Takaitaccen bayani a kan littafin ’Yantarun Nana Asma’u danfodiyo

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, Mai kowa, Mai komai, Wanda Ya bai wa Dokta Sa’adiya Omar damar yin bincike a kan wadansu gungu na mata masu taruwa su je wurin Nana Asma’u, diyar Mujaddadi Shehu Usmanu domin neman karuwa da ilimin da Allah Ya arzuta ta da shi. Tsira da amincin Allah kuma […]

Takaitaccen bayani a kan littafin ’Yantarun Nana Asma’u danfodiyo
Takaitaccen bayani a kan littafin ’Yantarun Nana Asma’u danfodiyo

Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, Mai kowa, Mai komai, Wanda Ya bai wa Dokta Sa’adiya Omar damar yin bincike a kan wadansu gungu na mata masu taruwa su je wurin Nana Asma’u, diyar Mujaddadi Shehu Usmanu domin neman karuwa da ilimin da Allah Ya arzuta ta da shi. Tsira da amincin Allah kuma su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu tare da mutanen gidansa da sahabbansa.
Wannan littafi mai yawan shafi 115, wanda kuma kamfanin buge-buge na Print IkRA na Gusau ya buga shi, ya kunshi babi guda uku. Babi na daya an wallafa shi ne a kan ‘Yantaru: Samuwarsu da Tsarin Ayyukansu. A nan, mawallafiyar ta yi bayanin cewa, ‘‘Yantaru na nufin taro-taro na jama’a’ kuma sunan ya samo asali daga daya daga cikin wakokin Shehu Usmanu na Fulatanci, inda ya yi amfani da kalmar ‘taroje’ wato cincirindon taron jama’a yana kiransu ya zuwa hasken babban rabo. Haka kuma mawallafiyar ta yi bayani cewa a wajen shekarar Miladiyya ta 1840 ne Nana Asma’u, wacce babbar malama ce da ta yi fice a fannonin Alkur’ani da Fikihu da Hadisi da Tauhidi da harshen Larabci da fannoninsa; ta ‘yi hobbasa wajen kokarin fitar da wani tsari na ilimantar da mata’ wanda shi ne ya zo ya zama tsarin ‘Yantaru. A wannan tsarin ne gungu-gungu na matan aure da zawarawa sukan niko gari daga sauran garururwa kamar su Kware da Goronyo da Wurno da Kabi da Gumi su zo har Sakkwato ko Wurno duk inda take domin daukar karatu. Haka kuma mawallafiyar ta yi bayanin tsarin shugabancinsu wanda ya nuna su da kansu suke zaben shugabanninsu sa’annnan su nemi tabarrukin Uban Garinsu da kuma ita Nana Asma’u ko magadanta. A cikin shugabannin akwai Jaji da Waziri da Majidadi da Imamu da Zakara da Beru da sauransu.
Babi na biyu ya kunshi bayani ne a kan sakonnin da wakokin ’yantaru suke dauke da su. Bayanin ya nuna cewa mafi yawan wakokin bege ne ga Annabin Tsira da wasu Sahabbai da kuma Shehu Usman da sauran malaman Jihadi.
Babi na uku ya kunshi wakokin ’yantaru na wannan karni da aka taskace aka kuma kaddamar da su.
A yanzu haka ’yantarun suna nan suna ci gaba da harkokinsu amma a yanzu sun fi ba da karfi a kan hidimar masallatai da jinyar marasa lafiya da wankan gawa da sauran hidimomim da ba na ilmi ba ne kai tsaye.
