Takaddamar nada Mukaddashin Gwamnan Neja ta dauki sabon salo

Hujjar da Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya bayar cewa Mataimakinsa Alhaji Ahmad Musa Ibeto ba ya gari, shi ya sa ya mika wa Shugaban Majalisar Barista Adamu Usman ragamar mulki ba ta gamsar da dama daga cikin ’yan majalisar ba, inda wasu suka nuna cewa ba su samu wasikar da Mataimakin Gwamnan […]

Takaddamar nada Mukaddashin Gwamnan Neja ta dauki sabon salo
Takaddamar nada Mukaddashin Gwamnan Neja ta dauki sabon salo

Hujjar da Gwamnan Jihar Neja Dokta Mu’azu Babangida Aliyu ya bayar cewa Mataimakinsa Alhaji Ahmad Musa Ibeto ba ya gari, shi ya sa ya mika wa Shugaban Majalisar Barista Adamu Usman ragamar mulki ba ta gamsar da dama daga cikin ’yan majalisar ba, inda wasu suka nuna cewa ba su samu wasikar da Mataimakin Gwamnan ya rubuta wa Gwamnan cewa ba ya gari ba, da kuma amsar da Gwamnan ya ba shi. 

Wasu daga cikin ’yan majalisar sun nuna mamakin yadda Gwamnan ya tsallake tanadin da aka yi a tsarin mulki da ya bayar da damar mika wa Mataimakin Gwamna ragamar mulki a duk lokacin da Gwamna ba ya gari ko kasa don kar a samu gibi wurin gudanar da harkokin mulki.
Binciken da wakilinmu ya gudanar, ya gano cewa tun cikin watan Disamba ne Mataimakin Gwamna Alhaji Ahmad Musa Ibeto ya rubuta wa Gwamna Mu’azu Babangida Aliyu wasikar neman izinin zuwa hutu a biranen Dubai da Landan sannan ya karasa Saudiyya domin yin Umara, sai dai Gwamnan bai ba shi amsa ba. Ganin haka ne, ya sake rubuta wata wasikar cikin watan Janairun da ya gabata, ita ma bai samu amsa ba, al’amarin da ya sa ya hakura da batun baki daya.
Alhaji Musa Ibeto dai ya nuna mamaki da ya ji a kafofin labarai cewa Gwamnan ya mika wa Shugaban Majalisar ragamar mulkin jihar ne, saboda ya je hutu kuma ba ya kasar. Ya ce lamarin ya saba wa tsarin mulki, domin yana nan bai je kasar waje ba, saboda bai samu amsar wasikarsa ga Gwamnan ba.
Ya rarrashi magoya bayansa su kasance a kowane lokaci masu bin doka don wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya yaba musu kan yadda suka ci gaba da nuna masa kauna, kuma ya kara samun magoya bayan daga kananan hukumomin jihar daga lokacin da ya fice daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.
Kakakin Gwamnan Jihar, Mista Isreal Ebije Ayegba a wata takardar da ya sa wa hannu ya ce matakin da Gwamnan ya dauka ya yi daidai, saboda Dokta Mu’azu Babangida Aliyu mutum ne wanda yake martaba dokoki, kuma ko kadan ba zai yi abin da zai tayar da husuma ta kowace fuska ba.
Shi kuwa Kakakin Jam’iyyar APC a Jihar Neja Mista Jonathan batsa ya kwatanta matakin da Gwamna Babangida Aliyu ya dauka da yi wa dimokuradiyya karan-tsaye, duk da cewa ya sha ikirarin cewa zai ba Mataimakinsa duk hakkokinsa, sai ga shi bai dade da yin wannan maganar ba ya yi amai ya lashe.
Ya ce me ya sa Gwamnan bai dauki irin wannan mataki a kan ’yan Jam’iyyar APC da suka koma PDP ba, sai wadanda suka bar PDP suka koma APC ake yi musu bi-ta-da-kulli?