Takaddama ta sarke game da shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar Osun

Tun bayan da sabon Ooni na Ife Oba Adeyeye ya karbi sandar mulki, wani abin da ya dauki hankalin Yarbawa, musamman a Jihar Osun shi ne, wanda zai zamo Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar, mukamin da aka ba Owa Obakin na Ijesha, wato Oba Gabriel Adekunle Aromolaran. Wata matsalar da ake ganin za ta kunno kai […]

Takaddama ta sarke game da shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar Osun
Takaddama ta sarke game da shugabancin Majalisar Sarakunan Jihar Osun

Tun bayan da sabon Ooni na Ife Oba Adeyeye ya karbi sandar mulki, wani abin da ya dauki hankalin Yarbawa, musamman a Jihar Osun shi ne, wanda zai zamo Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar, mukamin da aka ba Owa Obakin na Ijesha, wato Oba Gabriel Adekunle Aromolaran. Wata matsalar da ake ganin za ta kunno kai a lardin na Oduduwa, tuni dai Owa na Ijesha ya kira taron ’yan jarida, bayan kammala taron majalisar sarakunan da sukan yi a kowane wata, wanda ya gudana a garin Oshogbo, inda ya ce majalisar ta nada shi ya zama shugabanta bayan mutuwar Ooni Oba Okunade, kana ya kara da cewa Ataoja na Oshogbo Oba Jimoh Olanipekun ne ya tayar da maganar cewa tunda dai shi aka ba jagorancin majalisar, to shi zai ci gaba da jan ragamarta koda kuwa an nada sabon Ooni.
“Ni nake jagorantar taron Majalisar Sarakunan Jihar Osun a fadar tsohon Ooni Oba Okunade tun yana raye. Ni kuma ke zartarwa a bisa dalilan yawan shekarunsa,” inji Oba Aromorala, wanda ya yi alkawarin cewa ba zai ba sarakunan da suke goya masa baya kunya ba, kana zai yi aiki tukuru tare da gwamnatin Ra’uf Arebgesola domin ci  da ikhar gaba.
Da aka tambayeshi ko mene ne matsayin sabon Oonin idan shi ne shugaban majalisar? Sai ya ce sarakunan da suka ba shi ragamar jagorancinsu ne kawai za su iya ba da wannan amsa.
A nata bangaren cibiyar ci gaban Ile-ife, ta yi watsi da ikirarin Oba Aromorala ta kuma shawarce shi da ya guji yin abin da ya saba wa tarihi tun lokacin iyaye da kakanni, domin a cewar cibiyar, doka ce ta ba Ooni na Ife damar zama shugaban majalisar sarakunan jihar na dindindin, ba tare da  karba-karba ba.