je-ka- ka-dawo da kuma masu sana’ar karuwanci tamkar jirgin kasan da ya hararo tasharsa?
Ina magana ne kan dabi’ar neman mata a junansu da niyyar jima’i, wadda na yi magana a kan ta a wannan jarida a kwanakin baya; wadda a hausance ake kira madigo. Game da wannan dabi’ar, sai dai mu ce Innalillahi wa inna illaihi raji’un! Domin wallahi duk yadda muke zaton ta, to, ta wuce nan. Ta wuce inda ma ba a tsammanin za ta je a kasar Hausa a yau.
Na lura da kyau, mutanen da ya dace su fito su yi jan ido, kuma su yi nasiha ga masu aikata wannan mummunar dabi’ar, mai saukar da masifa a bayan kasa da rusa asasin tubalin tarbiya da tsarkin manyan gobe; duk sun noke, sun yi shiru saboda dalilan da ba su wuce nauyin laifin da fadarsa da kuma alkunya mara amfani ba. Ga shi kuma galibin wadanda ya kyautu su yi magana da jan hankali a kai, wannan bala’i ya ci gidajensu!
Shin yin shiru da kau da kai tare da barin ci gaba da ruruwar wannan fitina a tsakanin iyalai a makarantunmu da gidajenmu da ofisoshinmu da otal-otal dinmu da suke tsakiya da gefenmu, zai haifar mana da da mai ido kuwa? Ina hukumomi irin na shari’a a jihohinmu da kuma hukumomin gyara tarbiyya suka makale ne?
Gizago, ko ka san cewa kwanaki a wata makaranta ta ‘yan mata, wadda aka sanya wa sunan wata uwargidan tshohon shugaban kasar Najeriya, aka samu wata daliba, Bahaushiya, tana lalata ‘yan mata da wannan muguwar dabi’ar? Al’amarin ne dai ya kai ga sallamar ta daga makarantar. Da yake hukumomi a yau ba ruwansu da kula da zamantakewar al’ummar da amanarsu take hannunsu, musamman manyan gobe, kuma iyayen gobe, wanda amanar tarbiyar ‘ya’yanmu da jikokinmu za ta fada hannunsu a gobe, kuma makarantar farko da yaro ko yarinya take fara halarta a rayuwarta, wato uwa mace! Sai ga shi wannan fitinanniyar yarinya da aka kama tana lalata abokan karatunta ta hanyar madigo a makaranta kuma shugabannin makarantar suka kore ta, ta tsallaka wata unguwar da take kusa da wannan makaranta ta ba da abin duniya, aka dauke ta a wannan makaranta, wadda dukkannin makarantun na hukuma ne kuma na je-ki-ki-dawo gida ki taya inna aiki!
A wannan sabuwar makaranta da wannan daliba mai koyar da dalibai madigo ta koma, ta ki gyara kura-kuranta da suka kai ga tonuwar asirinta a makarantar baya, inda ta ci gaba da jan zarenta a wannan sabuwar makaranta cikin nutsuwa ba tare da ya tsinke ba, kuma ta samu daurin gindi a wajen wasu malaman makarantar, ba tare da sanin shugabannin makarantar ba!
Asirin wannan daliba ya sake tonuwa ne a wata rana da aka kama wani mai koyar da tarbiya a bandakin makaranta, yana cin amanar wata daliba da hukumomi suka damka a hannunsa. Lokacin da aka zo yi wa wannan daliba horo sai ta bude bakinta, ta bayyana wa iyayenta na makaranta cewar ita fa abin da take yi nafila ne a kan abin da wasu dalibai suke yi. A karshe sai allura ta tono garma, inda wannan daliba ta fasa wa ‘yan kungiyar madigo na wannan makaranta kwai a ka. kungiyar da waccan fitinanniyar daliba take jagoranta.
A karshe dai wannan daliba mai koyar da ‘yan mata kawayen karatunta madigo, ta sake samun kanta a matsayin korarriya a wannan sabuwar makaranta. Maimakon kaskanci ya samu wannan daliba, sai wasu manyan hamshakan mata, masu hannu dumu-dumu a wannan sana’a suka ji labarinta; inda suka kira ta suka yi mata irin fadansu na manya. A karshe dai saboda wannan fada na manya sai wannan budurwa ta hakura da karatun, kuma aka yi mata tukwici da mota mai dan karen tsada, wadda hatta ‘yan kasuwa, attajirai da kananan barayin lalitar hukuma na unguwarsu, babu wanda yake tunanin ya kai ga mallakar irin wannan mota, saboda tsadarta!
