Takaddama: Yadda aka sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango

A kwanakin baya ne aka kawo karshen takaddama tsakanin fitattun jaruman fina-finan Hausa, Ali Nuhu da kuma Adam A. Zango.Idan ba a manta ba, takaddama ta barke tsakanin jaruman watanni hudu da suka gabata bayan jaruma Rahama Sadau ta yi amfani da shafin Instgram wajen cin zarafin Zango, al’amarin da yaron Zango mai suna Ali […]

Takaddama: Yadda aka sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango
Takaddama: Yadda aka sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango

A kwanakin baya ne aka kawo karshen takaddama tsakanin fitattun jaruman fina-finan Hausa, Ali Nuhu da kuma Adam A. Zango.
Idan ba a manta ba, takaddama ta barke tsakanin jaruman watanni hudu da suka gabata bayan jaruma Rahama Sadau ta yi amfani da shafin Instgram wajen cin zarafin Zango, al’amarin da yaron Zango mai suna Ali Artwork ya rama wa ubangidansa a kan ubangidan jarumar wato Ali Nuhu. Daga nan wutar takaddamar ta ci gaba da ruruwa har ta kai da Zango ya yi hira da ’yan jarida hade da bayyana cewa ya yanke duk wata alaka tsakaninsa da Ali Nuhu.
Masu iya magana sun ce komai ya yi tsanani to zai yi sauki, inda hakan ya sanya a makonni biyu da suka gabata, aka sasanta jaruman bayan da aka yi zaman sulhu a Hotel din Gamji da ke Kaduna, a karkashin kwamitin sulhu, wanda Shugaban kungiyar ’yan fim ta MOPPAN, Malam Khalid Musa ya jagoranta.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Darakta kuma Furodusa Abu Sarki da Furodusa Tahir I. Tahir da Furodusa Abdul Amart da Darakta Sadik N. Mafia da kuma mai daukar hoto Isma’il M. Isma’il.
Wata majiya wadda ta halarci zaman sulhu ta bayyana wa Aminiya a lokacin zaman Malam Khalid ya bayyana muhimmancin zaman lafiya, yafiya da kuma hakuri da juna, sannan ya bayyana illar da ke tattare da rashin jituwa tsakanin juna.
Jaruman sun gabatar da jawabai masu daukar hankali, inda suka bayyana sabanin a matsayin aikin shaidan, sannan suka bayyana farin cikinsu ganin wannan rana da komai ya koma daidai.
A yayin zaman an kuma shirya abubuwan da suka shafi zumunci, inda za a yi taron shan ruwa a gidan Ali da kuma Zango.
Majiyar ta ce: “Ali Nuhu da Adam Zango sun fito dakin sulhu suna masu farin ciki da jin dadi. An shirya za a yi shan ruwa a gidan Zango ana jibi jajiberin Sallah, sannan Sallah saura kwana biyu kuma za a je gidan Ali Nuhu a Kano don shan ruwa.”
Majiyar ta bayyana akwai taron da jaruman za su halarta daban-daban a Yamai babban birnin Nijar, amma  sakamakon sulhun bangaren Zango za su je Kano gidan Ali, inda washegarin Sallah za su wuce Nijar gaba daya a matsayin iyali daya.
“Da tafiyar ba daya ba ce, amma yanzu mun dunkule ta, za mu tafi tare a matsayin iyali daya.” Inji majiyar.
Majiyar ta ce kwamitin ya shafe wata uku yana yunkurin sulhunta jaruman, inda Abu Sarki ne ya rika fadi tashi wajen ganin an sasanta, daga baya Isma’il M. Isma’il ya shigo ciki, ganin haka sai Tahir I. Tahir ya ba da goyon bayansa, sannan saura suka biyo baya, hakan ya sanya aka nada Malam Khalid a matsayin shugaban kwamitin sulhun.
Aminiya ta tambayi majiyar yaya batun su Rahama Sadau da kuma Ali Artwork da ake ganin su ne ummul’aba’isin rura wutar rikicin? “Salon da aka dauka wajen yin sulhun shi ne, mun yi amfani da iyayen gidansu ne, saboda idan ana maganar uba ai ba a maganar da, kowane uba a tunaninmu ya isa da gidansa. Muna tunanin Ali Nuhu ya isa da Rahama Sadau da duk wani yaro da ke karkashin kamfaninsa, haka shi ma Adamu muna tunanin yana da iko a kan Ali Artwork da iri-irensa, hakan ya sanya ba mu gayyaci yaransu ba, saboda kada abin ya zama da yarinta, ko ya zama ba yadda muke so ba, hakan ya sa muka yi zaman da iyayensu. Kowannensu zai koma ya gyara gidansa.”
Majiyar ta bayyana wa Aminiya tuni kamfanonin jaruman biyu suka shirya wa juna fim, inda nan ba da jimawa ba za a fara daukar wadannan fina-finai don tabbatar wa duniya sulhun ya tsaya da kafafunsa.
“Akwai fim yanzu na kamfanin Ali Nuhu wato FKD Production, Adamu ne babban jarumi, shi kuma Ali Nuhu zai tallafa masa, haka kuma shi ma kamfanin Prince Zango na Adam A Zango ya shirya wa Ali Nuhu fim, inda kuma Adamu zai tallafa masa.” Inji majiyar.
Rufa’i Ibrahim wani mai sharhi kan abubuwan da ke faruwa a masana’antar fim ta Kannywood ya bayyana shakkunsa game da sulhun, inda ya bayyana cewa yaran jaruman suke yin ruwa da tsaki wajen iza wutar rikicin.
Ya ce: “Idan ba ka manta ba ko lokacin da Artwork ya ci zarafin Ali Nuhu, yaransa irinsu Shamsu dan Iya da Garzali Miko ne suka kada suka raya sai da ’yan sanda suka kama shi, sannan a cikin hirar da Zango ya yi da ’yan jarida, ya bayyann yaran Ali ba su ba shi daraja, ya yi korafi kuma Ali bai dauki kwakkwaran mataki ba, don haka idan jaruman suka iya tankwara yaransu, to komai zai tafi daidai.”
Hashim Hassan ya bayyana sulhun abin farin ciki ne, kuma ya gamsu a wannan karon jaruman da gaske suke wajen kawo karshen sabanin da ke tsakaninsu.