Takaitaccen tarihin Masarautar Bauchi (3)
A zamanin Yakubu ya yi yake-yake 43 kamar yadda na fadi a baya, wadanda ba za mu iya bayyana su a nan ba. Ya ci Misau ya kori Habe, shi da Malam dan Kawu na Malam Zaki. A cikin yake-yaken nan kuwa wasu masu ban tusayi ne, wasu kuma masu ban tsoro, wasu kuwa gwanayen […]
A zamanin Yakubu ya yi yake-yake 43 kamar yadda na fadi a baya, wadanda ba za mu iya bayyana su a nan ba. Ya ci Misau ya kori Habe, shi da Malam dan Kawu na Malam Zaki. A cikin yake-yaken nan kuwa wasu masu ban tusayi ne, wasu kuma masu ban tsoro, wasu kuwa gwanayen ban sha’awa da gaske.
Malam Yakubu ya fara jihadi ne a wani gari da ake kira Kanyallo, an ce akwai wani mutumin Kanyallo ne ke shiga masallacin Malam Yakubu a Inkil da Magariba in an yi ruku’u ya sare kan mutum daya cikin masallata. Da abin ya yi yawa, sai aka yi dabara aka kama shi. Malam Yakubu ya sa aka yanka shi da wukar da yake sare kan masallatan. Wannan wuka ce aka rike idan shari’a ta yanke hannun barawo ta samu da ita ake yi. (Ita ce wukar da Wambai ke bai wa kowane sabon Sarkin da aka nada a Bauchi).
Bayan yakin Kanyallo, Malam Yakubu ya yi yake-yaken da suka sa kasar Bauchi ta wajen Kudu ta dangana da Kwararrafa, ta Yamma har Lere, ta Gabas ya yi iyaka da dan uwansa Malam Buba Yero na Gombe, wanda a wajen rabon iyaka aka samu dan sabani amma daga baya aka daidaita.
A cikin yake-yaken da ya yi za a iya karkasa su kashi uku kamar haka:
1. Gudunmawa: Sarkin Musulmi ya taba umartar Malam Yakubu ya bar yakin Dass ya tafi ya tsare Shehu Laminu da ya nufo kasar Hausa da yaki. Malam Yakubu ya tafi ya hadu da Shehu Laminu a inda ya yi sansani a tsakanin Kyawa da Fake a kasar Kano (yanzu Jihar Jigawa). Wannan yaki muhimmi ne kuma mai tarihi. Kuma masu bayar da labari suna bayar da labarai mabambanta a kansa. A takaice an ce, a lokacin Sarkin Bauchi ya iso ya yi sansani, Shehun Borno ya tura wani Kachallansa ya dubo yawan jama’ar da Yakubu ya zo da su, domin an ce Shehun Borno ya zo da dawaki dubu 44 da 444. To da Kachallan ya zo da jama’arsa sai ya kewaye sansanin Sarkin Bauchi Yakubu, amma wannan bai razana jama’ar Bauchi ba, suka ci gaba da sha’aninsu a sansanin, suka ci kasuwa da sauran jama’a. Da Kachalla ya ga haka, sai ya koma ya bayyana wa Shehun Borno cewa mutanen kadan ne, amma a yadda ya gan su suna da karfin hali ba za su gudu ba koda za a kashe su duka.
A lokacin duka-duka dawakin Malam Yakubu 5000 ne, sai dai akwai maharba masu yawa. Da aka fara yaki kura ta murtuke ba a ganin abokan gaba, nan ne aka kashe Madakin Bauchi Hasan, wanda shi ne jagoran yakin Bauchi, har Barebari suka yanke kansa suka kai wa Shehun Borno a kan cewa kan Malam Yakubu ne. To amma a cikin jama’ar Shehun Borno akwai wanda ya san Malam Yakubu sosai, sai ya ce da Shehu wannan ba Malam Yakubu ba ne, wani hakiminsa ne, kuma idan Malam Yakubu ya ji an kashe wannan mutum, lallai za ka gan shi a nan gaba gare ka. Bai dade da fadin wannan magana ba, sai suka ji Malam Yakubu ya yi sallama a cikin tantin Shehun Borno. Nan aka ce Shehun Borno ya fice ta wata kofa (ya gudu) ya bar gadon da yake zaune a kai da tabarminsa da sauran kayayyakinsa.
2. Sarkin Musulmi ya taba umartar Malam Yakubu ya tafi Misau ya taimaki Sarkin Katagum, ya je ya samu an ci garin Misau an kone garin. Sai Haben suka mika wuya, inda daga baya bisa umarnin Sarkin Musulmi aka mika garin ga Malam Muhammadu Manga, bayan ya yi zaman shekara daya a garin Buri-Buri a kasar Bauchi da izinin Malam Yakubu.
Yake-yake don kafa daular Musulunci sun hada da:
(1). Yakin Kanyallo (wanda muka ambata a baya).
(2). Yaki Miri
(3). Yakin Gubi yakin da ya yi zafi domin an ce jarumai ne da suka sa Habe da yawa da suke kewayen Bauchi suka mika wuya.
(4). Yakin Buli da Falfelu da Baba da Gambiri da Lere da Ribina, wadda cin ta ya sa Jarawa duka suka bi. Sai yakin Zarandan Habe da na Kantana da na Angas da na Montal da na Mada da na Kwararrafa (wato Wukari).
Malam Yakubu ya tafi Lafiyan Barebari amma bai yi yaki da su ba, kuma a kan hanyarsa ta zuwa Lafiyar ne ya yi sansani a bukur, amma bai yi yaki da su ba, bisa umarnin Shehu Usman dan Fodiyo wanda ya ce masa kada ya yaki bukur. Malam Yakubu ya yi yaki da Dass amma bai ci ta da yaki ba, domin yana cikin yaki da su ne, Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ya yi masa umarnin ya tafi ya tsare Shehun Borno.
