Takaitaccen tarihin sarakunan Haɓe na Kano (3)

A makon jiya mun kawo muku tarihin Sarki Nawata da Gawata da Yusa dan Giji-Masu da Naguji dan Dariki da Guguwa dan Giji-Masu da Shekarau dan Dariki da Tsamiya dan Shekarau. A yau za mu tashi daga kan Sarki Usmanu Zamna-Gawa, Sarki na Goma (10) a jerin sarakunan Habe wanda ya mulki Kano  daga 1343 […]

Takaitaccen tarihin sarakunan Haɓe na Kano (3)

A makon jiya mun kawo muku tarihin Sarki Nawata da Gawata da Yusa dan Giji-Masu da Naguji dan Dariki da Guguwa dan Giji-Masu da Shekarau dan Dariki da Tsamiya dan Shekarau. A yau za mu tashi daga kan Sarki Usmanu Zamna-Gawa, Sarki na Goma (10) a jerin sarakunan Habe wanda ya mulki Kano  daga 1343 zuwa 1349 Miladiyya:

Sarki Usmanu Zamna-Gawa (1343 – 1349 Miladiyya)

Usmanu shi ne Sarki na Goma a cikin jerin sarakunan Kano. Sunan mahaifiyarsa Kumaryaku. Ya samu wannan suna na Zamna-Gawa ne saboda kisan Tsamiya da ya yi, sannan ya kulle ƙofar ya zauna a cikin gida tsawon kwana bakwai. Lokacin da ya fito ba a san yadda ya yi da waccan gawa ba. Binne ta ya yi? Cinye ta ya yi? Ba wanda zai iya ɗorar da labari, sai shi sai Allah Masanin abin da ke ɓoye da na bayyane. Ya mulki Kano na tsawon shekara bakwai.

Yaji ɗan Tsamiya (1349 -1385 Miladiyya)

Sarki Yaji shi ne Sarki na Goma Sha Daya a jerin sarakunan Kano. Asalin sunansa Ali, saboda zafin zuciya da yake da ita shi ya saka ake kiransa da Sarki Yaji. Shi ne ya kori Sarkin Rano daga Zamna-gaba. Ya zauna a Bono tsawon shekara biyu. Sannan ya tafi Kura ya zauna tare da Ajawa da Warjawa da Arawa. A lokacinsa ne Wangarwa suka zo Kano suka Kawo Musulunci.

Sarki Yaji ya karɓi Wangarwa hannu bibbiyu, a hannunsu ya karɓi Musulunci. Sannan ya gina musu masallaci a wancan gurbin da ya karya gunkin Tsumburbura (Yankin Dala ke nan). An ce Sarkin Gazarzawa wanda ɗaya ne daga cikin Maguzawan da suka saura, yakan ɗebi jama’arsa kullum da dare su je su yi najasa (kashi) sannan su goga a jikin masallacin. Ganin haka ya sa Sarki ya sanya mai gadi amma ba su daina ba. Sukan je su yaudare shi. Ba su daina wannan mummunan aiki ba har sai da Wangarawa suka yi addu’a Allah Ya makantar da su. Bayan makancewarsa aka tuɓe shi daga sarauta (Sarkin Gazarzawa) sannan aka yi  masa Sarkin Makafi. Wannan ita ce farkon sarautar makafi a Kano.

Haka Sarki ya umarci dukkan jama’ar masarautarsa da Sallah kuma suka bi. Bayan wannan Sarki Yaji shi ya ci Santolo da yaki. Ya roki malaman Wangarawa su yi masa addu’a ya je ya yaki Santolo. A wannan lokaci Santolo ita ce kaɗai babbar kasa da ta rage. Kuma cin ta da yaki zai karya lagon duk wani mai bautar gunki. Hakan kuwa aka yi, jama’ar Wangarwa da Kanawa suka haɗu suka tada runduna mai karfi suka ɗunguma zuwa Santolo. A rana ta farko an wuni ana gwabzawa amma ba wanda ya yi galaba a kan wani. Washegari da fiddowar alfijir sarki ya ɗaura ɗamarar yaki. Suna shiga a wannan rana Allah Ya kawo nasara.

Sarki Yaji ya yi sauratar Kano na tsawon shekara talatin da bakwai. Hakika ya kawo ci gaba sosai a wannan masarauta ta Kano.

Bugayya ɗan Tsamiya (1385 – 1390 Miladiyya)

Bugayya shi ne Sarki na Goma Sha Biyu a jerin sarakunan Kano. Sunansa na asali shi ne Muhammadu. Shi ne Sarkin da ya kori sauran Maguzawa daga gindin Dutsen Fanisau. Ya ce da su, su watse kuma suka bi. Saboda haka ya zauna a ƙasarsa salin-alin ba wani yaƙi. Ya ci gaba da karɓar haraji a hannun jama’a, ya mulki Kano na tsawon shekara biyar.

Kanajeji ɗan Yaji (1390 – 1410 Miladiyya)

Kanajeji shi ne Sarki na Goma Sha Uku a jerin sarakunan Kano. Asalin sunasa shi ne Ibrahim. Sunan mahaifiyarsa Aunaku. Sarki Kanajeji ya kasance mutum mai fitina, tunda ya hau karagar mulki bai zauna a gida ba. Shi ne Sarkin da ya yaƙi ƙasar Zazzau. Sarki ya haɗa rundunar mayaƙa da kayan abinci aka haɗu a Turunku. Kamar yadda ya zo a littafin Labarun Hausawa da Maƙwabtansu. Amma Gwangwazo (2005) ya ce a Kudan aka fafata. A koma dai ina aka fafata wannan yaƙi, rudunar mayaƙan Kano ba su samu nasarar wannan yaƙi ba. Wannan har ta sa Sarkin Zazzau alfahari yake cewa: “Wane abu ne Kanawan Kanajeji ye?”

