Tabbas kam soyayya karya ce!

Masu iya magana sun ce fahimta fuska ce. A yayin da wasu suka hakikance cewa akwai soyayya kuma soyayya gaskiya ce. Wasu kuwa sun yi watsi da batun na soyayya, sun yanke hukuncin cewa lallai soyayya karya ce. Wannan matsayar ce ma Naseer Mustapha Kano ya dauka, inda har ma ya yi bayanin dalilin da […]

Tabbas kam soyayya karya ce!
Tabbas kam soyayya karya ce!

Masu iya magana sun ce fahimta fuska ce. A yayin da wasu suka hakikance cewa akwai soyayya kuma soyayya gaskiya ce. Wasu kuwa sun yi watsi da batun na soyayya, sun yanke hukuncin cewa lallai soyayya karya ce. Wannan matsayar ce ma Naseer Mustapha Kano ya dauka, inda har ma ya yi bayanin dalilin da ya sanya shi bayyana haka. Ga abin da yake fada da kansa:

Naseer Mustapha Kano, 08034746514:
Gaisuwa da fatan alheri ga dukkan ma’abota wannan shafi na Dausayin kauna. FDk, ashe da ma soyayya ba gaskiya ba ce? Ashe dama ba komai a cikin soyayya sai bakin ciki da takaici da bata lokaci? Wadda nake so ta yaudare ni, ta ha’ince ni. Shekararmu biyu muna soyayya ni da ita, bayan wata daya da tashinsu daga unguwarmu, suka koma Fagge. Na je gidansu amma ta kalli idanuwa ta ce mini: “Ban gane ka ba, na manta waye kai; sai ka yi bayani.”
Lallai Fagge ta amsa kirarinta: ‘Faggen wuta, Faggen Lamarudu! Garin da babu dan halak sai shege! In ka ga dan halak bako ne, kafin a kwan biyu ya zama shege!’
***
Ni kuwa na ce, don dan wannan abin ya faru sai ka ce soyayya karya ce? Wannan abin da ya faru bai isa ya karyata cewa akwai so ba, watakila ma tun farko babu soyayya a tsakaninku, kai ne dai ka dauka ko akwai, lokacin da gaskiya ta bayyana, sai ka yi kudin goro, ka ce babu soyayya. Daure ka kara bincikawa, za ka gamu da soyayya, Malam Naseer! – FDk.
***
Sadiya Mesona, Kano:
FDk, yaudara ba ta yi ba, mayaaudara ba su yi ba. Ita fa soyayya daya ce ko e, ko a’a amma ban ga dalilin da ka san ba aure ne a gabanka ba, za ka je ka sanya wa mace soyayyarka. Ina magana ne a kan wasu maza mayaudara. A gaskiya a yanzu maza sun fi mata yaudara, domin suna sanya wa mace soyayyarsu, su shaku sosai har ta makance, don so in ya yi so, mace ba ta ganin gabanta, makancewa take yi; ya zamanto ba ta ganin komai a gabanta sai masoyinta. Wani lokaci koda saurayin gaskiya ne ya zo, wanda yake son ya aure ta, ba za ta saurare shi ba. Don haka mayaudara ku sanya tsoron Allah a ranku. Kodayake wani lokaci matan ma sai a hankali. Don haka mata ku bi a hankali, don ban ga dalilin zafafa soyayya ba.
***
S.A.D, 08126383223:
Assalamu alaikum jagoran masoya FDk, ina miko gaisuwata ga duk ma’abuta wannan fili na Dausayin kauna. Hmm, a gaskiya Sha’awa ba ki yi mana adalci ba, kodayake an ce laifi tudu ne, take naka ka hango na wani.
***
Maryam Zubairu Garabasa, Kazaure:
FDk, bayanin da Sunusi Musa Ciyaman ya yi a makon jiya, ya sanya a karon farko zan tofa albarkacin bakina a wannan fili mai matukar amfani. Da fatan mata za su dauki darasi daga bayanansa.
***
Shamsu Gezawa Kano, 07066796978:
