Takaitaccen tarihin Sarakunan Fulani na Kano (3)
A makon jiya mun kawo muku ci gaba da takaitaccen tarihin sarakunan Fulani wadanda suka fara mulkar kasar Kano daga jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo kawo yau, kamar yadda muka samo daga shafin rumbun ilimi. To yau za mu dora daga inda muka kwana kamar haka: Abdullahi Bayero dan Abbas (1926 zuwa 1953) Miladiyya […]
A makon jiya mun kawo muku ci gaba da takaitaccen tarihin sarakunan Fulani wadanda suka fara mulkar kasar Kano daga jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo kawo yau, kamar yadda muka samo daga shafin rumbun ilimi. To yau za mu dora daga inda muka kwana kamar haka:
Abdullahi Bayero dan Abbas (1926 zuwa 1953) Miladiyya
Sarki Abdullahi Bayero shi ne Sarki na 53 a jerin Sarakunan Kano kuma Sarki na 10 a jerin Sarakunan Fulani. Sannan kuma Sarki na 3 da Turawa suka naɗa. An naɗa Sarki Abdullahi Bayero a matsayin Sarkin Kano ne lokacin yana Ciroman Kano. Shi ne farkon Ciroman Kano da ya zama Sarki. Sarki Abdullahi Bayero mutum ne mai haƙuri da kuma tattalin jama’arsa.
A zamanin Sarki Abdullahi aka kammala aikin ruwan famfo da aka jawo daga Kogin Calawa zuwa Gwauron Dutse sannan aka rarraba shi zuwa unguwanni da gidaje. Sannan a zamaninsa aka kammala aikin wutar lantarki. A zamaninsa aka kammala ginin Asibitin Shahunci. Sannan a zamaninsa aka gina Makarantar Midil ta Kano wadda ta koma Kwalejin Rumfa. Wannan makaranta tana nan a kan titin zuwa Jami’ar Bayero daga Gidan Murtala. Tana nan tana kallon katangar badala da ke tsakanin Sabuwar Kofa da Kofar Dan’agundi daidai bakar lamba.
Sannan a lokcinsa aka gina Makarantar Koyon Sana’o’i ta Ƙofar Nasarawa. Sarki Abdullahi shi ya sa aka yi ta ciccike kududdufan da ke cikin birnin Kano saboda kiwon lafiya. Sannan a lokacinsa aka gina Makarantar Aikin Shari’a da ta Koyon Aikin Shari’ar, wato ‘Judicial’ da kuma ‘Law school’. Ita Judicial ita ce ta koma Makarantar Koyon Harshen Larabci (School for Arabic Studies -SAS) da ke Ƙwalli a halin yanzu.
Sarki Abdullahi Bayero ya mulki Kano na tsawon shekara 27.
Muhammadu Sanusi I (1953 zuwa 1963) Miladiyya
Sarki Muhammadu Sanusi shi ne Sarki na 53 a jerin Sarakunan Kano, sannan Sarki na 11 a jerin Sarakunan Fulani.
Sarki Muhammadu Sanusi babban malamin addini ne kuma sufi. Mutum ne marar tsoro, managarci, sannan masanin addini. Da hawansa karagar mulkin Kano ya fara da tsarkake Masarautar Kano daga ƙazantar giya da sata da kuma karuwanci. Sarki Muhammadu Sanusi shi ne Sarkin da ya riƙa zartar wa mashaya giya haddi a sarari, karuwai kuma yana tsare su a gidan kaso, su je su yi idda bayan gama iddarsu sai kuma su yi aure; idan sun samu miji. Samun wannan miji shi ne belin karuwa.
A zamanin Sarki Muhammadu Sanusi an ƙara gina wasu makarantu da asibitoci da dai sauran kayan more rayuwa. A lokacinsa aka gina Makarantar Babbar Firamare ta Birnin Kudu a 1954, sannan a zamaninsa aka giggina makarantun U.P.E. a wasu unguwannin Kano uku da suka haɗa da Jarƙasa da Makafin Dala da kuma Kurawa a 1960. Sannan a zamaninsa aka gina Makarantar Horar da Malamai (Kano Teachers College) a 1957. Sannan a zamaninsa aka gina katafaren Asibitn Kashi na Dala. Da sauran muhimman ayyuka da aka gudanar a zamaninsa.
Muhammadu Inuwa Abbas (1963)
Sarki Muhammadu Inuwa shi ne Sarki na 54 a jerin Sarakunan Kano, sannan Sarki na 12 a jerin Sarakunan Fulani. An yi masa sarautar Kano lokacin yana riƙe da muƙamin Turakin Kano. Sannan ya yi hakimi a Bichi, da kuma Gundumar Minjibiri wacce ta haɗa da Kunya da Kuru kafin zamowarsa Sarki.
Sarki Muhammadu Inuwa Abbas bai yi tsawon zamani a kan karagar mulkin Kano ba. Ya yi sarauta ta tsawon wata shida kacal. Ya rasu a 1963. Allah Ya jiƙansa, amin.
