Tahir Fadlallah: Mai otal din Tahir Guest Palace da ke Kano ya rasu
Dan asalin kasar Lebanon, ya bar wasiyya duk inda ya rasu a binne gawarsa a Kano
Allah Ya yi wa attajirin Kano kuma mai kamfanin Tahir Guest Palace, Tahir Fadlallah rasuwa a safiyar Juma’a.
Tahir Fadlallah wanda dan asalin kasar Lebanon ne, ya rasu ne yana da shekara 74 bayan ya yi fama da rashin lafiya.
- NAJERIYA A YAU: Hukunce-Hukuncen Zakatul Fitr
- ’Yan bindiga sun saki hoton jaririyar da fasinjar jirgin kasan Abuja ta haifa a hannunsu
Attajirin wanda ya shafe shekara 72 a Kano, ya rasu ne a wani asibiti da ke kasar Lebanon, inda aka yi jinyarsa.
A ranar Asabar ake sa ran isowar gawarsa Najeriya domin jana’iza da kuma binne ta a Kano.
Mai kamfanin na Tahir Guest Palace, ya bar wa iyalansa wasiyya cewa a binne gawarsa a Kano, ko a ina ya rasu.
Kafin rasuwarsa, ya kasance shugaban kungiyar ’yan kasar Lebanon mazauna Najeriya.
Ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya biyar da kuma cikoki 10.
A ranar 5 ga Fabrairu, 1948 aka haife shi a Beirut, babban birnin kasar Lebanon.
Bayan shekara biyu da haihuwarsa iyayensa suka dawo Kano da zama tare da shi.