Tabarbarewar tsaro a yankin Arewacin kasar nan

A lokacin da aka dage zaben ranar 14 ga watan Fabrairun bana zuwa makonni shida, an ba da uzurin kawo karshen kungiyar Boko Haram ne, wadda ta kashe fiye da mutum dubu 15 tun shekarar 2009. Kuma ta raba  fiye da miliyan  daya da muhallinsu. Jama’ar kasar nan sun kwana da sannin cewa an sayo […]

Tabarbarewar tsaro a yankin Arewacin kasar nan
Tabarbarewar tsaro a yankin Arewacin kasar nan

A lokacin da aka dage zaben ranar 14 ga watan Fabrairun bana zuwa makonni shida, an ba da uzurin kawo karshen kungiyar Boko Haram ne, wadda ta kashe fiye da mutum dubu 15 tun shekarar 2009. Kuma ta raba  fiye da miliyan  daya da muhallinsu. Jama’ar kasar nan sun kwana da sannin cewa an sayo sabbin kayan aiki kuma an sake dabarun yakin da ake da kungiyar. Amma kuma kasar ta tsinci kanta cikin wani mawuyacin hali.
An ’yanto garuruwa kamar Chibok. Wasu mutane da suka samu kubuta suna bayyana yadda ’yan Boko Haram suka gallaza musu ukuba. Wasu suna ganin nasarar da aka samu wajen ’yanto garuruwan an same su ne domin tallafin da aka samu daga dakarun kasashe makwabta. Ko ma me ne ne, a zahiri yake cewa nasarar da aka samu abin a yaba ne. Kuma ya dace a tabbatar da dorewarta. Yankunan da ke karkashin ikon ’yan Boko Haram ya kai girman wasu daga cikin kasashen Turai. Kodayake, wancan farmakin ya sa sun ja baya daga wuraren da suke da iko da su. A lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kama aiki ya ba da umarnin cewa cibiyar da ke jagorantar yaki da kungiyar ta koma da hedkwatarta birnin Maiduguri, wato kusa da fagen daga. Wannan abu da ake ganin zai taimaka a yakin, sai dai akasin hakan ake samu musamman ganin yadda ake ci gaba da samun karuwar hare-haren Boko Haram. Zubar da jinin ya karu matuka musamman cikin watan azumin Ramadan. daruruwan mutane sun rasu a cikin makonnin fara kai hare-hare. Kamar yadda ya zama dabi’arsu, sun fi kai hari ne a masallatai da majami’u  da wuraren cin abinci da kuma sauran wuraren taruwar jama’a. Kodayake, babu wanda ya dauki alhakin kai harin amma sun fi kama da irin wadanda kungiyar Boko Haram take kaiwa a wadannan yankunan.
Harin da aka kai masallacin ’Yantaya ya faru ne lokacin da Malam Sani Yahaya na kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a, wanda ya saba yin wa’azi kan muhimmancin zaman lafiya da kaucewa tada fitina, yake Tafsirin Al-kur’ani Mai Girma. A Sabon Garin Zariya, akalla mutum 25 ne suka rasu, galibinsu mata ma’aikatan gwamnati. Har ila yau, harin ya fi rutsa da su ma’aikatan jinya da kuma na kananan hukumomi da suke halartar shirin tantance su. Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i ya soke shirin tantancewar kuma ya shawarci jama’a da su kauracewa wararen taruwar jama’a. Akwai wadanda suka yi amannar cewa karuwar hare-haren Boko Haram yana faruwa ne saboda cire shingayen bincike sojoji da aka yi, kwanakin baya a yankunan da harin ya shafa. Har ila yau, ra’ayi ya bambanta, inda wasu gwamnoni suke kira da a dawo da su, yayin da wasu kuma suke ci gaba da goyon bayan cire su. Wadanda suke goyon bayan cirewar suna cewa ba a taba kama wani dan ta’adda ba a irin wadannan shingayen. Kuma sun kasance wasu wurare da ke haifar da jidali da kuma kasancewarsa wurin karbar cin hanci da kuma kashe-kashe.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ike Ekweremadu ya ce hare-haren Boko Haram ya karu ne daga lokacin da Shugaba Buhari ya kama mulki a karshen watan Mayu. A martanin da jam’iyya mai mulki wato APC ta mayar, ta ce “aski ne ya zo gaban goshi, inda a baya ake samun jerin hare-hare yanzu kuma dai-daiku ne.” Kakakin jam’iyyar Alhaji Lai Mohammed ya ce an dauki matakan da suka kamata a ciki da wajen kasar don ganin bayan kungiyar. Ko haka batun yake, ko kuma akasin hakan, wannan ya nuni da cewa yakamata a kara azama wajen yakin da ake da Boko Haram. Ya dace mahukunta su lalubo dalilin da ya sa sojoji suka dakatar da aikinsu. Da kuma yadda ’yan gwagwarmayar, wadanda suke tserewa, amma a yanzu suke kaddamar da hare-hare.

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna