Tabarbarewar tarbiyyar matasa abin damuwa ne – Farfesa Rabi Muhammad

Farfesa Rabi Muhammad ita ce Farfesa mace ta farko a fannin kimiyyar ilimi a Jihar Sakkwato ta da, wanda ta hada jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara. Ta shafe shekara 17 a matsayin shugabar makarantun mata a Jihar Sakkwato, Aminiya ta tattauna da ita kan sha’anin rayuwarta: Tarihina Sunana Rabi Muhammad an haife ni a […]

Tabarbarewar tarbiyyar matasa abin damuwa ne – Farfesa Rabi Muhammad

Farfesa Rabi Muhammad

Farfesa Rabi Muhammad ita ce Farfesa mace ta farko a fannin kimiyyar ilimi a Jihar Sakkwato ta da, wanda ta hada jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara. Ta shafe shekara 17 a matsayin shugabar makarantun mata a Jihar Sakkwato, Aminiya ta tattauna da ita kan sha’anin rayuwarta:

Tarihina

Sunana Rabi Muhammad an haife ni a garin Argungu a Jihar Kebbi ranar 12 ga Yunin 1962. Na yi karatun firamare a makatantar Shehu Kangiwa bayan na gama na tafi Sakandaren ’Yan Mata ta Illela wadda na gama 1981. Daga nan kai-tsaye na shiga Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari na samu Takardar Shaidar Malanta ta NCE a fannin Geography da Biology.

Ina cikin karatu na yi aure bayan na gama NCE na tafi yi wa kasa hidima a lokacin ana hidimar kasa da NCE, na yi a Kwallejin Sarkin Musulmi Abubakar bayan na gama sai suka rike ni, na ci gaba da karantarwa a wannan makaranta. Ina wurin mai gidana ya tafi karatu sai aka yi min canjin wajen aiki zuwa Sakandaren ’Yan Mata ta Sakkwato (GGC), na yi shekara daya na sake komawa can, ina makarantar ce aka kirkiro Jihar Kebbi sai aka samu guraben ayyuka, domin mafi yawan shugabannin makarantun ’yan asalin Jihar Kebbi ne hakan ya sa na zama shugabar makaranta a lokacin ina da digiri na farko a fannin Biology.

Makarantar da na fara shugabanta ita ce makaratar mata a Karamar Hukumar Tambuwal daga nan sai Illela daga nan na koma Bodinga a cikin haka ne na koma na yi digirina na biyu a fannin kimiyya, ban tsaya ba na ci gaba da karatun digiri na uku ina cikin karatun ne aka mayar da ni Makarantar Mata ta Hafsatu Ahmadu Bello, ina can ne na gama karatun digirin-digirgir (PhD).

Shekara 17 ina shugabar makarantar  bayan samun canjin gwamnati sai aka mayar da ni Kwalejin Ilimi (COE) a matsayin malamar makaranta na yi shekara daya a can na sai nemi aiki a Jami’ar Usman Dan Fodiyo na samu yau shekara 10 ina aiki da su. A lokacin da suka dauke ni sun ba ni matsayin Babbar Malama a haka likafa ta ci gaba har ga shi yanzu na zama Farfesa.

Kalubalen

Babban kalubalen da na samu a rayuwa shi ne lokacin da maigidana ya kuna. Abin da ya faru kuwa shi ne, ya same ni ina girki a saman murhu a waje, domin sa’ar da na shiga kicin don in yi aiki a ciki sai na fahimci tukunyar iskar gas na yoyo sai na kulle kicin din. Da ya zo sai ya bude kicin yana tambayar dalilin fitowata waje kafin in gaya masa wutar da ke waje ta kama shi yana cikin kicin din.

Daga nan ne makwabta suka taimaka aka tafi da shi asibiti, likitan da ya fara duba shi ya ce in ya wuce makon da muka kawo shi to zai iya tashi, amma damar tashin nasa ba ta da yawa. A gaskiya na shiga damuwa da jin cewa da wuya ya rayu, hankalina ya tashi sosai. Allah Ya kaddari yana da kwana gaba sai ko ya rayu aka yi ta jinya har aka cimma karshen jinya.

Burina a kuruciya

Gaskiya burina na kuruciya ya cika domin ina son karantarwa kuma ga shi ina cikinta, kuma ina son zama Farfesa, ga shi na gode Allah na samu biyan bukata na rayuwa. Amma zan ci gaba da karatu domin buri bai karewa sai mutum ya mutu.

Darasin da na koya a rayuwa

Na koyi darasi na rayuwa da yawa na yi shugabar makaranta da mu’amala da mutane da yawa maza da mata yara da manya na fahimci dabi’ar mutane daban-daban. Na koyi yin hankuri, domin lokaci yana warke kowace irin cuta, in ba ka iya mu’amala da mutane ba za ka shiga cikin damuwa koyaushe in ka iya ba ka kwana da bakin cikin kowa.

Abin da nake son a tuna ni da shi

A matsayina na malamar makaranta ina son a tuna ni kan na yaye dalibai da suka kai matsayina na Farfesa, ina son a tuna da yawan farfesoshin da na yaye ina son a tuna da alherin da na yi. Domin idan ka yaye dalibai ka gina al’umma ne.

Tarbiyyar mata matasa

Gaskiya a halin yanzu  abin na da ban tsoro domin ba su da kunya kuma wannan shi ne babban aibin da ke kawo rashin tarbiyya, domin duk wanda ba ya da tarbiya za ka samu bai da tsoro duk abin da zai yi ba shakku don yana ganin ya fi iyayensa wayo.

’Yan kadan ne cikinsu ba su sa yaudara a lamuransu, akwai ban tsoro yadda zuciyar matasa ba ta da tausayi da tsoro, musamman mata in ba su da tarbiyya wadanne irin yara za su haifa tunda ba ka bada abin da ba  ka da shi, Allah Ya kare mu.

Kasancewata Farfesa mace  a fannin kimiyyar ilimi (Science Education) a tsohuwar Jihar Sakkwato

Wannan babu abin da zan ce sai godiya ga Allah, baiwa ce daga Ubangiji na gode maSa sosai

Iyali

Ina da ’ya’ya biyar, mata uku maza biyu. Maza biyu da mace daya sun yi karatun digiri na biyu. Dayar kuma tana hidimar kasa, dayar kuwa za ta kammala sakandare a yanzu. Haka kuma ina da jikoki biyar.

Shawara ga mata

Su ji tsoron Allah su nemi ilimi, duk rayuwar da ke da jahilci cikinta babbar illa ce.  Marar ilimi ba ya mu’amala mai kyau, ina kira ga mata su nemi ilimi. Maza kuma su ji tsaron Allah su bari matansu su nemi ilimi domin duk yadda mace ke son ilimi in mahaifinta ko mijinta bai sanya ta ba, ba yadda za ta yi.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara