Tafiya a saman tirela: Ganganci ko neman sauki?

Sau da yawa, motocin kan jefar da mutanen a lokacin da suke gudu, ko kuma rassan bishiyoyi da wayoyin lantarki su buge su su fado kasa

Tafiya a saman tirela: Ganganci ko neman sauki?

Dabi’ar yin doguwar tafiya a saman manyan motocin dakon kaya daga Arewa zuwa Kudancin Nijeriya ko kuma daga Kudu zuwa Arewa ko a cikin yanki guda, takan kai ga an loda motane a saman motocin da suke dauke da lodin dabbobi ko hatsi ko kayan gwari ko karafa da sauran kayayyaki.

Lodin ba shi da wata ka’ida. Hasali ma, a wasu lokuta sai bayan motocin sun fara tafiya direbobi ke tsayawa a hanya domin daukar karin fasinjoji, baya ga wadanda suka dauka tun daga farko.

Sau da yawa, motocin kan jefar da mutanen a lokacin da suke gudu, ko kuma rassan bishiyoyi da wayoyin lantarki su buge su. Wani lokaci kuma, idan motocin suka yi hatsari, kayan da suke dauke da su ne kan danne mutanen har su rasa rayukansu.

Yawanci, an fi danganta ’yan ci-rani masu tafiya neman kudi a Kudancin kasar da hawa irin wadannan motoci, watakila saboda karancin kudin mota a hannunsu lokacin da za su tafi.

Amma me ke sa su ci gaba da hawa irin wadannan motoci a hanyarsu ta dawowa Arewa ko komawa gida bayan sun samo kudin da suka fita nema? A wasu lokuta ma, har sukan shafe kwanaki a hanya idan aka yi rashin sa’a mota ta lalace, suna jiran a gyara ta.

Wannan dabi’a an dade ana yin ta, tun kafin tsadar rayuwa da hauhawar farashin man fetur su janyo tashin kudin sufuri da suka tilasta wa mutane da dama neman wasu hanyoyi domin samun saukin kashe kudin sufuri da sauran bukatun yau da kullum

‘Neman sauki ke sa mu hawan gwangwaro’

Wakilin Aminiya ya ziyarci daya daga cikin tashoshin da ake loda matafiya a saman manyan motocin dakon kaya tare da dabbobi da sauran kayayyaki a yankin Isheri Kara, da ke kan iyakar Jihar Legas da Ogun.

A wurin, ya shaida yadda ake daukar tarin fasinjoji a saman kaya bayan manyan motocin sun gama lodin kayansu a cikin Legas. Daga nan ne direbobin kan yada zango a Isheri Kara domin neman karin kaya tare da daukar matafiya a saman motocin.

Ibrahim Muhammed, wani matashi da ke hawa manyan motocin dakon kaya idan zai koma gida a Arewa, ya shaida wa Aminiya haka a lokacin da yake kokarin hawa daya daga cikin motocin, cewa, halin matsin rayuwa ne ya sa suke amfani da irin wadannan motocin bayan sun gama neman kudi a Legas.

“Ka ga tsadar mai ta sa kudin mota ya yi tsada. Yawanci ba mu iya biyan kudin karamar mota, domin muna tafiya gida ne da ’yan kayan da muke saya mu tara a hankali domin guzuri. Za a caje mu kudin mota Naira dubu 40, banda kudin kayan da za mu dauka. A gida kuma muna da hidimomi da nauyin iyali a kanmu. Wannan ne ya sa dole muke hawa gwangwaro domin neman sauki.”

Ya ci gaba da cewa “Duk da cewa akwai hadurran da ke tattare da hakan saboda rashin kyawun hanya da sauran matsaloli, haka muke yin tafiyar saboda matsin rayuwa. Sai dai Allah Ne Mai karewa,” in ji shi.

Shi ma Muhammadu Nasir, wani matashi dan asalin Jihar Sakkwato mai sana’ar sayar da karas a Legas, ya shaida wa Aminiya cewa ya shafe watanni shida a Legas yana gudanar da sana’arsa, amma kudin da ya tara ba su da yawa sakamakon tsadar rayuwa.

“A cikin sana’ar nake ci, nake sha, nake biyan sauran bukatuna, sannan ina taimaka wa dangi da abokan arziki. dan abin da ya rage ne zan yi amfani da shi idan na koma gida domin yin noma.