Darrusan Da Ya Kamata Mu Koya Daga Harkar ’Yantaru: Babban darasi da ya kamata mu dauka daga harkar ’yantaru shi ne yadda Mujaddadi Shehu Usmanu da diyarsa Nana Asma’u da sauran malaman Jihadi suka bai wa ilmin mata da ilimantar da mata muhimmanci. Tarihi ya zo da bayanin cewa shi kansa Shehu Usmanu yana koyar da mata a makarantarsa kuma sai aka sami wasu magauta suka kai masa suka saboda wai ya hada maza da mata a wuri daya. Shehu Usmanu ya yi amfani da ka’idar nan ta addinin Musulunci wadda malamai suka fi sani da ‘akhafud dhararaini.’ Watau in abubuwa biyu marasa kyau suka fuskance ka, kuma ya zama dole sai ka zabi daya, to sai ka dauki mafi kankantarsu wajen cutarwa. Sai ka yi shi domin ka guji mafi girma wajen cutarwa. A nan ya nuna wa magautansa cewa barin matan cikin duhun jahilci ya fi muni fiye da hada su da maza wajen ilmantar da su.
Darasi na biyu shi ne irin sadaukarwar da ita Nana Asma’u ta yi wajen kula da ilimantar da wadannan mata, da kuma irin yadda sauran ’yan uwanta mata ’ya’yan Shehu Usmanu da kuma diyarta da jikokinta suka ci gaba da wannan hidima har zuwa yau.
Darasi na uku shi ne yadda su kansu ’yantarun suke niko gari su yi takanas ta Sakkwato domin su kawo ziyarar daukar karatu da ziyarce-ziyarce da sauran hidimomin addini ba tare da sun dora wani nauyin bakuncinsu na lokaci mai tsawo ba. Bayani ya zo a cikin wannan littafi cewa ranar da suka iso Sakkwato ne kawai ake tarbar su da dafaffen abinci wanda ita Nana Asma’u ko magadanta suke shiryawa.  Sauran kwanakin da za su yi, sukan zo da kayan abincinsu ne su yi wa kansu girki, su ciyar da kansu. Wannan ya nuna dogaro da kai da kare mutunci sabanin abubuwan da muke gani a yau inda mutane suke shantakewa, su saki nauyinsu rugujub a kan gwamnati.
Shawarwarin matakan da ya kamata al’ummar Musulmi ta dauka don daraja Nana Asma’u da harkar ’yantaru: Ina ganin ba abin da za mu yi mu nuna godiya da matukar jin dadin kokarin da Nana Asma’u da su ’yantarunta suka nuna wajen habaka ilimin mata illa mu hadu mu kafa Jami’ar Mata Mai Zaman Kanta a Sakkwato ko a Wurno wadda za a lakaba wa suna kamar haka: Jami’ar Mata Ta Nana Asma’u danfodiyo. Wannan jami’a bai kamata Gwamnatin Jiha ko ta Tarayya ta kafa ta ba. Mu al’ummar Musulmi ya kamata mu bude asusun kafa ta. Idan muka tara Naira biliyan goma kacal sun isa a yi gine-ginen kafa ta da sayen kayan aikin da za a fara karatu da su. Gwamnatin Jihar Sakkwato sai ta taimake mu da sadakar fili mai girman hekta 100 wanda shi ne zai cika sharuddan Hukumar Kula Da Jami’o’i ta kasa (NUC). Ina rokon Mai Martaba Sarkin Musulmi da ya ba da umurnin kafa Kwamitin Tsara Jami’ar Nana Asma’u ta Mata domin a fara aiki nan take.
Ina kuma kira ga manyan masu kudi cikinmu da kuma kananan masu kudinmu da su dauki wannan muhimmin al’amari da gaske, domin mu cin ma nasara da gaggawa. Allah Ya sa mu dace, Ya kuma ba mu ikon fadi da cikawa tare da ladar kyakkyawar niyya.
Allah Ya saka wa Dokta Sa’adiya Omar saboda zuzzurfan binciken da ta yi wajen wallafa wannan littafi da sauran littattafan da ake kaddamarwa a yau. Allah Ya kara mata kuzari da hazaka da lafiya, Ya kuma ja kwananta domin ta ci gaba da zama fitila mai haskaka wa sauran matan al’ummarmu hanyar ilmi.
Farfesa Munzali ya gabatar da wannan jawabi ne a ranar 19-4-2014 a Sakkwato, yayin kaddamar da littafin.

Kamfanonin waya na shirin ƙara kuɗin kira da na data a 2025

Mutum 5 da suka yi tashe a shafukan sada zumunta a 2024

NAJERIYA A YAU: Abin da ya sa ake bikin ‘Boxing Day’ a ranar 26 ga Disamba

Ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a gidan mutuwa a Borno