Taimakon gajiyayyu na rage aikata laifuka – Kwamishinan ’yan sanda

Wani matashi mara galihu mai suna Ayoola da ke yawo domin tsintar tsofaffin abubuwa a cikin bola a Ibadan, wanda ’ya’yansa biyu suka rasa rayukansu a rana daya a dalilin fatara da yunwa; ya samu tallafin kayan abinci da sabon babur da zai rika amfani da shi wajen neman abun dogaro. Kwamishinan ’yan sanda na […]

Taimakon gajiyayyu na rage aikata laifuka – Kwamishinan ’yan sanda
Taimakon gajiyayyu na rage aikata laifuka – Kwamishinan ’yan sanda

Wani matashi mara galihu mai suna Ayoola da ke yawo domin tsintar tsofaffin abubuwa a cikin bola a Ibadan, wanda ’ya’yansa biyu suka rasa rayukansu a rana daya a dalilin fatara da yunwa; ya samu tallafin kayan abinci da sabon babur da zai rika amfani da shi wajen neman abun dogaro.

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo, Alhaji Muhammad Musa Katsina ne ya bayar da wannan taimako daga aljihunsa domin shiga sahun bayin Allah masu yin amfani da dukiyarsu wajen tallafa wa jama’a mabukata da ke cikin halin kaka-ni-kayi.
A hira da wakilinmu jim kadan bayan mika kayan abincin da makullin sabon babur ga wannan matashi a harabar cocin Celestial da ke Agbowo a birnin Ibadan, Kwamishinan ’yan sanda Muhammad Musa Katsina ya ce ya tausaya wa wannan mutumi da matarsa ne saboda labarin da ya samu cewa suna cikin kuncin rayuwa musamman yunwa da ta haifar da kamuwa da cututtuka ga ’ya’yan na su suka yi ba tare da samun mataimakin zuwa Asibiti domin ceto rayukansu ba.
Ya ce, idan ba a hanzarta taimaka wa wannan mutumin ba, yana iya samun kansa cikin miyagun mutane masu tayar da hankalin jama’a. “Saboda haka na yanke shawarar bayar da wannan tallafi da zai taimaka wajen rage radadin rashin da suka yi kuma zai tsame shi daga fadawa cikin tunanin aikata miyagun ayyuka” inji Kwamishinan, wanda ya umarci likitocin asibitin ’yan sanda dake Ibadan su dauki dawainiyar kula da lafiyar wannan mutum da matarsa mai goye da karamin yaro da juna biyu ba tare da sun biya ko kwabo ba har zuwa lokacin da za su murmure.
Da yake amsa wata tambaya Kwamishinan ya ce ya saba bayar da irin wannan taimako ga mabukatan da aka tabbatar da cewa suna bukatar abun dogaro da kai. Ya ce, a matsayinsa na Musulmi, yana bayar da taimakon ne a boye ba tare da duniya ta sani ba. “Daga cikin albashina nake bayar da irin wannan tallafi ga mabukata saboda Allah. Irin wannan taimako yana taimaka mana wajen samun nasarorin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin jama’a a Jihar Oyo. Mutane (farar hula) masu yawa suna ba mu muhimman labarai a dalilin yarda da amincewa da suka yi da salon ayyukan namu.”
A nan sai ya yi kira ga ’yan Najeriya musamman masu hali su yi amfani da dukiyarsu wajen taimaka wa marasa karfi da suke cikin halin ni ’ya su ta hanyar sama musu ayyuka da sana’o’i domin dogaro da kansu amma ba tara mutane a cikin gida ana raba musu abinci da ’yan kudaden cefanen yini daya ba. “Duk wanda ka samar masa aiki ko sana’a, to zai amince da mahukunta kuma zai zama darasi ga sauran bata gari da za su yi watsi da miyagun ayyukansu domin komawa ga madaidaiciyar hanyar rayuwa.” Inji shi.