Takaitaccen Sharhi
Wannan wake mai baitoci 31, an rubuta shi ne da nufin gabatar da tarihin Dokta Bukar Usman a takaice, wanda a ranar 10 ga Disamban 2019 ya cika shekara 77 a duniya. Babban dalilin yin haka kuwa shi ne, saboda la’akari da yadda ya kasance mai amfanar al’umma a rayuwarsa. Dalili ke nan ma amshin […]
Wannan wake mai baitoci 31, an rubuta shi ne da nufin gabatar da tarihin Dokta Bukar Usman a takaice, wanda a ranar 10 ga Disamban 2019 ya cika shekara 77 a duniya.
Babban dalilin yin haka kuwa shi ne, saboda la’akari da yadda ya kasance mai amfanar al’umma a rayuwarsa. Dalili ke nan ma amshin waken ya kasance: ‘Dan Najeriya, mai kishin kasa, Bukar Yamtarawalar zamani.’ Wanda haka ke kara tabbatar mana da cewa lallai shi mai kishin kasa ne, musamman ta la’akari da yanayin rayuwarsa da ayyukansa.
Baitin farko ya bude ne da jinjina ga Allah (SWT), sannan kuma a baiti na biyu sai aka bijiro da yabo ga Manzon Allah (SAW). Wannan ke nuna godiya ga Allah da Ya samar mana da duk wata jagora kuma Ya ba mu ikon gabatar da kowane aiki a rayuwarmu.
Yamtarawala: Wadansu za su yi tambayar shin me wannan kalma ke nufi? To ba kalma ba ce, suna ne na wani jarumi kuma muzakkari, wanda ya bayyana a tarihin kasar Biu ta Jihar Borno (mahaifar Dokta Bukar Usman). Kamar yadda tarihi ya nuna, wannan mutum shi ne ya kafa kasar Biu kuma shi ne shugabanta na farko da ya ba ta kariya daga dukkan wasu hare-haren yaki a wancan zamani mai dadewa. Tarihin Yamtarawala ya yi kama da na Bayajidda, jarumin da ya bayyana a Daura ta Jihar Katsina.
Sauran baitoci sun bijiro da bayanai dalla-dalla na ranar haihuwar Dokta Bukar, wasu makarantun da ya yi, ayyukan da ya yi, sannan kuma aka zayyano yadda ya kasace marubuci, wanda ya wallafa littattafai da yawa a fannoni daban-daban na rayuwa. Haka kuma an bayyana yadda ya kafa Gidauniyar Bukar Usman, wacce ta ta’allaka wajen taimakon al’umma a fannoni daban-daban, musamman ma bunkasa ilimi a cikin al’umma.
Mu duba wannan baitin, wanda ke jaddada halayensa na taimakon al’umma: “Taimakon gajiyayyu Bukar ya saba, Tallafi na karatu ya ba da sawaba, Dan kwarai mai himma da zurfin tunani.”
Haka kuma, an zayyana sunayen mahaifansa da matansa na aure da kuma ’ya’yansa a cikin waken.
A takaice dai a wannan wake, an yi kokarin kwatanta jarumai biyu mabambanta. Yamtarawala – wanda ya yi zamani can a baya, shekaru masu yawa da suka shude, watau Yamtarawala na dauri. Sai kuma Dokta Bukar, wanda ya yi zamani a wannan lokaci, wanda shi ma yake yi wa al’ummarsa hidima – ya zama Yamtarawalar Zamani!