Tagwaye sun samu rashin jituwa bayan shekara 20 suna amfani da lasisin tuki daya

Wadansu tagwaye a kasar China da suke da kama sosai da juna da hakan ya sanya suke amfani da lasisin tukin mota daya, sun samu rashin jituwa bayan shekara 20 suna amfani da lasisin. Idan kamannin tagwaye ta yi iri daya sosai daya na iya aikata laifi daga bisani a kama wanda ba shi ya […]

Tagwaye sun samu rashin jituwa bayan shekara 20 suna amfani da lasisin tuki daya

Tagwayen da ke amfani da lasisin tuqi xaya

Wadansu tagwaye a kasar China da suke da kama sosai da juna da hakan ya sanya suke amfani da lasisin tukin mota daya, sun samu rashin jituwa bayan shekara 20 suna amfani da lasisin. Idan kamannin tagwaye ta yi iri daya sosai daya na iya aikata laifi daga bisani a kama wanda ba shi ya aikata laifin ba, musamman lokacin da suke cikin kuruciya.

Wadannan tagwayen da suka dade suna amfani da lasisin tuki daya maimakon kowanne ya mallaki nasa, hukumar da ke da alhakin bincike wannan lamari sun kama tagwayen.

An yi ta yada hoton bidiyon tagwayen da suke garin Yan. Sakamakon rashin jituwar da suke yawan samu idan aka zo amfani da mota wadda ake da bukatar lasisin tuki, tun farko idan daya daga cikinsu ya batar da nasa, sai ya yi amfani da na dan uwansa. Duk da yake yana da matukar wahala wajen sabunta lasisin tuki, amma haka tagwayen suke kokarin amfani da lasisi daya a shekarun.

Tagwayen sun dade da batar da lasisin tukin u na ainihi. Kuma a duk lokacin da dayan cikin tagwayen yake da bukatar amfani da lasisin, sai ya dauki na dan uwansa, yayin da su kuma tagwayen suke ci gaba da amfani da lasisi daya kasancewar kamannin da suke da ita, har sai da wata rana ’yan sanda suka gano cewa, daya daga cikin tagwayen na amfani da lasisin da hukuma ta dakatar.

Daya daga cikin tagwayen ne ya tona asirinsu, ina ya nuna cewa, su ba tagwaye ba ne wa da kane ne kuma ya mika lasisin tukin da ke hannunsa ga dan sanda. Dan sandan ya koma cikin motarsa ya gwada lasisin  a na’urar tattara bayanai inda ta nuna cewa, mutum biyu ne ke amfani da lasisin. Akwai wata alama daya da ta bayyana bayanan mutum biyu, wadda ta hada da gashin kai, daya daga cikin tagwayen ya rage sumarsa yayin da dayan kuma bai rage ba. Dan sandan ya koma cikin motarsa ya bai wa daya daga cikin tagwayen umarnin ya cire malafar da ya sa, hakan ya tabbatar masa da binciken da yake yi musu.

“Duk da yake tagwayen sun yi kama da juna, amma akwai abin da ya bambanta su da ya hada da girman jiki da yawan gashin da daya ya bari,” inji dan sandan mai suna Zhao Din da ke sashin ’yan sandan da ke lura da ababen hawa a Lardin Ken.

Babban daga cikin tagwayen an yi masa tarar Dala  298 (kimanin Naira dubu 107 da 280) kan laifin amfani da lasisin tukin da aka dakatar. Daga bisani ya bayyana wa dan sandan cewa, shi da dan uwansa sun kai sama da shekara 20 suna amfani da lasisin tuki daya.