Takaddama kan kwanan aure ta haddasa kisan kai
Ana tuhumar wani magidanci a Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa bisa zarginsa da haddasa mutuwar matarsa, bayan ya doke ta saboda takaddama a kan raba kwanan aure tsakaninta da kishiyarta a ranar 14 ga watan nan da muke ciki. Matar mai suna A’isha Musa da ke zaune a Unguwar Daurawa a Birnin Kudu, mijinta […]
Ana tuhumar wani magidanci a Birnin Kudu da ke Jihar Jigawa bisa zarginsa da haddasa mutuwar matarsa, bayan ya doke ta saboda takaddama a kan raba kwanan aure tsakaninta da kishiyarta a ranar 14 ga watan nan da muke ciki.
Matar mai suna A’isha Musa da ke zaune a Unguwar Daurawa a Birnin Kudu, mijinta ne mai suna Umar Haruna ya dawo daga wata tafiya, maimakon ya je gidanta, sai ya tafi gidan kishiyarta, Hafsa Umar, dalili ken an ta je gidan domin neman hakkinta na aure.
Kamar yadda bincike ya nuna, zuwan A’isha gidan ke da wuya sai ta hau mijin nata da fada, ta ce ai kwananta ne amma ya dauka ya kai wa amarya. Kakakin rundunar ’yan sanda na Jihar Jigawa tabbatar da labarin cewa ita amarya Hafsa ta ce wa mijinsu Umar ya tafi wajen uwargidan, ya sauke mata hakkinta, in ya so washegari ya dawo wajenta ya kwana, ya bi doka kamar yadda addini ya tanada. Bayan amarya ta sasanta su sun tafi wancan gidan sai sabuwar rigima ta hada su, inda shi kuma ya doke ta, lamarin da ya zo da karar kwana. Shi ne ya mijin ya kai ta asibitin Birnin Kudu domin ceton ranta, amma kafin aiki ya zo kanta tuni rai ya yi halinsa.
Kakakin ’yan sanda, SP Audu jinjiri ya kara da cewa, suna tsare das hi mijin da ake tuhuma, yana amsa tanbayoyi kuma da zarar sun kammala nasu bincike, za su gabatar da shi zuwa sashin binciken kwakwaf da ke hedikwatar ’yan sanda domin zurfafa bincike a kansa. Ya ce da zarar duka sassan biyu sun gama bincikensu, za su gurfanar da shi a gaban kotu domin hukunci.