“To, idan ka biya kudin karamar mota, za ka ga abin da ke hannunka ba zai ishe ka komai ba. Wannan ne ya sa muka fi son hawa babbar mota, inda ba za ka biya fiye da Naira dubu 10 ba, maimakon Naira dubu 30 zuwa 40 da za ka biya a karamar mota. Sai dai a babbar motar babu sauri, ana iya yin kwana uku ba a isa gida ba,” in ji shi.

Aminiya ta tattauna da wasu ’yan Arewa da ke hawa manyan motocin dakon kaya daga Kalaba zuwa Arewa domin jin dalilan da ke sa su fifita wannan hanya duk da hadurran da ke tattare da ita.

Jalabibi Abdurahman, wani dan asalin Jihar Sakkwato da ke zaune a Fatakwal, ya shaida wa Aminiya cewa tsadar kudin mota ce ta sa shi neman sauki ta hanyar hawa babbar mota.

“Ni dai tsadar kudin mota ce ta sanya ni neman sauki ta hanyar hawa babbar mota. Ka ga daga Fatakwal zuwa Sakkwato akwai nisa, kuma idan karamar mota zan bi, sai na kashe sama da Naira dubu 40. Bayan na isa Sakkwato ma sai na sake hawa wata mota zuwa Gwadabawa, sannan daga can in nemi wata motar da za ta kai ni kauyenmu.

“To, idan aka hada da kudin da zan rika kashewa wajen cin abinci a hanya, sai na kashe kusan Naira dubu 60. Amma idan na hau babbar mota, zan iya isa kauyenmu da kudin da bai wuce Naira dubu 15 ba. Sauran kudin kuma sai a yi hidimar gida da su,” in ji shi.

Shi ma dan Bala Shafi’u, wani matashi dan asalin Jihar Kano da ya je Kalaba ci-rani, ya bayyana cewa idan zai koma gida, yakan jira ne har sai ya samu babbar motar dakon kaya da zai bi zuwa Kano.

“Idan zan koma gida, nakan tsaya ne in samu babbar mota, ita nake hawa zuwa Kano, domin a gaskiya ba zan iya biyan Naira dubu 35 daga Kalaba zuwa Kano ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Saboda haka nakan jira idan na ga ana lodin babbar motar da ta zo daukar garin rogo ko manja, sai in bi ta, domin suna yi mana rangwamen kudin mota.”

Taimakon su muke yi —Direbobi

Shamsu Attahiru, wani matashin direban babbar mota, ya shaida wa Aminiya cewa sau da yawa ba wai don samun kudi suke daukar fasinjojin ba, sai dai domin taimaka musu.

Ya ce, “Za ka ga mutum ya zo da kayansa yana rokon a taimaka masa a dauke shi, domin lokacin tafiya zuwa Arewa ya yi, amma ba shi da kudin mota. Wasu ma ko kudin guzuri ba su da shi. To irin wadannan babu yadda za ka yi face ka taimaka musu. Wani lokacin ma kai ne za ka kara da saya masa abinci a hanya,” in ji direban tirelar.

Ya kara da cewa, “Akwai wadanda kuma suke da kudi, amma ba su isa su biya kudin karamar mota ba. Saboda haka, mafi yawan lokaci taimako kawai muke yi musu. Yawancinsu suna cikin halin kunci da talauci, duk da cewa akwai wasu da son araha da wayo ne ke sa su hawa saman tirela, wato Waju,” in ji shi.

Shi kuwa Malam Audu Dabuwa, Shugaban kungiyar Direbobin Motocin Homa Bas masu lodi a yankin Isheri Kara a karkashin kungiyar Direbobi ta NURTW, ya shaida wa Aminiya cewa akwai matafiya da dama da ke hawa saman tirela alhali suna da kudin da za su biya su hau karamar mota, amma suna kyashin yin hakan.

“Za ka ga mutum ya daure kudi masu yawa a aljihunsa, amma ya je ya hau saman tirela saboda son araha da kuma wayon da yake yi wa kansa. Wannan kuwa shi ake kira wayon rashin wayo, domin mutum zai yi kwana uku ko fiye da haka a hanya, kuma idan ka kididdige kudin abincin da zai ci a hanya, za ka ga sun fi kudin motar haya da yake gudun biya.

“Wata babbar motar ma za ta iya lalacewa a hanya, wanda hakan zai sa su sauka su sake neman wata mota tare da biyan kudi a karo na biyu. Amma akwai wasu da talauci da rashin hali ne kawai ke tilasta musu bin motocin dakon kaya zuwa Arewa,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ba kowane dan ci-rani da ya zo Legas ne yake samun wadataccen kudi ba, domin akwai wadanda ko wajen kwana ba su da shi, balle a yi maganar ajiyar kudi.

