Taimakon al’umma ne burina – Zainab Muntari Bello

Tarihina: Sunana Zainab Muntari Bello. Sunan mahaifina marigayi Alhaji Amadu Bahago. An haife ni a 1945 a garin Minna, Jihar Neja. A garin na yi makarantar firamare, daga nan sai na tafi shahararriyar makarantar mai suna kueen Elizabeth a Ilorin don karatun babbar takardar shaidar kammala makaranta (HSC) a 1965. Sai aka yi mini aure. […]

Taimakon al’umma ne burina – Zainab Muntari Bello
Taimakon al’umma ne burina – Zainab Muntari Bello

Tarihina:

Sunana Zainab Muntari Bello. Sunan mahaifina marigayi Alhaji Amadu Bahago. An haife ni a 1945 a garin Minna, Jihar Neja. A garin na yi makarantar firamare, daga nan sai na tafi shahararriyar makarantar mai suna kueen Elizabeth a Ilorin don karatun babbar takardar shaidar kammala makaranta (HSC) a 1965. Sai aka yi mini aure. Na je Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga 1965 zuwa 1967 inda na karanta fannin ilimi da tarihi. To daga ABU na dan fara aiki a kueen Amina, Zariya. Daga nan sai na zama shugabar makarantar mata na tsawon shekara guda a nan Minna. Shi kuma maigidana an ba shi kwangilar sayo abinci irin su shinkafa da masara da dawa da sauransu a Hukumar Sayen Hatsi  (Grains Broad), saboda a lokacin ana karancin abinci. Muna nan tare da maigidana Allah Ya jikansa da rahama sai aka dauke shi aiki a Legas a Bankin Amurka domin da ma sha’anin kudi ya karanta. To daga Bankin Amurka sai ya koma aiki a Bankin Sabanna, a haka dai har lokacin ajiye aikinsa ya yi, ya ajiye. To muna cikin tunanin yaya za a yi,sai tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida a lokacin yana mulki ya kira maigidana ya ce, to yanzu dai hedkwata ta koma Abuja, ba kuma za mu tafi mu bar kudi a baya ba, saboda haka daga nan sai Abuja. A haka har ya bar aikin baki daya. Ni kuma sai na ci gaba da aikina a hukumar bayar da tallafin karatu aka kuma ba ni wuri na musamman tare da wadansu malamai. Kafin in bar su sauran malaman su ci gaba. Sai da na je garuruwa da dama ,domin ka san sai an yi ganawar ido da ido da wanda za a ba tallafin. Sai an san shi wane ne, daga ina yake, ina za shi karatu? Rasha zai tafi ko Birazil da sauransu. Da ni dai aka fara yin wannan aikin wanda zan ce har yanzu ana ci gaba da yin sa. daliban da suka yo karatun Dokta duk sai suka ki dawowa gida, suka kama aiki a can kasashen da suka yi karatun ko wata kasar daban. Amma dai ba su dawo nan gida Najeriya ba don su yi aiki. 

To amma kuma duk lokacin da wadansu daga cikinsu suka zo ganin gida sukan yi kokarin a kai su inda nake, ni kuma sai in ce a’a, su yi zamansu ba sai sun ganni ba. Ni dai aiki ne na yi kuma ina amsar albashina don ba kyauta na yi ba. Saboda haka, komai za ka yi ka rike amana. 

Rayuwar yarinta:

To ni dai ba zan ce na sha wata wahala ko gwagwarmayar yarinta ba, musamman a batun neman ilimi. Dalili kuwa shi ne,a garinmu akwai jirgin kasa kafin ya gangara zuwa Abuja. Saboda haka, a duk lokacin da zan tafi makaranta can Ilorin sai a dauko ni a hannu a kawo ni tashar jirgin, in shiga tare da sauran kawayena wadanda suka fito daga Kano da Kaduna da sauransu. Idan muka je can Ilorin kuma, sai makaranta ta turo mota a zo a dauke mu zuwa makaranta. Kuma ilimin a wancan lokacin kyauta ne ba kamar yanzu ba. Gaskiya mun yi zumunci sosai ba tare da nuna bambanci ko matsayi ba musamman a kan abin da ya shafi mukami na waje ko na cikin makaranta ba. Muna tamkar uwa daya uba daya.