Sarkin Kano Ado dan Abdullahi Bayero (1963 Zuwa 2014)
Alhaji Ado Bayero. Shi ne Sarki na 55 a jerin Sarakunan Kano kuma Sarki na 13 a Sarakunan Fulani. Tun daga farkon sarautar Kano zuwa yau (2017), marigayi Alhaji (Dokta) Ado Bayero shi ne Sarkin da ya fi kowane Sarki daɗewa a kan karagar mulkin Kano. Sarkin ya mulki Kano na tsawon shekaru 51 tun daga 1963 har zuwa 2014.
Tsohon ma’aikacin banki, Wakilin Doka, ma’aikacin Hukumar En’e (NA), kuma tsohon Wakilin Najeriya a kasar Senegal. An samu daraja da martabar Masarautar Kano ta ɗaukaka a iya tsawon mulkinsa.
An haifi Alhaji Ado Bayero a ranar 25 ga Yunin 1930 (Wikipedia, 2014; Mahmood, 2014; Umar, 2008). Shi ɗan Sarki Abdullahi Bayero ɗan Sarki Muhammadu Abbas ɗan Sarki Malam Ibrahim Dabo, Bafullatani kuma Basulluɓe. Sunan mahaifiyarsa Hajiya Hasiya.
Tasowarsa
Marigayi Alhaji Ado Abdullahi Bayero, ya fara karatunsa na addini tun yana ƙarami kamar yadda aka saba. Sannan daga baya aka saka shi a makarantar Midil ta Kano, kuma ya samu nasarar zarcewa zuwa Makarantar Koyon Larabci ta Kano (SAS) inda ya kammala a 1947. Ya kuma halarci Kwalejin Horar da Akawu-Akawu ta Zariya wadda ta zama Sashin Mulkin na Jami’ar Ahmadu Belleo da ke Zariya a 1952.
Ayyukan da ya yi
Kafin zamowarsa Sarki, Ado Bayero ya yi aikin banki da The Bank of British West Africa har zuwa 1949, inda daga nan ya zarce Hukumar En’e (Natibe Authority) a matsayin Akawun Majalisa. A 1954 kuma aka zaɓe shi a matsayin dan Majalisar Jihar Arewa da ke Kaduna. Daga kan wannan muƙamin kuma aka yi masa Wakilin Doka na Kano tun daga 1957 zuwa 1962. Sannan ya zama Wakilin Najeriya a Kasar Sanagal muƙamin da yana kansa aka yi masa Sarautar Kano.
Zamowarsa Sarki
Alhaji Ado Abdullahi Bayero, ya zamo Sarkin Kano ne a 1963. Shi ne sarkin Kano na 55, sannan Sarki na 13 a jerin Sarakunan Fulani.
Gudunmawar da ya bayar
Alhaji Ado Bayero ya bayar da gagarumar gudunmawa da ba zai yiwu a ƙididdige ta ba. Shi ne Sarkin da Kano ta zama jiha a hannunsa. Ya yi zamani da gwamnoni 15 kuma ya yi aiki da shugabannin ƙasa 13. Ya ga canje-canje iri-iri. Da bakinsa yake cewa, “Da mu muke yi, aka zo ana yi da mu, yanzu kuma sai an yi a gaya mana.” (Mahmood, 2014).
Sarki Ado Bayero ya ciyar da Kano gaba, kama daga taimakon ɗaiɗaikun mutane; dalilin da ya sa ake yi masa kirari da ‘Baya goya marayu, Uban marasa uba,’ har zuwa kan ƙungiyoyi da gina masallatai da makarantu da sauran ayyukan alheri masu dambin yawa. Bari mu leƙa Umaru (2008), mu ɗan tsakuro:
- Kira zuwa ga addinin Musulunci da tsayar da ibada da musuluntar da waɗanda ba Musulmi ba.
- Gina masallatai da makarantun Islamiyya a cikin birni da ƙauyukan Kano.
- Nuna soyayya ga malamai da masu wa’azi da sauran masu yi wa addini hidima.
- Bada goyon baya ga aiwatar da shari’ar Musulunci da ƙarfafa aiki da ita da zartar da hukunce-hukunce bisa tafarkinta daidaitacce.
- Sake gina katangar gidan Sarki da duwatsu da siminti.
- Lulluɓe titunan cikin gidan Sarki da tayil mai kyau.
- Sake gina gidajen Wambai da Galadima da Waziri da gidajen hakimai da ke ƙananan hukumomi.
- Wadata hakimai da ababen hawa.
Rasuwarsa
Alhaji Ado Bayero ya mulki Kano na tsawon shekara 51. Ya rasu a ranar 6 ga Yunin shekarar 2014. Ya rasu ya bar ’ya’ya maza 31 da ’ya’ya mata 30. Allah Ya jiƙansa da rahama, amin.
Mun ciro wannan rubutu ne daga shafin Rumbun Ilimi wato https://rumbunilimi.com.ng/masarautu.html