Takaitaccen tarihin birnin Garoua a Jamhuriyar Kamaru

Garoua shi ne birni inda aka haifi Shugaban kasar Kamaru na farko, Ahmadou Ahidjo. kabilun da suka fi yawaita a birnin su ne Fali, Fulani da kuma Hausawa. Ga duk wani wanda ya kai ziyara birnin Garoua yana iya ganin babban masallaci da aka gina a shekara ta 1982 a unguwar Poumpoumré. A shekarun baya […]

Takaitaccen tarihin birnin Garoua a Jamhuriyar Kamaru

Garoua shi ne birni inda aka haifi Shugaban kasar Kamaru na farko, Ahmadou Ahidjo. kabilun da suka fi yawaita a birnin su ne Fali, Fulani da kuma Hausawa. Ga duk wani wanda ya kai ziyara birnin Garoua yana iya ganin babban masallaci da aka gina a shekara ta 1982 a unguwar Poumpoumré. A shekarun baya kuma tallafin da Mulukiyyar Sa’udiyya ta bayar ya sa a dada gyara masallacin.
Har ya zuwa shekara ta 2011, ana iya ganin wata dorina da aka yi wa lakabi da suna ‘Afirika’ a cikin ruwan kogin
Benoué. Wannan dorinar da ubangidanta ya maida ta kamar dabbar gida, ya dinga fitar da ita daga cikin ruwa yana kewayawa da ita a cikin gari, sa’annan kuma daga bisani ya maida ta a cikin ruwa inda take kwana.
Hakan ya kai ga tarin masu yawon bude ido kamar Turawa da sauransu suna kai wa wannan dabbar ziyara suna kuma daukar hoto da ita.
Wani abin da zai sa jama’a su bukaci ziyartar birnin Garoua, shi ne filin jirgin sama na kasa da kasa, inda a wasu shekaru jiragen sama na kasashen ketare suka dinga sauka. Kodayake a yanzu kasar Kamaru na da karancin jiragen sama, hakan kuma ya makarar da zirga-zirgar da jama’a suke yi. Sai dai akwai kasuwar kayan sana’ar hannu na gargajiya da jama’a suke dinga ziyarta.
A shekara ta 1992 ne Magajin Garin Garoua na wancan lokacin, marigayi Ahmadou Hayatou (dan gidan sarauta) ya yi tunanin hada ’yan kasuwa masu sayar da kayayyakin da aka sarrafa su da hannu a wuri guda a maimakon yadda suke watse a cikin gari. A cikin wannan kasuwar sayar da kayan sana’ar hannu, ana iya samun takalma, tabarmai, kwanduna da kuma sutura, hadi da kayan gwala-gwalan mata da aka sarrafa da fatun dabbobi daban-daban, aka kera su. Daga cikin fatun dabbobin akwai na macizai, awaki da kuma tumaki.
A wata unguwar da ake kira Kilarou, ana iya samun makera na gargajiya, wadanda suke kera su awarwaro, su yarruka, duwatsun wuya, bokitai, akwatuna, gatari, fartanya da kuma zobuna.  Kodayake kuma a yanzu duk wasu harkokin da suka danganci gargajiya, jama’a na yin jifa da su, amma kuma akwai raguwar guggubin wadanda har a yanzu suke samun tafiyar da rayuwarsu karkashin wannan sana’a, abin da ’yan kasuwar masu sayar da wadannan kayayyakin suka saida mini ke nan. Suna cewa kayan kasuwarsu sun fi karbuwa idan suka tafi kasashen waje domin tallatawa, a manyan tarurruka da Turawa suke halarta. A nan ne suke haduwa da wadanda suka fi darajanta kayan kasuwarsu.
Wata matsalar da ’yan kasuwar suke fuskanta shi ne, kamar na samun damar saran itatuwa da za su sassake su sarrafa, domin su fitar da surar wata dabba ko kuma wani abu daban kamar kujera ko kuma kotar wuka. Hakan a dalilin cewa akwai haramci wurin sarar itatuwa a yankin Arewacin Kamaru. A dalilin zaizaiyar kasa da hakan ke yawan haifarwa. Saboda haka jami’an da suke kare muhalli na sa ido sosai wurin ladabtar da kuma hukunta duk wani wanda aka same shi da aikata laifi ga muhalli.
A garin Pitoa, mai nisan kilomita goma sha biyar daga birnin Garoua, akwai wata kasuwa da ake cinta a kowace ranar Lahadi. Wannan kasuwar kuma tamkar wata mahada ce ga dukkanin al’ummomin da suke zuwa daga kudancin kasa da kuma yankin Arewaci, har ma daga Najeriya, musamman ma Mubi da Yola mutane na zuwa da kayan kasuwarsu kamar su tasoshi da farantai da cokali da sauransu suna sayarwa a wannan kasuwar ta garin Pitoa.
Hari la yau kuma akwai tarin gidajen naman daji kamar na Benoué da Bouba Ndjidda da kuma na Faro, inda ake samun ganin dabbobi daban-daban kamar su zaki, giwaye, dorina, bauna,da ire-iren tsuntsaye. Ga kuma su tsaunuka masu aman wuta irin na Rhumsiki, mai nisan kilomita dari uku da arba’in daga Arewacin Garoua. A gidan ajiye namun daji na Bouba Ndjidda ne ma a bara, wasu maharba da ake kyautata zaton cewa sun fito daga kasashen Chadi ko kuma Sudan; suka dinga kai hari ga tarin giwayen da suke kunshe a wannan wurin, bisa ga dalilin cewa suna da bukatar samun haurensu su kai kasuwa domin sayarwa, saboda akwai bukatar hauren a wasu kasashe na yankin gabashin duniya. Lamarin da ya kai ga hukumomi tashi tsaye domin su shawo kan wannan al’amarin.