Tafiye-tafiyen Buhari waje sun fara jawo cece-ku-ce

Ga dukkan alamu tafiye-tafiyen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke zuwa kasashen waje sun fara tayar da kura da cece-ku-ce, inda hatta ’yan takifen Buharin suka fara shiga sahun masu sukar tafiye-tafiyen, tare da yin rubuce-rubuce a kai.A karshen makon jiya fitacciyar ’yar jaridar nan kuma Editan Aminiya ta farko Hajiya A’isha Umar Yusuf ta […]

Tafiye-tafiyen Buhari waje sun fara jawo cece-ku-ce

Ga dukkan alamu tafiye-tafiyen da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke zuwa kasashen waje sun fara tayar da kura da cece-ku-ce, inda hatta ’yan takifen Buharin suka fara shiga sahun masu sukar tafiye-tafiyen, tare da yin rubuce-rubuce a kai.
A karshen makon jiya fitacciyar ’yar jaridar nan kuma Editan Aminiya ta farko Hajiya A’isha Umar Yusuf ta shiga sahun mutanen da sukar yawan fita waje da Shugaba Buhari ke yi a wani rubutu mai kanun “Gaskiya Shugaba Buhari, ba wannan muka zabe ka, ka yi ba,” a filinta na Another Dimension (Wata Sabuwa) na jaridar Daily Trust ta ran Asabar.
A cikin rubutun ta ce, ta yi waiwaye kan dalilan da suka jawo canjin da ya kawo Buhari gadon da kuma irin dimbin kalubalen da shi kansa ya ce ya gada daga gwamnatocin da suka gabata da uwa uba matsalar hare-haren Boko Haram, ta ce idan har taron kasashen Rainon Ingila a Malta ya zame tilas Shugaba Buhari ya halarta me zai hana ya tura Minista a Ma’aikatar Man Fetur ya wakilce shi a taron kasashe masu arzikin gas da aka gudanar a Iran. Ta yi tambayar cewa me ya sa bayan ya amshi gayyatar Teheran sai ya zarce zuwa taron Malta daga can kuma ya wuce Faransa kamar Najeriya ba ta cikin rikici? Ta kuma yi tambayar cewa tura Mataimakinsa Yemi Osinbajo zuwa Faransa ba zai wadatar ba ne. Ta ce ko tsohon Shugaba Obasanjo, wanda bai hadu da matsalolin da Shugaba Buhari ya hadu da su ba, an soke shi da kasancewa Shugaba mai son keta hazo. To yaya abin zai kasance ga wanda aka zabe shi a lokacin da kasa take cikin yaki da ’yan ta’adda kuma take kokarin gano yadda za ta magance kai hare-haren bama-bamai?
Ta ce, “Eh, muna sane da cewar da Shugaba Buhari ya yi na kada mu sanya ran wata mu’ujiza daga gare shi domin ba zai kawar da matsalolin cikin dare daya ba, kuma mun amince da hakan. Amma tabbas kasancewarsa tare da mu a daidai lokacin da muke fuskantar matsaloli zai karfafa mana gwiwa da tabbacin ci gaba da hakuri har a kawo karshen lamarin.
Sai ta bukaci na kusa da Shugaban kasa ciki har da tsohon shugabanta Malam Garba Shehu cewa su sanar da shi ’yan Najeriya ba sa jin dadin kan yadda ya koma shugaba mai son keta hazo wanda ba zai ce a’a ga duk wata dama ta fita kasar waje ba.
Kwatsam sai fitacciyar jaridar nan ta Intanet Sahara Reporters wadda daya ce daga cikin kafafen watsa labarai ’yan ga-ni-kashe-nin Buhari ta fitar da nata rahoton tana sukar tafiye-tafiyen Shugaba Buhari.
Jaridar wadda ta fi mayar da hankali kan kudin da ake narkawa a yayin tafiye-tafiyen wadanda suka kai sau 14 tun rantsar da shi a karshen watan Mayu, ta ce kwana biyu kafin haka ta ba da rahoton soke-soke da ’yan siyasa da masana ke yi kan yawan tafiye-tafiyen Shugaban a daidai lokacin da kasar ke cikin matsaloli da suka hada karancin man fetur da karuwar hare-haren Boko Haram da suke bukatar kular gaggawa da kuma sanya ido.
A cewar jaridar bincikenta ya gano tafiyar wuni biyu da Shugaban kasa Buhari ke yi ta lashe Dala dubu 350 (kimanin Naira miliyan 68) zuwa Dala dubu 500 (kimanin Naira miliyan 97). Daga nan sai ta jejjero kudin da aka kashe a yayin tafiye-tafiyen da Shugaban ya yi zuwa Iran da Faransa tare da bayyana cewa wasu kudaden da aka kashe ba ta samu bayansu ba, yayin da alawus din Shugaban kasa a kowane dare bai cikin abin da ta samu.
