Takaddama a Oyo: Olubadan na Ibadan ya yi amai ya lashe
Takaddama tsakanin Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo da Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji ta kawo karshe a lokacin da Olubadan ya halarci taron sarakunan jihar da Gwamna ya yi a makon jiya a Gidan Gwamnati a Ibadan. Gwamnan ya kira taron sarakunan ne domin neman goyon bayansu a kan kyautata tsaro da samar […]
Takaddama tsakanin Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo da Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji ta kawo karshe a lokacin da Olubadan ya halarci taron sarakunan jihar da Gwamna ya yi a makon jiya a Gidan Gwamnati a Ibadan.
Gwamnan ya kira taron sarakunan ne domin neman goyon bayansu a kan kyautata tsaro da samar da zaman lafiya da tattaunawa a kan muhimman ayyukan da gwamnatinsa ta aiwatar a baya da kuma neman shawararsu kan yadda za a gina ci gaban da zai amfani jihar a cikin shekara 25 masu zuwa.
Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron, Olubadan na Ibadan ya jinjina wa Gwamna Ajimobi kan irin muhimman ayyukan ci gaban jama’a da ya aiwatar a sassan na jihar. Sarkin ya yi fadi cikin raha cewa, Gwamna Ajimobi ya cancanci tazarce karo na 3 idan da tsarin mulkin kasa ya amince. Ya ce, “Lura da abubuwan ci gaba da na gane wa idanuna ya sa nake jinjina wa Gwamnan da neman ya sake zama Gwamna a zaben mai zuwa idan da tsarin mulki ya amince.”
Wadansu fitattun mutane ’yan asalin Ibadan ba su ji dadin wadannan kalamai da suka fito daga bakin Olubadan ba, wanda ya sa Basaraken ya ce shagube ne da raha ya yi bayan kwana 2 da fadin haka.
Oba ya ce kafofin labarai da suka yayata labarin cewa ya nemi Gwamna ya yi tazarce karo na 3, ba su fahimce shi ba. Ya ce ya yi wannan bayani ne cikin raha domin “A matsayina na Sarki, ba ni da iko ko karfi a kan zabe ko sake zaben kowa. Na fadi haka ne cikin raha a lokacin da muke gaisawa da Gwamna a wajen taron,” inji shi.
Oba Saliu Adetunji ya musanta karbar “Na goro” daga hannun Gwamnan kamar yadda wadansu ’yan birnin Ibadan suka fara zargi. Ya ce “Duk wanda yake da tabbatacciyar shaidar jingina wadannan kalamai da karbar “Na goro” daga hannun Gwamna ya fito ya nuna wa duniya.” Sarkin ya kara da cewa, “Idan ma Gwamna ya yi mana laifi to kuwa bai dace a mayar masa da mummunan martani daga bangarena ba.”
Idan ba a manta ba takaddama tsakanin Gwamna Ajimobi da Olubadan ta faro ne bara, lokacin da Gwamnan ya amince da daukaka darajar wasu hakimai zuwa matsayin sarakuna a masarautar Ibadan, wanda Olubadan ya ki amincewa da hakan. Sababbin sarakunan su 21 sun yi wani yunkuri na kawar da Olubadan daga karaga a wancan lokaci, wanda ya haifar da kace-nace a tsakanin Majalisar Olubadan da ofishin Gwamna.
Yanzu haka akwai kararraki 5 da suke gaban kotu a kan wannan jayayya tsakanin Gwamna da Sarki da ake hangen cewa akwai hannun wadansu fitattun ’yan siyasa a cikin wannan al’amari da ya ki ci, ya ki cinyewa.