Takaitaccen tarihin Masarautar Gombe

Yadda aka rada sunan garin Gombe Tarihi ya nuna a karni na 14 aka fara sanin garin Gombe, sai dai kafin wannan lokaci an yi wadansu mutane masu karama da sarauta da ake kira ‘Soninke Mandigos’, wadannan mutane su ne suka samar da tsatson garin Gombe, kuma littafin ‘Tarekh-el- Sudan’ (Tarihin Kasar Bakake) na musu […]

Takaitaccen tarihin Masarautar Gombe

Mai martaba Sarkin Gombe Alhaji Abubakar Shehu Abubakar

Yadda aka rada sunan garin Gombe

Tarihi ya nuna a karni na 14 aka fara sanin garin Gombe, sai dai kafin wannan lokaci an yi wadansu mutane masu karama da sarauta da ake kira ‘Soninke Mandigos’, wadannan mutane su ne suka samar da tsatson garin Gombe, kuma littafin ‘Tarekh-el- Sudan’ (Tarihin Kasar Bakake) na musu lakabi da ‘Fararen Shugabanni’.Wadannan mutane ana kuma kiransu da ‘Kaya- Manga’. Sun mulki yammacin Sudan na wasu karnoni da dama. A cikin Kaya-Manga an samu wani mutum da ake kira Bin-Kaya Mob, wanda sarki ne a wata masarauta da ake kira Mande, a yammacin Sudan din, wanda kuma wannan sarki ya ci zamaninsa a cikin karni na 10.

Sarki Bin-Kaya Mob yana matukar ji da jikansa Bin-Abubakar, wanda har ta kai ko kuda ba ya so ya taba shi. Ya mayar da shi dan lelensa kuma shafaffe da mansa. Hakan ce ta sanya Kaya Mob ya bai wa jikansa wani bangare na masarautar tasa da ake kira Ukuba. Bin-Abubakar kaka ne ga Aliyu Ukuba, wanda shi kuma yake mahaifi ga Usman. Aliyu Ukuba shahararren malami ne, ya haddace Alkur’ani, wanda daga baya aka hada shi aure da ’yar gidan wani attajiri a garin Tibati, inda kuma suka haifi Usman.

A nemi Jaridar AMINIYA don samun cikakken rahoton.