Takaddamar tsige Gwamnan Adamawa: Nyako ya ki amincewa da sharadin Jonathan

Yunkurin ceto kujerar Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Hamanyero Nyako ya samu cikas bayan da Gwamna Nyako ya ki amincewa da sharadin da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gindaya masa.Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa, Shugaba Jonathan ya amince ya dakatar da yunkurin tsige Nyako da ’yan Majalisar Adamawa da dukkansu ’yan […]

Takaddamar tsige Gwamnan Adamawa: Nyako ya ki amincewa da sharadin Jonathan
Takaddamar tsige Gwamnan Adamawa: Nyako ya ki amincewa da sharadin Jonathan

Yunkurin ceto kujerar Gwamnan Jihar Adamawa Admiral Murtala Hamanyero Nyako ya samu cikas bayan da Gwamna Nyako ya ki amincewa da sharadin da Shugaban kasa Goodluck Jonathan ya gindaya masa.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa, Shugaba Jonathan ya amince ya dakatar da yunkurin tsige Nyako da ’yan Majalisar Adamawa da dukkansu ’yan PDP ne suka shirya bisa sharadin Gwamna Nyako zai janye takardar da ya aike wa gwamnonin jihohin Arewa 19 inda a ciki ya zargi fadar Shugaban kasa da hadin baki kan kashe-kashen da ke aukuwa a Arewa.
Sai dai majiyar ta ce, Gwamna Nyako wanda ya koma Jam’iyyar APC mai adawa, ya fi amincewa ya rasa kujerarsa ta Gwamna da ya amince da sharadin Shugaban kasar bisa dalilin babu abin da ya hada takardarsa da batun tsige shi. Ya tsaya kai da fata cewa, gazawar Shugaban kasar ya dakatar da masu yunkurin tsige shi da suka hada da magoya bayansa da abokansa na nuna cewa ya amince da karya doka.
An shirya ci gaba da ganawa kan lamarin a ranar Talata da rana inda aka sa ran samun matsaya.
Masu ruwa da tsaki a Jam’iyyar PDP a Jihar Adamawa da suka hada da ministoci biyu na Harkokin Matasa Boni Haruna da na Harkokin Mata Zainab Maina a bayan nan sun nuna goyon baya ga yunkurin ’yan majalisar jihar na tsige Gwamnan da suke zargi da yin almundahana.
Sai dai Nyako da jam’iyyarsa ta APC sun zargi PDP da amfani da “muguwar hanya” don gaggauta cire shi a wata bayyananniyar hanya da ta saba wa doka tare da raina umarnin kotu.
Gwamna Nyako, ya gana da tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida a Minna a ranar Litinin kafin ya zarce zuwa Abuja a ranar don ganawa da Jonathan, sai dai ya ki cewa uffan duk da tambayoyin da aka rika yi masa kan batun.
Bayanai na baya-bayan nan sun ce Gwaman Nyako ya yanke shawarar ci gaba da fafatawa don kare kujerarsa bayan da wasu kungiyoyin jama’a da mukarrabansa suka tashi haikan wajen kubutar da kujerarsa.
 A ranar Litinin ne Gwamna Nyako ya shaida wa daya daga cikin mukarrabansa cewa zai gwammace ya  sauka maimakon a tsige shi, sai dai jaridar Premium Times ta ce, Majalisar Sarakunan Jihar ta gana a fadar Lamidon Adamawa a ranar Talata don daukar matakan sanya ’yan majalisar su janye tuhume-tuhumen da suke yi wa Gwamnan da Mataimakinsa.
Nyako ya so yin murabus ne don tilasta shugaban majalisar ya rasa tasa kujerar saboda sun fito daga mazaba daya da Mataimakin Gwamna Bala Ngalari, wanda dan Jam’iyyar PDP ne kuma ake jin kwamitin da aka kafa zai wanke shi daga zarge-zargen da ake yi masa.
Kakakin Gwamna Nyako Ahmad Sajo ya shaida wa Aminiya a Yola, cewa a shirye Gwamnan yake ya sauka daga mukaminsa idan yunkurin tsige shi ya ci gaba da keta tsarin mulki da ka iya jefa jihar a cikin tashin hankali.
Ya nuna shakku cewa zai yi wuya kwamitin binciken ya yi adalci ganin yadda aka kafa shi a bisa haramtacciyar hanya, sai dai ya ce Nyako zai kalubalanci lamarin a gaban kotu.
An samu zarge-zargen da ke cewa sojoji ne suka tilasta Mukaddashin Babban Jojin Jihar Mai shari’a Ambrose Mammadi ya kafa kwamitin binciken.
Kwamitin ya fara zama a ranar Talata a dakin taro na Dandalin Ribadu bayan an hana shi zama a otel din J&J Holiday billa saboda dalilai na tsaro da kasuwanci, inda mahukuntan otel din suka yi kuka mamayar da sojoji da sauran jami’an tsaro suka yi wa otel din ya hana abokan cinikinsu da dama hulda da su. Kwamitin ya tunkari Cibiyar ’Yan jarida ta Jihar da Ofishin kungiyar kwadago, amma suka ki amincewa
inda suka ce sun zabi su ci gaba da kasancewa ’yan ba ruwanmu kan takaddamar.