Tabbas akwai yunwa a Najeriya amma sauƙi na tafe — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya magantu kan halin ƙuncin rayuwa da ya addabi al’ummar Najeriya yana mai tabbatar da cewa lallai ana fama da yunwa a ƙasar. Sai dai shugaban ya ba da tabbacin cewa sauƙi na tafe nan gaba kaɗan saboda wasu tsare-tsare da yake ɗauka domin kawo ƙarshen matsalolin. Kashi 63 na ’yan Najeriya […]

Tabbas akwai yunwa a Najeriya amma sauƙi na tafe — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya magantu kan halin ƙuncin rayuwa da ya addabi al’ummar Najeriya yana mai tabbatar da cewa lallai ana fama da yunwa a ƙasar.

Sai dai shugaban ya ba da tabbacin cewa sauƙi na tafe nan gaba kaɗan saboda wasu tsare-tsare da yake ɗauka domin kawo ƙarshen matsalolin.

Wata sanarwa da hadiminsa a ɓangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ya ce Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ƙulla yarjejeniyar inganta harkokin sarrafa naman dabbobi da wani kamfani a birnin Rio de Janeiro na ƙasar Brazil.

Tinubu ya ce akwai wasu muhimman tsare-tsare da gwamnatinsa ta shimfiɗa domin kawo bunƙasa harkokin noma da kiwo.

Shugaban ya kuma faɗi yadda yake ƙoƙarin shawo kan matsalolin ƙarancin abinci da kuma rigimar manoma da makiyaya. Tinubu ya tabbatar akwai yunwa a Najeriya

“Muna ƙoƙarin magance ƙuncin rayuwa da ake fama da rashin tabbas ta hanyar inganta tattalin arziki.

“Za mu yi duba zuwa matsalolin da muke da su a ƙasar domin kawo damarmaki da ke ciki.

“Samar da abinci yana da matuƙar muhimmanci, amma a yanzu da muke magana akwai yunwa sai dai akwai haske a gaba wanda kowa zai shaida hakan.”

 

An kashe manoma 7, an ƙone buhun masara 50 a Neja

DSS ta kama jami’in hukumar agaji na bogi

Na yi wa mahaifina alƙawarin ba zan taɓa aikata masha’a ba — Murja

Jerin ƙasashe 24 da suka yanki tikitin Gasar AFCON 2025