Tabbas, a kowane fim sai na sha mari – Inji Nura MC
Fitaccen jarumi a harkar fina-finan Hausa mai suna Nuraddin Muhammad Usman wanda aka fi sani da MC Khan ya ba da haske dangane da dalilan da suka sa ya shiga harkar fim da kalubalen da ya fuskanta da kuma gaskiyar batun nan da jama’a ke yi cewa duk fim din da ya fito sai ya […]

Fitaccen jarumi a harkar fina-finan Hausa mai suna Nuraddin Muhammad Usman wanda aka fi sani da MC Khan ya ba da haske dangane da dalilan da suka sa ya shiga harkar fim da kalubalen da ya fuskanta da kuma gaskiyar batun nan da jama’a ke yi cewa duk fim din da ya fito sai ya sha mari.
Tarihina a takaice
Assalamu alaikuma, suna na Nuraddin Muhammad Usman wanda aka fi sani da Nura MC Khan, an haife ni a Tudun Wada, Kaduna. Na yi makarantar firamare da sakandare, bayan na kammala ne sai na koyi sana’ar gyaran mota, daga bata na bar aiki, inda na koma makaranta har na yi difloma a shekarar 2010 a bangaren lissafin shiga da fitar kudi (Accounting) a Makarantar Horar da Ma’aikata da ke Makera. Daga nan ne sai na fara harkar fina-finan Hausa.
Dalilin da ya sa na shiga harkar fim
Ra’ayi da sha’awa ne suka ja ni zuwa sana’ar fim. Hakan kuwa ya samo asali ne, kasancewar tun ina yaro ina kallon fina-finan Indiya. Dalilin da ya sa mutanen unguwarmu suka fara kirana da sunan ‘Nura Boss’. Sun sanya mun wannan inkiyar ce saboda da zarar mun kammala kallon fim din Indiya, abu na gaba shi ne kwaikwayon duk wani abu da ya shafi tsalle-tsalle da guje-guje da muka ga an yi a fim din.
kalubale
kalubalen da na fuskanta na farko shi ne hassada daga wasu daga cikin abokan sana’ar a lokacin da suka fahimci tauraruwata ta fara haskakawa, sai kuma irin rade-radin da abokaina suka yi ta yayatawa a watannina na farkon a harkar. Inda suke ta suka da kananan maganganun wai ina wahalar banza, kuma a ganin su abincina ba ya harkar. Gwiwowina ba su yi sanyi ba ko kadan, na ci gaba da abun da na sa a gaba, ganina ya yi musu wuya matuka. Amma fa ba su fasa surutai ba har sai da ya zama cewa hanyar da za su iya ganina cikin sauki shi ne ta kallon fina-finai Hausa. A cikin wannan yanayi mutum daya ne ba zan manta da shi ba wato Abubakar Yaros Khan saboda ya kasance wani mai karfafa mini gwiwa a kodayaushe.
Fina-finaina
Na fito a fina-finai kamar su: ‘Sai Wata Rana’ da ‘Kudi A Duhu’ da ’Bissalam’ da ‘Kaicona’ da ‘Hasken Zuci’ da ‘Alkawari’ da ‘Adamsy’ da kuma ‘Barti Ko Marti’
A kowane fim na fito sai na sha mari
Wannan daga darakta ne, saboda duk rol din da ya ba ka shi ne yake ganin ya dace da kai. Hakan ya sa yawancin daraktoci sun fi ba ni rol din bijirarre, ka ga ba ka raba wannan rol din da shan mari.
Burina
Na kara samun daukaka a harkar fim ta inda ni ma zan taimaki sababbin jini da sauran jama’a.
Iyali
Mahaifina dai ya rasu amma mahaifiyata tana raye. Aure kuma na dauki harami.