Takaici: Yadda Ybonne Nelson ta roki Iyanya ya aure ta
Ko ba a fada ba, a wannan lokacin, likkafar mawakin zamani, dan Najeriya, Iyanya ta yi gaba; kamar kuma yadda tauraruwarsa ke kara haskakawa.A kwanakin baya ne gaskiyar batun nan ya tabbata, inda wata ’yar fim a Ghana, Ybeonne Nelson, aka ce ta durkusa ta roki mawakin da cewa don Allah ya aure ta, saboda […]

Ko ba a fada ba, a wannan lokacin, likkafar mawakin zamani, dan Najeriya, Iyanya ta yi gaba; kamar kuma yadda tauraruwarsa ke kara haskakawa.
A kwanakin baya ne gaskiyar batun nan ya tabbata, inda wata ’yar fim a Ghana, Ybeonne Nelson, aka ce ta durkusa ta roki mawakin da cewa don Allah ya aure ta, saboda kaunarsa da take yi. Kamar yadda binciken Aminiya ya tabbatar, an ce mawaki Iyanya ya yi soyayya da ita; inda daga bisani ta neme shi da maganar aure, shi kuma ya juya baya, ya ce ba zai aure ta ba.
“Ybonne ta bukaci Iyanya da ya fara shirye-shiryen aurenta. Asali ma na yi magana da wani na kusa da mawakin, wanda ya gaya mini cewa ’yar fim din ta gaya wa Iyanya karara cewa ita fa babu abin da take bukata da shi sai aure, amma da ya nuna mata haka ba za ta yiwu ba, sai hankalinta ya tashi, ta gigice.” Inji majiyarmu.
A lokacin da ta shaida masa bukatarta, shi kuwa sai ya ce mata lokacin da zai yi aure bai yi ba. A kan haka ne sai ta duka kasa har gwiwa, ta ce masa: “Ina son ka, ina kaunarka har abada.”
Majiyar ta mu ta kara bayyana irin yadda ’yar fim din ta ji haushi, musamman saboda wannan abu mai kama da wulakanci da mawaki Iyanya ya yi mata. “Ni kuwa na fahimta da takaicin da ta shiga. Dama haka al’amarin soyayya yake, idan yarinya ta ce tana son mutum kuma har ta fara maganar aure amma mutumin ya ce a’a, lallai ba za ta ji dadi ba. Wannan al’amari yana nuna yadda Iyanya ya shahara, wanda ina ganin abin da ya sanya mata ke rububi, suna son ya aure su.” Inji majiyarmu.
Iyanya dai shi ne dan wasa na biyu daga Najeriya da ya wulakanta ’yar wasa daga kasar Ghana. Kwanakin baya ma, an samu rahoton da ya nuna yadda dan fim Jim Iyke ya wulakanta Nadia Buari, wacce fitacciyar ’yar fim ce a kasar Ghan.