Takaddamar Sanata Misau da Shugaban ’Yan sanda ta dauki sabon salo
Takaddamar da ke tsakanin Sanatan Bauchi ta Tsakiya Sanata Isa Hamma Misau da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ta dauki sabon salo bayan da Sanata Misau ya zargi shugaban ’yan sanda da yin lalata da wadansu ’yan sanda mata biyu wadanda ya yi musu karin girma a karkashin karin girma na musamman. […]

Takaddamar da ke tsakanin Sanatan Bauchi ta Tsakiya Sanata Isa Hamma Misau da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris ta dauki sabon salo bayan da Sanata Misau ya zargi shugaban ’yan sanda da yin lalata da wadansu ’yan sanda mata biyu wadanda ya yi musu karin girma a karkashin karin girma na musamman.
Sanata Hamma Misau da shugaban ’yan sandan sun sa zare ne bayan da sanatan ya zargi Ibrahim Idris da almundahana da aikata ba daidai ba a watannin baya, inda ya ce, rundunar ’yan sandan tana samun Naira biliyan 120 duk shekara daga kamfanoni da manyan mutane kan tsaron da take ba su, amma ba ta bayani kan yadda ta kashe su. Shugaban ’Yan sandan ya musanta zargin tare da bayyana Sanata Misau da gudajjen dan sanda.
Sai dai a zaman Majalisar Dattawa na shekaranjiya Laraba, Sanata Misau y ace lamarin shugaban ’yan sandan ya kazance, inda ya zarge shi da yi wa wata ’yar sanda ciki, inda a karshe ya aure ta da cikin wata hudu a garin Kaduna.
“A watan jiya Sufeto Janar din ya auri waccan matar kuma a dokar aikin dan sanda ba za ka auri matar da take aikin dan sanda ba, sai dai in ta yi ritaya. Sai ya yi sauri ya aure ta a asirce a Kaduna saboda matar tana da cikin wata hudu. Ina fadin wannan ne saboda rundunar, domin muna da jami’ai masu kwazo da dama da aka karya wa gwiwa, yanzu mun shiga tsaka mai wuya saboda Sufeto Janar din,” inji Misau.
Sai ya bukaci majalisar ta kafa wani kwamiti da zai binciki zarge-zargen da ya yi, inda ya yi alkawarin gabatar da takardu da bayanai ta yadda ’yan Najeriya za su san abin da yake faruwa.
kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin Kakakin ’Yan sandan Najeriya, CSP Jimoh Moshood kan sabon zargin ya ci tura. Saboda layin wayarsa ba ya tafiya har zuwa hada wannan rahoto.
Sai dai iyalan Asta sun shaida wa Aminiya cewa za su gurfanar da Sanata Misau kan bata musu suna.
Wanda ya yi magana a madadin iyalan, Nasiru Baba Saleh ya ce sun kadu da zargin na Sanata Misau, wanda ya bayyana da yi wa ’yarsu karya. “Muna da dukan shaidu cewa ba a boye aka daura auren ba. A Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna aka daura kuma mutane da dama sun halarta. Wakilan bangarorin biyu sun halarta. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna da Mataimakinsa da sauransu duk sun je. Don haka ba za mu dauki batun da wasa ba. wannan bata suna ne kuma ba za mu bari ya tafi a banza ba. Za mu kai shi kotu kan bata suna,” inji shi.