Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu

Sanatan ya ce akwai buƙatar shugaba Tinubu ya zauna da masu ba shi shawara domin ɗaukar matakan rage wahalhalu.

Tabbas ’yan Najeriya na cikin matsin rayuwa — Kalu

Sanata mai wakiltar Abiya ta Arewa, Uzor Orji Kalu, ya bayyana cewar tabarbarewar tattalin arziƙin ya jefa al’ummar Najeriya cikin ƙunci.

Yayin da yake zantawa da manema labarai a Majalisar Dokokin Ƙasa da ke Abuja ranar Talata, Kalu ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ɗauki mataki da gaggawa don rage wahalar da mutane ke ciki.

Tsohon gwamnan na Abiya, ya bayyana cewa babu wani shugaban ƙasa da zai so ganin al’ummarsa cikin wahala.

Ya ce, “Ko a ƙauyena, duk inda na je—kamfanoni da mutane—kowa na cikin tsaka mai wuya. Ina roƙon gwamnatin tarayya da shugaban ƙasa da ya kawo sauƙi ga ‘yan Najeriya cikin gaggawa.”

Kalu, ya jaddada cewa lamarin yana da matuƙar muhimmanci, “Shugaban ƙasa ya kamata ya ɗauki mataki, ba gobe ba, yanzu-yanzu.

“Ya kamata ya yi abin da ya dace saboda halin da ake ciki ba mai kyau ba ne. Ina ganin babu wani shugaban ƙasa da aka zaɓa da zai so ‘yan ƙasarsa su sha wahala.”

Ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu saboda ɗaukar matakan gyaran tattalin arziƙi, amma ya ce akwai buƙatar ɗaukar manufofin rage wahalhalu.

“Muna ganin gyaran da ake yi a yanzu bai taɓa faruwa ba cikin shekaru 60 da suka gabata. Babu wani shugaban ƙasa da ya samu ƙarfin gwiwar yin abin da Shugaba Tinubu yake yi a yanzu,” in ji Kalu.

Ya amince cewa gyare-gyaren shugaban ƙasa na buƙatar juriya da jarumta.

“Mutumin yana da jarumta sosai. Da ni ne shugaban ƙasa, watakila na ɗauki waɗannan matakan a hankali.”

Game da yiwuwar dawowa da tallafin man fetur, Kalu ya ce ba ya cikin tawagar kwamitin inganta tattalin arziƙi, amma yana ganin wannan batu ne da shugaban ƙasa ya kamata ya tattauna da masu ba shi shawara.

Ya kuma gode wa shugabannin jam’iyyar APC saboda ƙoƙarinsu wajen lashe zaɓen Gwamnan Jihar Edo.

Sojin sama sun yi kuskuren kashe mutum 16 a Zamfara

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7