Takaddama kan gadon kadarar Mandela ta kara zafi
Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta ki amincewa da karar da Winnie Madikizela-Mandela matar marigayi tsohon shugaban kasar Nelson Mandela ta shigar gaban kotu don ta mallaki kadarar marigayin da ke kauyen kunu.A karar da ta shigar gaban kotun, Madikizela-Mandela ta zargin marigayin mijinta da yin rijistar wata kadara ba ta hanyar da ta dace […]
Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta ki amincewa da karar da Winnie Madikizela-Mandela matar marigayi tsohon shugaban kasar Nelson Mandela ta shigar gaban kotu don ta mallaki kadarar marigayin da ke kauyen kunu.
A karar da ta shigar gaban kotun, Madikizela-Mandela ta zargin marigayin mijinta da yin rijistar wata kadara ba ta hanyar da ta dace ba, inda ya sanya sunansa ba tare da nata ba.
Idan za a tuna Mandela ya mutu kusan shekara daya ke nan, inda ya cire sunan Madikizela daga wasiyyar wadanda za su gaje shi.
An kiyasta kadarar marigayin da ke kauyen kunu za ta kai Dala miliyan 6.8. Ma’auratan sun shafe shekara 38 kafin aurensu ya mutu a shekarar 1996.
Madikizela ta shigar da karar ne tun a watan jiya don a bi mata kadinta, wato a mallaka mata kadarar da ta kira tata ce.
Ta ce tana zargin Mandela da yin sama da fadi lokacin da ya yi rijistar kadarar da sunansa kawai.
A karar da ta shigar gaban Babbar Kotun Mthatha ta ce marigayin ya yi amfani da dokar mallakar fili ta kasa wajen mallakar kadarar.
Lauyoyinta sun bukaci Shugaba Jacob Zuma da kuma Hukumar Bunkasa Karkara ta samar da sahihun takardu da za su bayyana yadda aka mallaki kadarar.
Mai magana da yawun shugaba Zuma, Mac Maharaj ya ce tuni babban mai shari’a ya bukaci a dakatar da sauraren karar har zuwa lokacin da shugaban kasa zai bada umarni kan batun.
Lauya Madikizela mai suna Mbuzo Notyesi ya ce suna da kwarin gwiwar samun nasara a shari’ar da suka shigar.
Ta ce kadararta ce, inda AbaThembu sarkin Buyelekhaya Dalindyebo ya mallaka mata a lokacin da Mandela yake zaman kaso.