“Idan wahala ta kori mutum zuwa Arewa, to ka ga ba shi da kudin mota. Wasu ma a sana’o’insu, ko da sun yi shekara guda ba lallai ne su iya tara kudin motar komawa gida ba. Wani yankan farce yake yi, wani kuma sana’ar goge takalma yake yi, wani kuwa rakiyar shanu ya zo yi. dan kudin da suka samu, idan sun cire kudin abinci da sauran bukatunsu, ba zai ba su damar biyan Naira dubu 30 zuwa 40 domin hawa karamar mota ba,” in ji Audu Dabuwa.

Ya ci gaba da cewa, “Saboda haka, irin wadannan mutane ba su da wani zabi face su rungumi hawa gwangwaro, duk da hadarin da ke tattare da yin hakan.”

Audu Dabuwa ya ce jami’an Hukumar Kiyaye Hadura ta kasa (FRSC) suna iya kokarinsu wajen tabbatar da cewa direbobin manyan motoci suna bin doka, tare da wayar da kan al’umma kan hadarin da ke tattare da hawa saman tirela.

“Sau da yawa irin wadannan motocin kan fita ne da daddare, lokacin da jami’an ba sa kan hanya. Mu a bangarenmu muna hada gwiwa da hukumar, muna gudanar da tarurruka da su. Suna jan kunnen direbobi da ’yan kamasho, amma lamarin ya ci tura.

“Wannan matsala ce mai wuyar magancewa. Kirana shi ne mahukunta su samar wa talakawa sauki, sannan jami’an tsaro da masu kula da hanya su rika sanya ido domin hana mutane jefa kansu cikin hadari,” in ji shi.

Wani direban tirela mai suna Suleman Sani, wanda wakilinmu ya tattauna da shi a Kalaba, Jihar Kuros Ribas, ya ce yawancin fasinjojin da suke dauka suna yi musu alfarma ne.

“Yawancin fasinjojin da muke dauka, alfarma muke yi musu. Kuma abin da muke karba daga hannun kowane mutum bai wuce Naira dubu 10 ba,” in ji shi.

Lokacin da ake loda mutane da saman wata tirela a tashar Isheri Kara

Shi ma Sani Kabo, wani direban babbar mota da ya kai kaya Kalaba kuma aka samu ana yi masa lodi zuwa Arewa, ya bayyana cewa masu motocin sun hana su daukar fasinjoji, amma tausayin halin da matafiyan ke ciki ne ke sanya shi daukar wasu daga cikinsu.

“Masu motocin sun kafa mana doka kada mu dauki fasinjoji, amma tausayawa ce ke sa ni daukar su saboda yadda suke zuwa suna neman taimako. Kuma ba na daukar fiye da mutum 12 zuwa 13, hakan ma domin in samu dan kudin da zan kashe a hanya ne, idan wata lalura ta taso. Wannan ne kawai ya sa nake daukar su,” in ji shi.

Sani Kabo ya kara da cewa, kasancewar mafi yawan tafiyarsu da daddare ake yi, ba sa fuskantar wata matsala sosai daga jami’an Hukumar Kiyaye Hadura.

“Amma lokaci zuwa lokaci akan samu jami’an Hukumar Shige da Fice da ke tsayar da mu domin bincikar fasinjojin da muka dauko, musamman game da mallakar Katin dan Ƙasa. Banda hakan, ba mu cika fuskantar wata matsala ba,” in ji shi.

Hatsarin da ke tattare da hawa tirela

Malam Audu Dabuwa, Shugaban kungiyar Direbobin Motocin Homa Bas masu lodi a yankin Isheri Kara, ya bayyana cewa baya ga yawan hadurran da ke tattare da hawa motar kaya domin yin doguwar tafiya, hakan ma babban ganganci ne da ke nuna rashin kula da muhimmancin lafiya da rayuwa.

“Sau da yawa za ka ga mutum yana saman kaya a bayan mota, barci ya kwashe shi, sai ya fado a tsakiyar tafiya. Direba ma ba ya sani, balle ya tsaya. A karshe sai ka ga ya mutu a hanya kamar kaza. A irin wannan yanayi ne za ka rika cin karo da gawarwaki a gefen hanya.

“Domin ana loda kaya fiye da kima a manyan motoci, sannan kuma a dora fasinjoji a saman kayan ba tare da wurin riko ba. Idan mota tana tafiya cikin gudu, tana iya watsar da mutane, ko kuma idan hatsari ya auku, a rasa rayuka da dama,” in ji shi.

