Takaitaccen bayani kan darare goma da layya

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu.  Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu, (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi sawunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  Bayan haka, yau insha Allah, tsokaci […]

Takaitaccen bayani kan darare goma da layya
Takaitaccen bayani kan darare goma da layya

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu.  Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammadu, (Sallallahu Alaihi Wasallam), tare da alayensa da sahabbansa, sannan da duk wadanda suka bi sawunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  
Bayan haka, yau insha Allah, tsokaci zai gudana a takaice ne kan rantsuwar da Allah Ya yi da Darare Goma da kuma wani abu na sha’anin layya. Ina fata Allah Ya sa ya yi amfani.
Tasirin yin azumi da yawaita kyawawan ayyukan ibada a wadannan kwanuka goma yana da yawa matuka.
Wadannan kwanuka goma su ne wadanda Allah Ya yi rantsuwa da su, inda Ya ce, “Ina rantsuwa da Alfijir da kuma Darare Goma… Ko a cikin wadannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi)?”   (Suratul Fajri).
Malamai sun ce ana dubi ne da abin da Allah Ya yi rantsuwa da shi, a yi kokarin rorar amfani da tasirin da ke cikin abin da aka yi rantsuwar a kansa.
Abdullahi dan Abbas, (Allah Ya yarda da su), ya ce Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Babu wasu kwanuka da aikin alheri ya fi soyuwa a cikinsu, kamar wadannan kwanuka (yana nufin kwanukan goman farko na watan Zul-Hajji).”  Sai (sahabbai) suka ce, “Ya Manzon Allah, ko da jihadi don daukaka Kalmar Allah?” Ya ce, “Ko da jihadi cikin daukaka Kalmar Allah. Sai dai (a ce misali) in mutum ya fita da ransa da dukiyarsa, kuma ya kasance bai dawo da komai daga ciki ba, (wato ya yi shahada kuma dukiya ta kare).”  Buhari ne ya ruwaito Hadisin.
Yin azumi yana daga cikin mafiya girman ayyukan alheri, domin ba a san iyakar ladarsa ba.  Allah Ya kebance wa kanSa shi, kamar yadda Buhari da Muslim suka ruwaito daga Hadisin Abu Huraira, (Allah Ya yarda da shi), daga Ma’aikin Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), inda Allah Ya ce, “…saboda shi (azumi) Nawa ne, Ni ne Zan yi sakamako a kansa….”   Dpn haka akwai bukata in mai karatu matukar yana iyawa, ya yi azumi a cikin wadannan kwanuka.  
Abu Sa’idul Khudriy, (Allah Ya yarda da shi), ya ce, Manzon Allah, (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Babu wani daga cikin bayin Allah da zai azumci wata rana saboda Allah kawai, face Allah Ya nisantar da fuskarsa daga wuta, nisan kharifa saba’in.”  Buhari da Muslim suka ruwaito wannan Hadisi.  Abin da ake ce wa kharifa, kamar yadda aka bayar da ma’anarsa, shi ne tsawon tafiyar mil guda.
Da yake azumtar wadannan kwanuka, mustahabbi ne ba dole ba, wanda ba zai iya yin su duka ba, to, ya dage ya azumci Ranar Arfa, wato ranar 9 ga watan Zul-Hajji, saboda falalarsa. Ma’aiki, (Sallallahu Alaihi Wasallam), lokacin da aka tambaye shi game da azumtar ranar Arafa ya ce, “Yana kankare (zunuban) shekarar da ta wuce da na wacce ake ciki.” Imam Buhari ya ruwaito shi.
Layya :
Layya tana cikin mafiya girman ayyuka kyawawa a cikin wannan wata na Zul-Hajji, kuma sunna ce mai karfi a Musulunci. Ma’aiki (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Babu wani aiki daga cikin ayyukan alheri da dan Adam (Musulmi) zai aikata a Ranar Sallah, wanda ya fi soyuwa a wajen Allah, kamar zubar da jini (yin layya), ku dadada zukata da shi.” Imamu Tirmiziy da Ibnu Majah da Hakim suka fitar da Hadisin daga A’isha, (Allah Ya yarda da ita).
Allah Ya ce, “Kuma ka (tsayar da) Sallah saboda Ubangijinka, kuma ka yi suka (wato Layya da Hadaya.” Surar Alkausar aya ta 2.  
Anas dan Malik (Allah Ya yarda da shi) ya ce, “Ma’aiki (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya kasance yana Layya da rago biyu kosassu, masu maiko, masu (manyan) kahonni.  Sai ya yi basmala (Bismillahi), ya yi kabbara (Allahu Akbar), ya dora kafarsa a gefen wuyan (abin yanka) ya yanka.  Ya yi yankan da kansa.” Buhari da Muslim suka ruwaito shi.
Abu Huraira (Allah Ya yarda da shi), ya ce Ma’aiki (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Wanda duk yake da wadata kuma bai yi Layya ba, to kada ya kusanci masallacinmu (wato ya yi zamansa a gida kawai).”  Imam Ahmad da Ibnu Majah suka ruwaito shi.  Imam Hakim ya inganta shi. Wasunsu, masu fitar da Hadisi sun rinjayar da wakafin (tsayar da) Hadisin ga Abu Huraira.  Wadanda suka danganta Hadisin ga Annabi (Sallallaahu Alaihi Wasallam) tabbatattu ne (wato Sikkat), a fagen amincinsu kan haka.  
Imam Daru kudniy da Hakim sun fitar da Hadisi daga Abdullahi dan Abbas, (Allah Ya yarda da shi), cewa Ma’aiki (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce, “Abu uku, a kaina farilla amma a kanku tadawwa’i:  Suka (Layya), Wutiri da Raka’o’in Alfijir.”
Wannan ya nuna karfin Sunnar lLayya. Hasali ma Imam Abu Haniyfa yana ganin wajiba ce; tare da wani zance da aka ruwaito daga Imam Malik. Sai dai jamhurun malamai da suka hada da Imam Shafi’i da Ahmad, sun tafi a kan cewa Sunna ce mai karfi.
Nau’in dabbobin Layya:
Ana farawa da rago lafiyayye; sannan tunkiya; sai bunsuru lafiyayye; sai akuya; sai sa da saniya; sai rakumi da taguwa. Amma a hadaya a Makka, ana farawa daga rakumi zuwa akuya.  Al’ada ce a ki ko a ji kunyar yin Layya da bunsuru ko akuya.
A’isha (Allah Ya yarda da ita), ta ce, “Ma’aiki (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya umurci a kawo rago mai kahonni, wanda ya taka baki (a kafafunsa); ya kwanta a kan baki (a cikinsa); kuma ya yi dubi a cikin baki (a idanunsa), sai aka zo da shi (don yin Layya), sai ya ce, “Ya A’isha! Kawo min wuka, ki wasa ta da dutse.”  Sai na aikata haka (inji A’isha), sai ya karba ya kama ragon ya kwantar da shi sannan ya yanka, bayan ya ambaci sunan Allah, ya yi addu’a:  “Ya Allah, Ka karba daga Muhammad da alayen Muhammad da kuma al’ummar Muhammad.”  Imam Muslim ne ya ruwaito shi.  A wata ruwayar kuma ya ce, “Bismillahi wallaahu akbar.”