Tagwaye sun kirkiri rusho mai amfani da ruwa a Kano
Wasu tagwaye a Jihar Kano sun kirkiri rusho wanda yake amfani da ruwa da fetur yana yin girki na tsawon awanni biyar. Hassan Muhammad Nawad da Usaini Muhammad Nawad ‘yan biyu ne masu shekaru 14 wanda suke kokarin cin gajiyar fasahar zamani ta hanyar kere-kere. Magidanci ya maka dan uwansa a kotu kan abinci Kotu […]
Wasu tagwaye a Jihar Kano sun kirkiri rusho wanda yake amfani da ruwa da fetur yana yin girki na tsawon awanni biyar.
Hassan Muhammad Nawad da Usaini Muhammad Nawad ‘yan biyu ne masu shekaru 14 wanda suke kokarin cin gajiyar fasahar zamani ta hanyar kere-kere.
- Magidanci ya maka dan uwansa a kotu kan abinci
- Kotu ta tabbatar da Sanwo-Olu a matsayin halastaccen Gwamnan Legas
Rishon wanda ake yi wa injinsa caji, yana da batiri wanda yake wana injin, inda shi kuma injin yake juya ruwan da fetur wanda shi ne yake bada wutar.
A zantawar su da Aminiya, tagwayen sun bayyana cewar sun dade suna tunanin kirkiro wani abu da zai amfanar da al’umma ta hanyar kere-kere.
A cewarsu, suna tattauna abubuwan da suke fatan yi a tsakaninsu a lokacin da suka zo barci, ko kuma yayin da suke wasa.
Haka kuma, sun ce iyayensu suna karfafa musu gwiwa wajen tabbatar da abubuwan da suke kokarin aiwatarwa.
Hassan ya ce sun fara tunanin kir-kiro wannan rusho ne shekaru biyar da suka wuce, wato tun suna makarantar firamare.
Kuma “ina yawan yin tunani a kan yadda ake amfani da gas ya ba da wuta ta griki, da kuma hanyoyin da za a bi domin saukaka abin.
“Hakan ne ya sa muka fara wannan, kuma ga shi yau ya kammala.
“Sai dai a wannan rusho namu, ruwan da fetur basa raguwa.
“Lita daya ta fetur za ta iya kaiwa wata ba ta kare ba. Fetur din da ruwan ana canja su ne idan sun yi baki, amma ba don sun kare ba. Kuma za su iya kaiwa shekara ba su yi baki ba.
“Shi wannan injin shi yake juya ruwan da fetur, wanda suke ba da wutar ta girki. Matukar akwai caji a batirin shikenan zai yi aiki ba tare da komai ba,” inji shi.
A cewar dan uwansa, Usaini, “Ruwan ba wai kamar sauran ruwa ba ne. Ana saka gishiri da alumun wanda yake zaman daya daga sinadaran da suke bayar da iskar da take zama wutar.”
Ya ce duba da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki, wannan kir-kira da suka yi za ta samar da sauki ga al’umma matukar an bunkasa shi kuma an yi amfani da shi yadda ya dace.
Ya kara da cewa fatansu a ko da yaushe shi ne ganin yara da matasa sun samar da sauyi ta hanyar yin amfani da kwakwalwarsu a kasar nan.
Sannan kuma sun ce suna da burin samar da hanyoyin saukaka rayuwa ga al’umma.
Hassan da Usaini wanda yanzu haka suke matakin karatun Sakandire a aji na biyu, sun kirkiro injin feshin maganin gona wanda ake masa caji.
Injin ana amfani da shi wajen feshi a gona ko a lambu domin saukaka hanyar ba tare da an yi amfani da hannu ba wajen feshin.
Abin da muke shirin kikira na gaba
Acewar ‘yan biyun a yanzu haka suna kan aiki domin samar da batiri wanda zai bada wuta makamanciyar ta lantarki wato (A.c) duka dai domin saukakawa al’umma wajen gudanar da rayuwa.
“A yanzu haka wannan aiki ya yi nisa. Muna so mu samar da batiri wanda zai iya daukar fanka, firinji da sauransu domin rage yawan dogaro da wutar lantarki.
“Kuma wannan inji yana karfin ba da wuta kwatankwacin ta lantarki kusan ma’uni 12 na volt.
“Amma a yanzu haka aikin ya tsaya sakamakon rashin wasu kayan aikin. Amma a yanzu haka ana kokarin samar da su. Da zarar an same su za mu ci gaba.”
Burinmu na rayuwa
Da suke bayyana kudurinsu da brusinsu na rayuwa, ‘yan biyun sun bayyana cewar sunaso su karanci fannin kere-kere a Jami’a, inda kuma sukeso suje kasr waje domin koyon wasu ayyukan a zahiri.
“Babban abin da muke bukata yanzu shi ne a taimake mu ta hanyoyi da dama, kamar samar mana da kayan aiki, ba mu kwarin gwiwa da kuma kokarin ganin an fadada abubuwan da muka yi ta yadda za a fara amfani da su.
“Muna ganin yadda kananan yara suke bajinta wajen kere-kere a wasu kasashen. Muna fatan muma wata rana mu kasance haka,” injisu.
A karshe sun yi kira ga yara da matasa masu basirar kere-kere da kada su gajiya, su kuma ci gaba da jajircewa domin ganin an samar da ci gaban kasar nan ta fannin.
Haka nan, sun yi godiya ga Cibiyar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta CITAD bisa goyon baya da kuma kayan aiki da wurin gudanar da aiki da ta ba su.