Takaitaccen bayani kan layya da Sallar Idi da abin da ya sadu da su (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu.  Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammad (SallAllahu Alaihi Wasallam) da alayensa da sahabbansa da duk wadanda suka bi sawunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  Bayan haka, a makon jiya mun yi tsokaci […]

Takaitaccen bayani kan layya da Sallar Idi da abin da ya sadu da su (2)
Takaitaccen bayani kan layya da Sallar Idi da abin da ya sadu da su (2)

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai.  Dukkan yabo da godiya na Allah ne, Ubagijin halittu.  Tsira da amincin Allah su kara tabbata ga mafificin halittu, Annabi Muhammad (SallAllahu Alaihi Wasallam) da alayensa da sahabbansa da duk wadanda suka bi sawunsu cikin kyautatawa har zuwa Ranar karshe.  
Bayan haka, a makon jiya mun yi tsokaci kan nau’o’in dabbobin layya, inda aka kawo nau’in ragon da Ma’aiki (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya yanka, wanda A’isha, (Allah Ya yarda da ita) ta bayyana, kuma shi ne mafi darajar raguna, wato mai manyan kahonni, mai baki a kafafu da ciki da idanu.  Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya yanka abinsa da kansa, saboda haka yana da kyau duk wanda zai yi layya, to ya yi kokari ya yanka da kansa.
Yana da muhimmanci a kara nanata cewa batacciyar al’ada ce a ki ko a ji kunyar yin layya da bunsuru ko akuya, alhali a tsari na dabbobin layya, su ne na biyu a muhimmanci, kamar dai yadda malamai suka yi bayani.
Lallai ne dabbar da za a yi amfani da ita wajen layya ta kasance lafiyayya, wadda ba ta da kowace bayyananniyar nakasa wadda za a kushe dabbar da ita. Kodayake Ma’aiki (SallAllahu Alaihi Wasallam) ya fadi aibi hudu ne a fili, amma jamhurun (mafi rijayen) malamai, sun tafi a kan ana iya kiyasin wadansu aibobi dangane da rashin lafiya da makamantanta.
Barra’u dan Azib (Allah Ya yarda da shi), ya ce, Ma’aiki (SallAllahu Alaihi Wasallam) ya mike cikinmu ya ce, “Hudu (halaye da kamanni a cikin dabbar layya) ba su ingantar da layya: makanta (koda ta gefe daya ce); rashin lafiya (bayyananne); gurgunta (bayyananniya mai hana tafiya); tsufa (wadda ta tsotse ba maiko da bargo a jikinta).”  Imam Ahmad da wasu hudu (As’habus Sunan) suka ruwaito shi.  Imam Tirmiziy da Ibnu Hibban da Hakim sun inganta shi.
Ana yanka rago dan wata takwas lafiyayye, kosasshe, amma wanda ya shekara ya fi.  Tunkiya, bunsuru da akuya, dole sai sun cika shekara guda cif da abin da ya wuce haka.  Shanu kuwa sai sun kai shekara biyu akalla.  Rakuma sai sun kai akalla shekara biyar.  Duk ana yanka su ne bayan an kare Sallar Idi.  Wuraren da ba su Sallar Idi wato mazauna daji, sai su yi hasashen lokacin kammalawa a birane, sannan su yanka.
Ana nanata cewa ya fi kyau mutum ya yanka layyarsa da kansa, domin Ma’aiki (SallAllahu Alaihi Wasallam) ya yi da kansa ne.
Ana son mutum ya fara ci daga naman layyarsa bayan ya dawo daga sallar Idi, kuma ya yi yankan. An fi so ya raba naman layya gida uku: ya ci; ya sadakar; kuma ya yi kyauta ga masu ziyararsa. Idan ya cinye duka shi da iyalinsa, daidai ne. Idan ya sadakar duka daidai ne.  Allah Shi ne Mafi sani.
Da yake yau rana ce ta 9 ga watan Zul-Hajji, wato Ranar Arafa, abu ne mai kyau koda mutum bai dauki azumi ba, saboda mantuwa ko gazawa, ya yawaita zikiri (ambaton Allah) fiye da kwanukan da suka gabata.  Ma’aikin Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam), ya ce, “Mafi falalar addu’a, ita ce wadda aka yi ta Ranar Arafa.  Kuma mafi falalar abin da na fadi, ni da sauran Annabawa gabanina, shi ne ‘La’ilaha illallahu wahdahu lashariikalahu.” Kamar yadda aka fitar a littafin Muwadda Malik, inji Imamu Nawawiy a littafinsa Al’azkar.

Sallar Idi da abin da ya rataya da ita         
 Idan Allah Ya kai mu gobe Asabar, wato Ranar Sallar Layya ke nan, ana son mutum ya yi wanka, ya sanya tufa sabuwa in da hali ko kuma wankakkiya mai kyau, mai tsabta. Ya sa turare, in ya samu. Ya fita zuwa filin Idi, in babu ruwa ko abin da ke hana a fita, alhali yana kabbarori har zuwa filin Idin. Idan ya isa sai ya zauna ya jira zuwan liman. Ba zai yi nafila ba,  zai yi ta fadin dayan biyun kabbarori ko ya rika musanyawa, lokaci bayan lokaci. Yana cewa: Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!! Ko kuma Allahu Akbar! Allahu Akbar!! La’ilaha illallah!!! Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Walillahil hamd!!!  Haka zai yi ta yi, har liman ya zo a tayar da Sallah. Za a yi kabbarori bakwai har da ta harama don yin Sallar Idi, sai a karanta Fatiha da sura, a yi ruku’u da sujada biyu kamar kowace Sallah.  A raka’a ta biyu a yi kabbarori shida har da ta tashi, sannan a karanta Fatiha da sura a yi ruku’a da sujada biyu, sannan a zauna a yi tahiyya a yi sallama.  Shi ke nan an kammala Sallar Idi.  
Idan mutum ya samu Sallar tare da liman, to, yana da kyau kwarai ya zauna cikin natsuwa ya saurari hudubar liman, matukar ba wata lalura mai karfi da za ta hana shi yin hakan.
Bayan liman ya kare hudubarsa, sai ya tafi ya yanka layyarsa in yana da abin yankawa, sannan kowane mamu, in ya isa gidansa sai ya yanka tashi layyar. Sannan tunda ya kame bakinsa, sai ya jira a fede abin layyar, sannan ya ci daga cikinta.
Idan mutum bai samu damar yin layya a gobe Asabar ba, zai iya yi jibi Lahadi da kuma washegari Litinin, wadanda su ne ranakun da ake iya yin layyar a cikinsu.
Daga lokacin da aka kammala Sallar Idi, mutum zai rika yin kabbarorin da aka zayyana a sama, daga bayan Sallar Azahar ta Ranar Sallah har zuwa bayan Sallar Asubahin rana ta hudu (daga Ranar Sallah) wato ranar Talata ke nan. Zai rika yinsu ne sau daidai ba zai doge ba, kamar a filin Idi.
Abu ne mai kyau kuma daga bayan Idi din har zuwa lokacin da Allah Ya so, ana son a ziyarci ’yan uwa da abokan arziki a taya juna murna da fatar alheri. Saboda lokaci ne na murna da annashuwa.  
Muna rokon Allah Ya karba mana ibadunmu, Ya kawo mana zaman lafiya da aminci a kasarmu da duniya baki daya, amin. A yi Sallar Idi da Layya lafiya!
Wassalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh!