Tagadas: Maka da Malku
Makonni kofar hanci da suka arce na yi balaguro zuwa kasar Niyar Jari, can na dangana da sahara a babban birnin Tagadas, inda na koyo yadda ake make ’yar Gusau da make da malku. Hakika na baje na-mujiya na gano harkokin rayuwar al’umma wadda ta bambanta da tamu. Mutanen Tagadas ba su da damin Hauro, […]
Makonni kofar hanci da suka arce na yi balaguro zuwa kasar Niyar Jari, can na dangana da sahara a babban birnin Tagadas, inda na koyo yadda ake make ’yar Gusau da make da malku. Hakika na baje na-mujiya na gano harkokin rayuwar al’umma wadda ta bambanta da tamu. Mutanen Tagadas ba su da damin Hauro, amma suna fantamawa, suna shakatawa, wato gwargwadon damin matsabbanka, gwargwadon shagalinka. Hakika Tagadas ta kayatar da ni.
Tun daga rana ta sili da sili zuwa rana ta sili da manuniyar sama, ina ta walankewa a cikin Hamada can kasar masu doguwar dabba. Wannan balaguro da na yi, ya sanya saura kiris in shiga jerin Abzinawan Haurobiya, domin na motsa muka-muki, inda na cukwikuye toyayyen nonon doguwar dabba da dan iccen buda-baki. Uwa-uba na yi gamo da katar, inda muka hada na-mujiya da daliban makarantar Dodorido da ke Farfajiyar Amintattar jaridar kasar Haurobiya.
Jagoran tattaki zuwa Tagadas, shi ne Dokta Kogin Albarka, wanda ya kaimu har gidan Babban mutum mai rawani, Shugaban Masu fuskantar alkiblar kadaita Mahalicci da ibada a kasar Niyar Jari. Wannan shugaba ya nada Dokta Kogin Albarka a matsayin Gamji dan kwarai, don haka ’yan makarant suka mika mini marsa da goriyar gayyata, inda muka rankayya don taya shi farin ciki. Kodayake wannan al’amari bai yiwu ba, amma ko ba komai mun ga gari, mun shiga gararin balaguro, amma mun warwatre tamkar mun ci awara.
Mai zaman dirshan dai bai ga gari ba. Idan ma ya yi rashion sa’a, yana zaune zai afka cikin garari.
Masu yaren hau-hau wajen hawansa ba tare da sa-in-sa ba, sun ce da ruwan tumbi ake jan na kwakware. Don haka da na lula cikin Hamada babu abin da na rika dundume kururuna da sai Maka da Malku da Ca’ammas. Maka dai wani dunkulen curin alkama ne da muke kira makararra-rani. Shi kuwa Malku, kan rago ne ko na dan bunsuru, ake sarrafawa a tsoma shi a cikin miya. Ca’ammas kuwa tamkar wasa-wasa ce, don haka ban yi mamaki ba, tunda a makaranta muna raba ‘gurasa gami da masa ga wasa-wasa a zuba a kwanon tasa, ’yan kasa su yi kwasa ba wani wasa.’
Batu na-dokin karfe, na fasko cewa kudin Jamhuriyar Niyar Jari, sun ishi dan gari zaman gari, har ma ya samu na-jari. A birnin Tagadas akwai wurin kasuwancin bisashe, inda masu laluben na-koko ke ci a jikin kofato; akwai Artabun-zana, inda masu fasahar zane-zane da kere-kere ke kera abin hannunsu; sai kuma Toluwar kasuwa, inda ake hada-hadar cinikin tufafi da kayan dundume kururu.
Wani abokina, mai suna Muhammadu Hangar da ke zaune a birnin Tagadas, ya bayyana mini yadda al’ummar birninsu ke fafutika wajen yaki da fatara da talalar talauci, inda nusar da ni irin dabarun da suka yi ta hanyar hada karfi da karfe, suka kafa kasuwar Artabun-zana. Sun yi rumfuna kofar hanci da tsayuwa bisa kafa daya, inda kalla gungun mutane kwanciyar magirbi da manuniyar sama ke ayyukan kere-kere. Kuma a kwani gefe ana yi musu cinikin kayayyakin da suka kirkira.
Babban abin da mutum ba zai taba mantawa da shi ba, a duk sa’adda ya ziyarci birnin Tagadas, shi ne babbar Mafuskantar Alkiblar kadaita Mahalicci da ibada mai tsohon tarihi, wadda masana suka ce an ginata cikin shekaru kwanciyar magirbi da zagaye da zagaye da suka shude. Babban abin ta’ajibi game da wanna mafuskantar alkibla, ita ce an ginata da laka, amma duk yunkurin da mmutane suka yi don mayar da ita ta zamani, al’amarin ya ci tura.
A daidai lokacin da nike yunkurin karkarewa, sai kawai ga wancan yaron na bayan kango ya zo yana tambayata ko mene ne ca’ammas? Ni dai ban ba shi amsa ba, amma abin da nike so da daukacin masu rausayawa a bayan kango, shi ne su tara ‘yan matsabbansu, su yi balaguro zuwa birnin Tagadas. Don a can ake samun ca’ammas a cacumeta da muka-muki; a can ake dumdume kururu da maka, har a make ’yar Gusau; a can ake kwasar lagwadar malku. Kai GizBaba idan ba ka san hanya ba, to ka zo ka yi biyayya, ni kuwa in taimaka in cilaka zuwa Tagadas.
Wata rna zan sake lulawa cikin Hamada har sai na dangana da Tagadas. Ina sha’awar wannan birni mai ban ta’ajibi. ’yan makaranta wadanda suka ziyarci Tagadas ina yi mana ban gajiya. Su kuwa wadancan da ba su samu damar ziyara ba, muna fatan za su zo mu nusar da su hanya. To kun ji!