Sardaunna masoya, ya aiki, ya hakuri da matan zamani? Shawara nake so ka ba ni, ina da budurwa, tana nuna mini tana so ne a gabana amma kuma wani in ya zo wurinta, shi ma sai ta ce shi take so. Na rasa yaya zan yi mata.
***
Malam Shamsu, ka ce ka hadu da tasi, wacce ba ta da gareji daya. Ka yi kokari ka nuna mata cewa ka fi sauran samarin kaunarta. Idan ta samu tabbacin cewa kai kwakkwara ne, kila ka rinjayi sauran, ta tsaya maka. Idan ba haka ba kuma sai dai ka canja wata daban, wacce za ta tsaya kanka kadai. – FDk.
***
Isyaku Muhammad Kiyawa, 07060496094:
Gaisuwa ga shugaban masoya, FDk. Ina so a mika gaisuwata ga a bar kaunata Ummi Musa Kiyawa. Ina sonta matuka.
***
Uhhm, haka dai Malam Isyaku, Allah Ya sa ita ma tana sonka, domin kuwa an ce son maso wani koshin wahala. – FDk.
***
Abdullahi Adamu Sakkwato, 08148583780:
FDk, gaisuwa mai yawa da fatan alheri a gare ka da sauran ’yan uwa baki daya, amin. Wanna ne karo na farko da na turo da sako. Gaskiya amsar da ka ba Yusuf Minna da Barira Sakkwato ta yi daidai. Allah Ya kara ilimi, amin.
***
Isma’il Ibrahim, 08033603963:
FDk, ina gaisuwa sannan ina so a gaishe mini da falleliya, zinariya, sarauniyar da ke mulki a cikin zuciyata, Amina Meenal. Ga shi a kullum ina so na kasance a tare da ita amma ba dama, kodayake na san wata rana za mu yi rayuwa tare amma wace rana ce? Ban sani ba.
***
Muhammad Sani Ciroma Tudun Murtala, 07069596572:
FDk, kuri’ata ta talaka ce. Dalilina shi ne: 1-Ya fi kaunarta da gaskiya, domin ya taimake ta lokacin da take neman taimako. 2-Ku sani fa, duk gidan da aka ce ruwan sama ya cika shi, ana iya asarar rai domin zai iya fadawa kan mutum. 3-Talaka ya sadaukar da rayuwarsa ba tare da tunanin abin zai same shi ba. Amma abin da attajiri ya yi: 1-Ya wulakanta ta saboda lokacin da ta sanar da shi, tsaki ya yi mata, ya koma barci; duk abin da zai faru sai da safe. Idan da ya zo ya samu ana jana’izar wani daga cikin gidan, ina ranar kudin? 2-Koda ta aure shi, ta sani fa ba za ta sami taimako ba, in dai yana barci ko kuma dare.
***
Yusuf Dabai K-Boy Bawasa, 09038386296:
Ina roko ga Dausayin kauna, a rika kyautata rayuwar masoya, kamar idan wani suka bata da budurwarsa; sai a ba su shawara su san yadda za su sasanta kansu. Mace, mai sa wa kato hawan jini!
***
Muhammad Sani Kaduna, 08065302177:
“FDk, yaya hakuri da jama’a? ina fatan kana lafiya. Allah kara girma da basira, amin. Na kasance ma’abucin karanta wannan shafi na Dausayin kauna amma ban taba aiko da sako ba sai wannan karon. Wallahi na sha wahala a soyayya, har na yanke hukuncin barinta. Kwastam, sai wani abokina ya zo mini da maganar wata bazawara, sakin wawa (daukar mai hankali). Ya yaba da kyan halinta, ga hankali da kyau da son addini kuma mahaifinta mai kudi ne. amma abin da ya ja hankali gare ta shi ne ibada amma ba mu taba ganin juna ba sai dai muna gaisawa ta wayar abokin nawa, don gudun saba wa shari’a. Domin ba ta kamata a ce na hakura da yarinyar, amma sai ya ce sam haka ba zai yiwu ba. ’Yan uwa, wace shawara za ku ba ni?