Cikin lokaci kankani wannan budurwa ta rushe gidan mahaifinta daga na gargajiya, ta maishe shi ko’ina tangaran, hade da saye gidajen makwabta domin fadada nasu. Kuma dattawan unguwa da gari, har da wadanda alhakin su sanar da rahamar Allah da dalilan saukar rahamar da kuma dalilan yankewar rahamar, suka zuba na mujiya, suna kallon wannan budurwa tana yi wa ‘ya’yansu da matansu dauki daidai, sabaoda tsoron tana da masu gidan rana. Idan ka yi mata maganar da ba ta gamsar da ita ba sai ta sa ka ja sarka, hade da daukar bokitin kashi a jarun!
Sannan wannan budurwa sai ya zamana ta zama mai sada mai nema da wadda ake nema, a ba ta ladarta. Kuma abin bakin cikin ma, yara ‘yan mata masu karatu a kananan makarantun sakandire da manya, a kullum kofar gidanta ban da manyan motoci masu duhun gilashi da lambar girma, ba ka ganin komai, musamman idan aka ce rana ta kai karshen yamma!
Su kuwa masu wanki da guga na unguwa da masu shagon kayan tireda da masu katin waya, ba irin girmamawar da ba su yi wa wannan tambadaddiya, ‘yar baya ga dangi, tamkar wata waliyya! Sunanta ma ba ya faduwa a bakunansu, sai Hajiya saboda kawai suna samun ribar kayan sana’arsu ta hanyarta. Sa’anin mahaifinta, saboda lalacewar al’umma, ta kai karshenta su ne masu durkusa mata, suna gaida ta saboda N500!
A gaskiya al’amarin nan na madigo, da na ajiye kunya a gefe nake maganarsa filla-filla; ban yi haka ba sai domin kazantar da ke cikinsa da kuma tasirin da yake kara yi a tsakanin matayenmu da kannenmu da ’ya’yanmu da ’yan uwanmu, wadanda su ne ke daukar amanar ’ya’yanmu a cikunansu, kuma su ne makarantar tarbiyyarsu ta farko; wanda idan suka rasa tarbiya, gobenmu ta baci! A saboda haka nake kara bincike mai zurfi a kan wannan masifa da ta kunno mana, wanda bayan asalinta da na yi bayani a rubutuna na baya.
A yau maganar ’yan boko ta kare, domin wadanda ba su bokon ma sun dauka, kuma ba kowa ya jawo mana wannan bala’i ba face mu da kanmu mazaje, wadanda a kodayaushe bukatar kanmu muke fifitawa a kan ta iyalanmu, amanar da Allah (SWT) Ya damka mana kuma Zai tambaye mu a kan ta; wadda za ta iya kai mu wuta kai tsaye (Allah Ya kiyaye)!
Ya zama wajibi kowane uba, kowane magidanci, ya koma cikin iyalansa, ya koma gidansa ya sake fasalin kulawa da kyautatawar da take tsakaninsa da iyalansa, musamman matayen aure da ‘ya’ya mata, wadanda muka riki al’adar watsi da tarbiyarsu da jawo su a jiki, muka mika wa iyaye mata, wadanda su kansu ba mu jawo su a jiki yadda ya kamata ba, bare mu san halin da suke ciki a zukatansu bare kuma mu san damuwar ‘ya’yanmu mata, wadanda suke da tulin tambayoyi a gare mu. Tambayoyin da ba wanda ya cancanci amsa musu su kamar iyayensu maza, amma sai muka dauki salon kyararsu da tsawatar musu a kan abin da ya dace mu saurare su da kunnuwan rahama!
Mata dai halitta ne tamkar mu, wadanda suke da sha’awa kamar mu, kuma sha’awarsu ta zarta tamu wajen kaiwa ga makura, kuma suke kaunar tsabta da kulawa ta hakika daga gare mu. Wanda rashin haka yake kai su ga damuwa mai tsanani a zukatansu, wanda bayyana hakan ga miyagun kawaye ke kai su ga fadawa ga halakar madigo! Ya Allah Ka tsare mu daga iface-ifacen shaidan!