Takaddamar iko na neman gwara kan sarakunan Hausawan Ibadan da Sasa

Jayayyar kan hurumin mulki da iko a tsakanin masarautun Hausawan Ibadan da Sasa a Jihar Oyo ta sake tashi a tsakanin Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ali Dahiru Zungeru da Sarkin Sasa kuma Sardaunan Yamma Alhaji Haruna Maiyasin.

Takaddamar iko na neman gwara kan sarakunan Hausawan Ibadan da Sasa

Jayayyar kan hurumin mulki da iko a tsakanin masarautun Hausawan Ibadan da Sasa a Jihar Oyo ta sake tashi a tsakanin Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ali Dahiru Zungeru da Sarkin Sasa kuma Sardaunan Yamma Alhaji Haruna Maiyasin.

Hakan ya sa Fadar Mai martaba Olubadan na Ibadan Oba Lekan Balogun ta shiga tsakani, inda ta nemi bangarorin biyu su kwantar da hankali domin guje wa barkewar rikici.

Haka hukumomin tsaro na ’yan sanda da DSS a jihar sun gayyaci bangarorin biyu domin dakile yiwuwar aukuwar hargitsi a tsakaninsu.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya gamo cewa, jayayyar ta fara zafi ne lokacin da Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin ya dauki matakin korar Shugaban Garejin Manyan Motoci na Alhaji Yaro Abubakar Akinyele daga ofishinsa da kuma kokarin nada wasu Hausawa a kan sarauta a garin Akinyele.

Hakan ne ya sa Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ali Dahiru Zungeru nuna rashin amincewa da korar da kuma nade-naden da Sarkin Sasa ke son yi.

Kuma take ya garzaya Fadar Olubadan na Ibadan inda ya mika korafi yana neman a taka wa Sarkin Sasa burki a kan matakan da yake dauka da ya ce za su iya tayar da zaune-tsaye a tsakanin al’ummar Hausawa, musamman saboda huruminsa ya tsaya ne kawai a Masarautar Hausawan Sasa, ba Masarautar Ibadan mai kunshe da kananan hukumomi 11 a Jihar Oyo ba.

Binciken ya nuna cewa bayan sauraron korafin, Fadar Olubadan ta fitar da sanarwa wacce ta aika wa kafofin labarai a Ibadan.

Sanarwar dauke da sa hannun Sakataren Labarai Mista Oladele Ogunsola ta ce Sarkin Hausawan Ibadan shi kadai ta sani a matsayin jagoran al’ummar Hausawa a wannan gari, kuma Unguwar Sasa da  Maiyasin yake jagorantar al’ummarsa a a karkashin Wakilin Olubadan, Baale Cif Amusa Ajani take.

Saboda haka Fadar Olubadan ba za ta amince da nade-naden da wasu shugabannin al’umma suke yi ba bisa ka’ida ba.

Sanarwar ta ce an dauki wannan mataki ne bayan korafin da Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ali Dahiru Zungeru ya kai mata.

Hakan ya sa Sarkin Hausawan Ibadan gayyatar sarakunan Hausawa da hakimai da dattijai zuwa taro na musamman a ranar Lahadin da ta gabata a fadarsa da ke Unguwar Sabo Ibadan.

Da yake yi wa Aminiya bayanin sakamakon bayan taron, Jarman Ibadan, Alhaji Danjuma Yakubu ya ce “taro ne na lalubo hanyar zama lafiya a tsakanin ’yan Arewa mazauna Masarautar Ibadan da Jihar Oyo baki daya.

“Duka mahalarta taron sun goyi bayan korafin da Sarkin Hausawa ya shigar a Fadar Olubadan da shiga tsakani da Olubadan ya yi domin samar da zama lafiya da kwanciyar hankali a Ibadan da Jihar Oyo.

“Taron bai amince da korar Shugaban Garejin Akinyele Alhaji Yaro Abubakar da Sarkin Sasa ya yi ba, kuma bai amince da nade-naden sarautu ba.

“Sai dai taron ya nemi dukkan sarakunan Hausawa a garuruwa daban-daban da hakimai su dauki matakin nuna soyayyar juna a tsakaninsu da dukkan ’yan Arewa da ke zaune a wannan sashe na Yarbawa tare da girmama doka da oda domin dorewar zama lafiya da guje wa aukuwar rikicin kabilanci da ya auku a Kasuwar Sasa da ya lakume rayukan daruruwan ’yan Arewa.”

Kokarin Aminiya don jin ta bakin Sarkin Sasa kuma Alhaji Haruna Maiyasin a kan wannan lamari ya ci tura.

Sai dai Sardaunan Samarin Yamma, Alhaji Haruna Bello Gambo ya ce, “Fadar Sarkin Sasa kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Hausawa a Jihohi 17 na Kudu ba ta samu wata takarda ta musamman daga Fadar Olubadan na Ibadan ba.

“Sai dai mun samu labarin da kafofin sada zumunta suke watsawa da muke zargin an kulla makirci ne domin a tayar da zaune -tsaye.

“A game da batun korar Shugaban Garejin Akinyele kuwa, kowa ya san cewa Sarkin Sasa ne ya nada shi a kan wannan mukami da ya kamata a rika yin zaben sabon shugaba bayan shekara hudu, amma Sarkin Sasa ya kyale shi a har tsawon shekara 16.

“Sannan an dauki matakin korar sa ne bayan korafin da jama’a suka rika kawowa zuwa Fadar Sarkin Sasa a kan takurawar da yake yi wa jama’a a garejin.

“Yanzu haka Sarkin Sasa ya kafa kwamitin da zai saurari shawarar jama’a a kan wanda ya cancanta a nada a matsayin sabon Shugaban Garejin na Akinyele,” in ji shi.

 

 

Aminiya ta gano cewa garin Akinyele da ke kusa da Ibadan wuri ne da ya kunshi muhimman abubuwa hudu da suka hada da garejin manya da kananan motoci da ke zirga-zirga a tsakanin Arewa da Kudu da babbar karar shanu ta Ibadan da kasuwar awaki da kuma sabuwar kasuwar kayan gwari ta duniya da Gwamnatin Jihar ta gina bayan rikicin kabilanci a Kasuwar Sasa da aka yi kusan shekara uku da suka gabata.

Bayan gwamnatin jihar ta tashi waxannan wurare hudu daga cikin gari zuwa wannan wuri, dubban ’yan Arewa maza da mata sun tare a garin na Akinyele inda suka gina gidajen zama da shiga cikin wadannan manyan kasuwanni domin gudanar da harkokinsu.

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna