Tafkin Gwakuru: Wurin da ke makare da kifaye amma ba a ci

Rafin Gwakuru wani dan karamin tafki ne ko kududdufi da ke yankin Kagarko Ta Kudu a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.Takfin wanda yake da tsohon tarihi da abubuwan al’ajabi iri-iri, shi ne yake shayar da mutanen Kagarko gaba daya ruwa kuma bai taba konewa ba rani da damina, duk da cewa babu ta inda […]

Tafkin Gwakuru: Wurin da ke makare da kifaye amma ba a ci

Rafin Gwakuru wani dan karamin tafki ne ko kududdufi da ke yankin Kagarko Ta Kudu a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.
Takfin wanda yake da tsohon tarihi da abubuwan al’ajabi iri-iri, shi ne yake shayar da mutanen Kagarko gaba daya ruwa kuma bai taba konewa ba rani da damina, duk da cewa babu ta inda yake da wata mahada da wani rafi.
Ruwan yana kewaye ne da wadansu bishiyoyi manya, a gefensa kuma wadansu ‘yan ciyayi ne da suka yi wani sunkuru, ruwansa kuma tar-tar yake, wanda ya sanya ake iya ganin abubuwan da ke kasar rowan. Sai dai idan an yi ruwan sama ruwan kan jirkice ya zama ja. Akwai kifaye iri-iri masu ban sha’awa da kuma wadansu macizai launi-launi da za ka yi ta ganinsu suna ta watayawa a cikin rowan, kuma a haka mutanen yankin ke yin harkokinsu a wajen tare da diban ruwa ba tare da wadannan macizan sun cutar da su ba.
A lokacin da wakilinmu na Kudancin Kaduna ya kai ziyara  wajen, ya samu tattaunawa da wadansu daga cikin mazauna wurin, inda Malam Aliyu Ibrahim, Shattiman Hakimin Gwakuru, ya bayyana cewa a duk shekara ana zuwa yasan wannan ruwa sau daya, inda maza da mata, yara da tsofaffi kan hadu a wajen ana kade-kade, yayin da shi kuma Magajin Rafin ya kan zo da wata ‘yar tukunya dauke da wadansu magunguna da za a ba duk wanda ke wajen, daga nan sai ya kwaso duk kifaye da macizan da ke cikin ruwan ya zuba su a tukunyar, idan an gama yasar sai ya mayar da su.
Ya ci gaba da cewa; “duk wadannan kifayen da ka gani ba a cinsu. Kamar shekaru ishirin da suka wuce akwai wata ‘yar kabilar Ibo da ake kira Ngozi da ta zo wajen wata ‘yar uwarta daga jihar Abiya, sai aka aike ta debo ruwa a wajen, to da ta ga kifayen sai ta zaci kamar sauran kifaye ne, sai kawai ta kama wani guda daya ta dauko ta je gida ta yayyanka shi gunduwa-gunduwa, sannan ta dora a kan wuta domin dafawa.  Zuwa can bayan wani lokaci da ta je ta bude tukunyar sai ta ga wannan kifin ya koma ya hade kamar yadda ta dauko shi a cikin rafin. In takaita maka labari, a wannan ranar dai matar nan ba ta kwana da rai ba.’’
Sarkin Rafin Gwakuru, Sa’idu Madauci Kagarko, wanda shi ne ke kula da wadannan kifaye da macizan da duk abin da ya shafi takfin, ya shaida wa Aminiya cewa ya gaji wannan sarauta ne daga wajen kakanninsa fiye da shekara dari biyu, wanda ya ce sarutar ta samo asali ne daga wata mata da ta zauna a wajen wacce ake kira Ya Sabulu. Ita dai wannan mata, kamar yadda ya ce, ba ta taba haihuwa ba, sai dai wani yaro da aka ba ta rikonsa,  wanda a karshe shi kuma ya gaje ta, bayan ta nuna masa duk abubuwan da ya jibanci takfin da abubuwan da ke cikinsa.
 Magajin Rafin wanda ya fito daga wannan tsatson, ya ci gaba da cewa, ‘’babu wani da zai taba maciji ko kifin da ke tafkin da sunan kashewa face ya mutu a wannan ranar.’’
Sarkin Rafin ya kuma ci gaba da cewa, duk mutumin da ya debi wannan ruwa sannan ya zo wajensa ya ba shi wadansu magunguna to in sha Allahu ko mece ce matsalarsa za ta kau.
A karshe Sarkin Rafin ya mika rokonsa ga gwamnatin jiha da ta tarayya da su waiwayi wannan waje su gyara shi, saboda tarihin da ke cike da wannan tafki don samar da kudin shiga, domin kasancewarsa wurin ziyarar da ke samun maziyarta daga ciki da wajen Najeriya, ya ce har turawa sun sha zuwa wannan waje. Don haka ya bukaci gwamnati da ta gyara ta kuma killace wajen don ci gaba da jawo hankalin ‘yan yawon bude ido da kan ziyarci wajen a kodayaushe. Ya ce ya aika wa karamar hukuma da bukatar hakan amma har yanzu ba ta ce komai  ba tukuna.