Jaridar ta ce jama’a sun shiga caccakar Shugaba Buhari kan yadda yake yawan fita kasashen waje a daidai lokacin  halin da take ciki na tsananin rashin man fetur da ci gaba da hare-haren Boko Haram da faduwar tattalin arziki da ya daga wa bankuna da sauran sassan kasuwanci hankali. Sai ta ce jihohi hudu kadai Shugaba Buhari ya ziyarta tun hawansa mulki. Kuma an sa ran zai je Jihar Legas kwana kafin fitarsa Malta don kaddamar da hekwafta da jiragen ruwa da motocin yaki da aikata miyagun ayyuka, amma hakan bai yiwu ba, bayan an takura wa jama’a tare da jawo cinkoson motoci.
Sai dai a martanin da Kakakin Shugaban kasa Malam Garba Shehu ya mayar kan cece-ku-cen da ta taso ya ce, ya ji mamakin yadda yake karanta shagube kan tafiye-tafiyen da Shugaba Buhari ke yi zuwa kasashen waje. Wani rubutu da ya fitar kuma aka buga a akasarin jaridun kasar nan mai taken: “Tafiye-tafiyen Buhari ba na kwasar garabasa ba ne,” ya lissafo kasashen da Buhari ya ziyarta da suka hada da Jamus da Afirka ta Kudu da Amurka da Nijar da Chadi da Kamaru da Benin da Ghana da Afirka ta Kudu da Indiya da Iran da kuma Malta, inda ya ce galibin tafiye-tafiyen kodai na Majalisar dinkin Duniya ne ko na Tarayyar Turai ko Tarayyar Afirka, kuma an yi su ne don halartar wani ayyananne taro ba wai ziyarar kasashen ba ne. Ya ce me ’yan Najeriya za su ce a lokacin da suka ga shugabannin duniya sun taru kamar yadda suka hadu a Faransa don tattauna dumamar yanayi a ranar Litinin amma ba su ga shugabansu ba? Sai ya ce, a duniyar diplomasiyya ganawa ta kut-da-kut a tsakanin shugabanni ta fi amfani da tasiri maimakon tura wakili. Ya ce, Buhari ya zo ne a lokacin da ’yan Najeriya ke tsananin bukatar canji, kuma wajen samar da wannan canji wajibi ne Shugaban ya aza harsashin hakan a ciki da wajen kasar nan, kuma shi ne abin da Buhari yake ta faman yi.
Shi ma jagoran Jam’iyyar APC ta kasa Cif Bola Tinubu ta hannun Shugaban Kwamitin Editocin jaridar The Nation, Sam Omatseye a wata sanarwa a ranar Litinin da ta gabata ya bukaci Buhari ya guji yin surutu ratata a duk lokacin da yake wajen kasar, kuma ya shaida masa cewa ’yan Najeriya sun fara kosawa da yawan tafiye-tafiyen Shugaban kasa. Ya ce akwai dimbin aikin da suka wajaba ya yi a cikin gida da suka hada da kawo karshen wahalar man fetur da ci gaba da kai hare-haren Boko Haram da yawan dauke wutar lantarki.
Cif Tinubu ya ce, kuskure ne Shugaban kasar ya rika shiru a cikin kasa, amma ya zama kamar sankira a waje.
Sai dai wani dan ga-ni-kashe- nin Buhari Malam Aminu Gamawa ya fadi a shfinsa na Facebook cewa: “Masu cewa Buhari yana yawo ba su san ma’anar yawo ba, kuma ba su fahimci shugabanci ba. Kuna tunanin dadi ne zai sa mai shekara 70 da wani abu tafiye-tafiye?”
Ya ce Najeriya ita ce kasar da tafi kowace yawan jama’a da karfin tattalin arziki a Nahiyar Afirka. “Domin dawo da martabarmu dole a dama da mu a abubuwan da ke faruwa a duniya. Bayan haka, wace kasa ce ya je babu dalili? In ka ga ya tafi taro gayyatarsa aka yi kuma ba shi kadai ne shugaban duniya da aka gayyata ba. Idan sauran kasashe sun je, me zai hana namu zuwa. Bayan haka, idan aka kwatanta tawagarsa da ta shugabannin da suka gabata sai ka ga ba ta wuce na wani Gwamnan ba. Kayan sawa ma har maimaitasu yake, saboda haka ba wani asarar kudi ake yi ba,” inji shi.
Ya kara da cewa “Kun ce ya zauna ya yi aiki, mene ne amfanin ministocinsa da sauran jami’an gwamnati? Idan ya ce shi kadai zai yi komai sai ku ce ya dawo da mulkin soja. Don haka ya kamata a yi masa adalci. Idan ya yi ba daidai ba za mu fada masa. Amma ban ga wani laifi a wadannan tafiye-tafiye da ya yi ba zuwa yanzu. Idan da gayyatarsa ake ba ya zuwa da mutane sun fara korafi. Al’amarin jama’a da shugabanci sai hakuri. Wanda ba ya sonka babu wani abu da za ka yi ka burge shi.”