Tagwayen da aka haifa a shekara daban-daban

Wasu iyalai a Jihar New Jersey ta Amurka sun shiga sabuwar shekarar 2024 cikin jin dadi da murna.

Tagwayen da aka haifa a shekara daban-daban

Tagwaye Ezra da Azikiel da aka haifa a shekara daban-daban

Wasu iyalai a Jihar New Jersey ta Amurka sun shiga sabuwar shekarar 2024 cikin jin dadi da murna inda suka haifi tagwaye, sai dai jariran an haife su ne a shekara daban-daban.

Wanda aka fara haifa mai suna Ezra an haife shi ne da misalin karfe 11:48 na jajibarin sabuwar shekarar, yayin da dan uwansa Ezikiel aka haife shi bayan minti 40 da misalin karfe 12:28 na ranar sabuwar shekarar Miladiyya ta 2024.

An haifi tagwayen ne a Asibitin Virtua Voorhees Hospital da ke South Jersey, inda iyayen suka ce suna cike da ‘murnar’ wannan muhimmin lokaci.

“Mahaifan (biyu) Eve da Billy suna cike da farin cikin cewa tagwayensu maza suna cikin koshin lafiya, kuma za su samu labari mai dadi da za a ba su game da ranar haihuwarsu,” in ji Asibitin Birtua Health.

Kuma wani abin sha’awa babban dan wato Ezra an haife shi ne a daidai ranar da aka haifi mahaifinsa, wanda shi ma aka haife shi a jajibarin sabuwar shekara, kamar yadda kafar labarai ta NBC ta ruwaito.

A wani labarin kuma, tagwayen Kirsimeti ne aka haifa a ranaku daban-daban. Iyayen tagwayen sun samu karuwar ce mako hudu kafin ranar da aka sa ran mai jegon za ta haihu.

Mahaifan Adeeka Ali da mijinta Faisal Imran da suke zaune a garin Livingston na kasar Scotland, sun je asibiti ne jajibarin Kirsimeti, inda matar ta haifi namiji mai suna Jami da ’yar uwarsa Rumi a cikin awa daya, sai dai kuma a ranaku daban-daban.

An haifi Jami da misalin karfe 11:44 na dare a jajibarin Kirsimeti, yayin da aka haifi abokiyar tagwancinsa Rumi da misalin karfe 12:27 na dare a ranar Kirsimeti.

Kadan ya rage Rumi ta zamo wadda aka fara haifa a ranar Kirsimeti a Scotland, sai dai Eliza Shearer ta samu kambin bayan da aka haife ta da misalin karfe 12:18 na daren Kirsimetin.

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya

Trump ya bayar da umarnin kamen ’yan gudun hijira a Amurka

Tags