Ya kara da cewa wasu fasinjojin sukan fara tafiya ne da nufin sauka a wani wuri da suka fada, amma idan an tsaya a hanya domin cin abinci ko shan mai, wasu kan sauka kafin a isa inda aka nufa su bace ba tare da sani ba.

“Ka san direba yana gaban mota, ba ya saukowa. Wani lokacin idan mai kaya ya zo domin duba kaya, sai a tarar babu kowa. Daga nan sai a fara bincike amma a rasa su.

“Sai daga baya a gano cewa wasu daga cikin fasinjojin ne suka boye ko suka tsere, har ma a wasu lokuta ake zargin su da satar kaya,” in ji shi.

Tirela babbar mota

Kalubale da muke fuskanta daga masu bin manyan motoci — FRSC

Jami’an Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) sun koka kan tarin matsalolin da suke fuskanta daga fasinjojin da ke bin manyan motoci domin yin balaguro.

Wani jami’in hukumar da Aminiya ta tattauna da shi, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa babban dalilan da ke sa mutane bin manyan motoci shi ne talauci da kuma karancin wayewar kai.

Ya ci gaba da cewa: “Yawancin hujjar da irin wadannan fasinjoji ke bayarwa idan muka hadu da su shi ne matsalar rashin kudi da neman sauki. Amma wannan ba hujja ba ce idan aka yi la’akari da hadarin da ke tattare da hawa saman manyan motoci.

“Misali, mutum zai ce idan zai yi tafiya tare da iyalinsa daga Kudu zuwa Arewa, zai kashe kusan Naira dubu 150 a karamar mota, amma a babbar mota zai iya kashe kusan Naira dubu 20 kawai.

“Amma ba ya la’akari da kwanakin da zai iya shafewa a hanya, musamman idan mota ta lalace ko aka samu wata matsala. A irin wannan yanayi, kudin abinci kadai zai iya kaiwa ninki uku ko hudu na abin da ya tanada. Ga kuma hadarin da ke tattare da hawa babbar mota, musamman wadda ke dauke da kaya,” in ji shi.

Jami’in ya kara da cewa, la’akari da lokutan aiki na hukumar tsakanin karfe 6 na safe zuwa 6 na yamma, hakan na sa wasu direbobin manyan motoci da ke karya doka wajen daukar fasinjoji su fi yin zirga-zirga da daddare domin kauce wa kama su ko tara.

“Ko da an tsayar da su da rana, wasu na kin tsayawa, wasu ma har suna gogar motocinmu suna wucewa da gudu. Wannan na faruwa ne saboda sun san doka ta hana mu bin mota idan ta ki tsayawa. Bugu da kari, ba mu da izinin daukar makami domin kare kanmu,” in ji shi.

Ya kara da cewa wata babbar matsala ita ce yadda wasu manyan motocin ke kasancewa mallakin ’yan siyasa ko masu kusanci da su.

“Idan muka kama direba, sai ya kira waya, daga sama kawai sai a kira mu a ce mu sake shi ya tafi. Wannan na daga cikin manyan kalubalen da muke fuskanta wajen gudanar da aikinmu kamar yadda doka ta ba mu,” in ji jami’in.

Ya ci gaba da cewa a da, hukumar tana da ikon bin mota idan ta ki tsayawa, amma saboda yawan hatsarurrukan da hakan ke haifarwa, an yi dokar da ta hana hakan.

“Saboda gudun kada mu haddasa hadari, kamar bugun mutane ko fadawa rami, aka hana mu bin motocin idan direbobi suka ki tsayawa,” in ji shi.

Mafita

Jami’in ya kuma bayyana rcewa, “dama guda da ta rage ita ce ta gyara dokokin hukumar, saboda maganar gaskiya yana da wuya a dakile wanna matsalar ba tare da yi wa dokokin da suka kafa hukumar kwaskawari ma ba.

“Akwai bukatar a ba da damar rufe hanya kamar yadda sojoji da ’yan sanda ke yi. Sannan  kuma a ba mu damar rike makami, don tsare kanmu. Idan hukumarmu ta samu wannan iko, to lallai za a samu nasara sosai.”

Ya kara da cewa, “Sai kuma a inganta tsarin sadarwa, ta yadda idan ka saba ka’ida a nan, za a kira jami’an tsaro da ke shinge na gaba, a sanar da su don su tsare ka tun gabanin ka isa.”

 

Daga Ibrahim B. Surajo da Adam Umar, Abuja, Abbas dalibi, Legas da Musa Kutama, Kalaba