An yi yaki da Habe Lago da Darazo, amma Malam Yakubu bai je yakin Darazo ba ya tura Zaginsa ne Abasama ya je ya ci su da yaki. Kuma Malam Yakubun ya ba Abasaman sarautar kasar Darazo, kuma zuriyarsa ce har yanzu ke sarauta. Yakin Malam Yakubu na karshe shi ne yakin Tiffi (a kasar Ningi), yakin na rana daya ne aka yi shi a inda Ningi take yanzu.
Rabon kasa:
1. Madaki Hasan: Bayan Sarkin Bauchi Malam Yakubu ya dawo sansaninsa daga Lafiya ne ya fara raba wa hakimansa kasa. Ya sa Madaki Hasan ya zauna a Wase ya wakilce shi a fuskar Wase da Shendam da dai duk kasar ta fuskar Kudu mai nisa wadda ta kai har bakin Benuwai da Lafiya.
2. Galadima Faruku: Da Sarki Yakubu ya dawo Bauchi, sai ya ba Galadima abin da ya kama daga Miri zuwa kasar Zungur da Gwardin da Duguri da dai kasar ta fuskar Kudu, kusa da Bauchi.
3. Sarkin Yaki Muhammadu Kusu: Sarkin Bauchi Yakubu, ya ba daga Zaranda zuwa Toro zuwa Rahama da inda ake kira Ningi a yanzu wato ta fuskar Yamma.
4. Wambai Abdu: Sarki ya ba shi kasar Galambi duka wato fuskar Gabas da ke kusa da Bauchi, wannan ya hada da kasar Ganjuwa da Lago da Yautare.
5. Ajiya Hammadi: Sarki ya ba shi kasar Bununu da bogoro da Lere da kuma sashin Angas.
6. Sarkin Yara Ibrahim: Sarki ya ba shi fuskar Gabas maso Arewa wato Kuna da Kubi da wani sashi na Darazo.
Wadannan su ne Sarkin Bauchi Malam Yakubu ya fara ba su kasa. Bayan yakin Kanembu (Kalumbu) da aka kashe Madaki Hasan, sai Sarkin Bauchi Yakubu ya nada Sarki a Wase ya ba wani kanen Madaki Hasan mai suna Abdu, ya maido sarautar Madaki nan Bauchi aka ba Fulanin Ganjuwa. Sabon Madaki aka ba shi kasar da Sarkin Yara Ibrahim ke kula da su. Idan aka lura zuriyar Madaki Hasan su suke sarautar Wase (ta Jihar Filato) har yanzu.
7. kasar Kirfi an raba Fulanin kashi biyu. Malam Badara aka ba shi kasar Badara hade da sarautar Iyan Bauchi. kasar dewu aka bai wa dan uwan Malam Badara mai suna Bargi, aka yi masa sarautar Bauchin Bauchi. Haben kasar Kirfi suna hannun Sarkin Kirfi domin ba a yi yaki da shi ba.
A zamanin Sarkin Bauchi Ibrahim an ce kasashe da dama sun yi tawaye, saboda haka bai yi yaki na bude kasa ba, sai dai ya yi kokarin kwantar da tawayen a wasu wurare. Kuma ya kai manyan hakimai zuwa wasu wurare inda za su tsare tawaye, kamar Sarkin Yaki an kai shi Lame, a baya yana Gumau ne. Sai Madaki aka kai shi Kafin Madaki, shi Sarkin kansa ya koma Rauta (zaman Ribadi) domin tsare tawayen Ningi. Galadima aka kai shi Gigyara domin tsare tawayen Duguri. A gabas da Kafin Madaki kuma an kai Dawakin Bauchi domin lura da Miyawa da sauran Haben da suke wurin.
Idan aka lura za a ga in ban da Malam Yakubu babu wanda ya fi Ibrahim aiki a cikin sarakunan Bauchi. Da ya ga kasa ta zauna lafiya bayan shekara 37 yana mulki, sai ya yi murabus ya bai wa dansa Usmanu sarauta, inda shi kuma ya shekara shida a kai.
Sarautar Usmanu ta hadu da rashin yardar wani baappansa Malam Halilu, inda abin ya janyo aka yi yaki na kwana daya a cikin garin Bauchi, aka kashe Halilu da kanensa Sa’idu. A lokacin Sarkin Bauchi Ibrahim (murabus) yana da rai a can Rauta, sai bayan shekara uku da wannan yaki ne Allah Ya yi masa rasuwa.
An tube Sarki Usmanu a Sakkwato kuma ya rasu a kasar Zamfara a wani gari mai suna Danso. Umaru ne ya gaji Usmanu kuma ya shekara bakwai yana sarauta kafin Turawa su cire shi su kai shi Ilori inda ya rasu.
Daga Sarkin Bauchi Malam Yakubu zuwa Sarkin Bauchi na yanzu Alhaji Dokta Rilwanu Sulaiman Adamu an yi sarakuna 11 a masarautar Bauchi, kuma masarautar yanzu ta kunshi kananan hukumomi takwas da suka hada da Alkaleri da Bauchi da bogoro da Darazo da Ganjuwa da Kirfi da Tafawa balewa da kuma Toro.
Wannan rubutu wasu takardu biyu da marigayi Alhaji Kawu Yakubu Lame Jami’in Watsa Labarai na Masarautar Bauchi ya ba ni kan tarihin Bauchi a ranar 11 ga watan Mayun, 1999, ne na sake wa fasali tare da gyara su.