Kasashen da na ziyarta:

A lokacin da nake aiki na je kasashen waje, irin su China da Turkiyya da Malesiya da sauransu, saboda tafiya da daliban ba zai yiwu a tafi da hamsin a lokaci guda ba sai dai a raba su kashi-kashi. To sai in sanya malamaina wannan ya je nan wancan ya je can. A haka dai na yi ta yi har lokacin ajiye aiki ya yi na kuma ajiye. Na bar aiki ne a lokacin da na cika shekara sittin kamar yadda doka ta ce.

Abin da na fi ba muhimmanci:

Zaman lafiya da jama’a da kuma taimako da abin da nake da shi komai kankantarsa. Kula da ’yan uwa da kuma wadanda suka zo neman taimako. A nan ko da ba ni da abin da zan bayar zan yi musu jawabi na ban hakuri don komai kudinka wata rana za a samu ranar da babu.

kungiyoyin da nake ciki:

Ina cikin kungiyar nan ta shirin kyautata rayuwar matan karkara wadda marigayiya matar tsohon Shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ta kafa, wato Uwargida Maryam Babangida. Ina daga cikin manyan da suka tafiyar da kungiyar. 

Mun yi yawo a garuruwa a wajen fadakar da mata a kan yadda za su rika biyayya da yadda za su tashi domin su nemi na kansu. Na kuma shiga kungiyar da Mai shari’a Fati Abubakar ta kafa da dai sauran kungiyoyi. 

Ita ma cibiyar addini ai tamkar kungiya ce mai zaman kanta. To a nan ma sai da na zauna da jama’a, tunda ba na aiki sai na ga wannan wurin ko in ce filin, (bayan na yanke shawara) a zo a gina masallaci da makarantar Islamiyya da kuma boko.

Saboda na lura yara ba su cika cin jarrabawa ba, to idan za a samu malaman da za su rika koya musu koda a cikin wata uku ne, ka ga za a samu ci gaba. Kuma ka ga karatun addini yana da muhimmaci. Mutum zai karanta kur’ani har ma ya haddace wasu surori, to in ana son a gane abin da sura ke nufi ko take magana a kai, ka ga a Islamiyya za a koya sosai.

Rayuwar mata:

A gaskiya mata na kokari sosai don yawancin gidaje a yanzu in ka je za ka tarar mafi yawan matan suna da ilimin fuskokin biyu komai karancinsa. Ka ga a yanzu ana samun mata a fannoni iri daban-daban, misali a wajen aikin kiwon lafiya da koyarwa da kuma samun masu yin wa’azi ko da’awa da sauran irinsu.

Matsaloli:

To duk da dai ba za ka shiga cikin kowa ka san abin da yake ciki ba, amma dai babbar matsalar ita ce, yawancin wadansu maza suna takura wa matansu ta hana su yin aiki. Wadansu kuma idan suna da abokan zama hakan na iya zama matsala har sai an samu an daidaita domin mazan ke da hakki da hali tare da ikon daidaita gidajensu. Haka kuma ake samun irin wannan matsalar a tsakanin zaman mai ilimi da marar ilmi, wanda an san ba za a zamo duk iri daya ba.

Shawara:

To babbar shawarata a nan ita ce  mata duk inda suke su yi kokarin neman ilimi ta fuskokin biyu, wato na addini da na zamani. Sannan ko da ba a je aikin ofis ba, to a nemi sana’a. Amma ba daidai ba ne a rika zama ana yin gulma domin an wuce wurin a yanzu. Mata su kama kansu, su zama masu biyayya ga mazansu, sannan su kara sa ido ga yaransu a wannan lokaci musamman saboda juyin zamani, sai ana lura da bayar da kyakkyawar kula.