‘Tabbatar da canji hakki ne a kan kowane dan Najeriya’

Sakataren karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano, Alhaji Sabo Iliyasu Saye ya bayyana cewa kowane dan Najeriya yana da hakki wajen tabbatar da ganin an aiwatar da canjin da aka samu a kasar nan, ta hanyar taimaka wa shugabanni su cimma manufofinsu na gudanar da gwamnati.Alhaji Sabo Iliyasu Saye ya yi wannan tsokaci ne lokacin […]

‘Tabbatar da canji hakki ne a kan kowane dan Najeriya’
‘Tabbatar da canji hakki ne a kan kowane dan Najeriya’

Sakataren karamar Hukumar Bichi a Jihar Kano, Alhaji Sabo Iliyasu Saye ya bayyana cewa kowane dan Najeriya yana da hakki wajen tabbatar da ganin an aiwatar da canjin da aka samu a kasar nan, ta hanyar taimaka wa shugabanni su cimma manufofinsu na gudanar da gwamnati.
Alhaji Sabo Iliyasu Saye ya yi wannan tsokaci ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce kowane dan kasa nagari yana da gudummawar da zai bayar wajen ganin  an amfani canjin da kasar nan ta samu ta yadda kowa zai samu rayuwa mai kyau.
Ya yi nuni da cewa yana da kyau ’yan Najeriya su san cewa an dade ana yi wa kasar nan mulki marar alkibla, don haka dole ne sai gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauki sahihan matakai na dora kasar nan a kan tubali mai inganci kafin a gyara barnar da ak yi a baya.
Alhaji Sabo Saye ya bukaci al’ummar kasar nan su fahimci cewa nan gaba abubuwa za su inganta saboda manufofin gwamnatin Buhari suna da kyau wajen kyautata ta fannin zamantakewa da tattalin arziki, inda ya yi fatan za a ci gaba da yi wa shugabanni addu’o’i na fatan alheri.
Sakataren ya bayyana cewa idan aka samu canjin gwamnati daga wata jam’iyya zuwa wata sai an yi tsare-tsare na tafiyar da gwamnati bisa  la’akari da manufar kowace jam’iyya, don haka wajibi ne a kara hakuri lokaci zai zo da jama’a za su yi murna kamar yadda suka jajirce wajen tabbatar da canjin da aka dade ana nema.
Alhaji Sabo Iliyasu ya ce kowa ya yarda cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da kishin ganin Najeriya ta kara bunkasa ta kowane fanni, don haka kowa ya tsaya wajen yin aiki da gaskiya da rikon amana ta yadda kasar nan za ta zamo abar  misali a tsakanin sauran kasashen duniya.