Bayan dawowar Sarki da jama’arsa gida da ƙyar, Sarki ya fara neman yadda za a samu galaba a kan Zazzagawa. Sai ɗaya daga cikin ragowar waɗanɗan kafirai ya ba shi shawarar cewa ya rungumi gunki, abin da kakaninsa da iyayensa suka tozarta. Haka kuwa aka yi, Sarki ya bi shawarar Bamaguje. Sai ya tambaye shi “Sanar da ni abin da zan aikata”. Sai ya ce da shi. “Ka yanki wannan reshen wannan itaciya (itaciyar da gunkin Tsumburbura ya taɓa zama),” ya yanki reshenta, ya tarar da macijiya ja a cikin reshen, ya kashe ta ya samu fatarta ya ɗinka huffi biyu da ita. Kuma ya sassaƙa dundufa huɗu da kuntukuru takwas da reshen itaciyar. Ya ɗauka zuwa Ɗanƙwai ya jefa su a cikin ruwa. Ya komo zuwa gidansa ya zauna kwana arba’in, sannan ya koma ya ɗauko su, ya kawo gidan Sarkin Cibiri. Sarkin Cibiri ya ɗinke su da ragowar fatar macijiyar nan, ya ce wa Kanajeji, “Idan kana son kowane abu daga na al’amarin duniya sai ka aikta abin da kakaninmu suka aikata tunda.” Ya ce, “To, sanar da ni, in yi,” Sarkin Cibiri ya tuɓe rigarsa ya ɗaura huffin fatar macijiyar nan, ya gewaya itaciyar nan sau arba’in yana waƙa irin waƙar Barbushe. Haka kuma Kanajeji ya yi.

Bayan aukuwar wannan da shekara ta kewayo, sai Sarki Kanajeji ya fita zuwa Zazzau, ya zauna a Gadas kamar yadda aka wallafa a littafin Labarun Hausawa da Maƙwabtansu. Sai dai, Gwangwazo (2005) ya bayyana cewa bayan waccan ridda (fita daga Musulunci da Sarki Kanajeji ya yi saboda amincewarsa da aikata abin da Sarkin Cibiri ya umarce shi na tsafi), daga baya ya tuba ga Allah. Kuma ya koma cikakken Musulmi. Sannan kuma yaƙin ma a Shika aka fafata shi. Kuma a wajen yaƙin ma shi Sarki Ibrahim Kanajeji ya karanta wannan ayar ya ce, “Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai, sau da yawa Allah Yakan bai wa jama’a kaɗan galaba a kan jama’a mai yawa da ikonsa. Allah Yana tare da masu haƙuri.”

Bayan da Sarkin Kano Ibrahim ya bada umarni rundunarsa suka auka cikin rundunar Sarkin Zazzau Muhammadu Abu, wuri ya kaure, yaƙi ya kai matuƙa.  A wannan yaƙi a 1399 aka kashe Sarkin Zazzau, aka tarwatsa rundunarsa. Aka kama na kamawa, daga baya Sarkin Kano Kanajeji ya zauna a wannan gari na Shika har tsawon wata bakwai ko shekara ɗaya cur a wata ruwayar. Wannan ta saka ake yi masa kirari: “Bakano kere, Kanajeji masha ruwan Shika, hana wankan Kubanni, make-make garin magabata”. Ya yi sarautar Kano ta tsawon shekara ashirin.

Umaru dan Kanajeji (1410 – 1421Miladiyya)

Sarki Umaru shi ne Sarki na Goma Sha Huɗu a jerin sarakunan Kano. Shi ne Umaru ɗan Ibrahim Kanajeji. Sunan mahaifiyarsa Yatari. Sarki Umaru malami ne mai ƙoƙarin aikata addini. Shi almajiri ne a wajen malam Ɗan Kurudumus. Tun yana ƙarami yake karantar da ilimin fiƙihu. Ya yi mulki na tsawon shekara goma sha biyu. Iya tsawon mulkinsa ƙasar Kano ta zauna lafiya shiru, ba tashin hankali, ba yaƙe-yaƙe ba zalunci.

Tarihi ya nuna cewa Sarki Umaru ya yi murabus ne daga gadon sarauta sakamakon wa’azi da wani abonkinsa ya yi masa. Sarki Umaru ya kasance yana da wani aboki tun tasowar yarinta. Sunan wannan abokin Sarki Malam Abubakar. Wata rana, bayan Sarki ya kammala bayar da karatu a gidansa da ke Kabuwaya, sai wannan abokin nasa ya zo ya yi masa sallama ya ce zai fita karatu zuwa Gabas (Borno). Suka yi sallama, Sarki ya yi masa addu’ar sauka lafiya da kuma dacewa da abin da za a je nema da kuma dukkan kariya. A kwana a tashi, bayan wasu shekaru, wata rana Sarki Umaru yana tsaka da bada karatu kwatsam, sai ga wannan aboki nasa mai suna Abubakar ya dawo. Da isowarsa ya tarar ana karatu, ya samu wuri ya zauna tare da kiyaye dukkan haƙƙoƙin majalisin karatu. Bayan da aka kammala karatu dukkan almajirai suka watse, sai ya zama daga Sarki sai wannan baƙo nasa. Sai Malam Abubakar ya yi wa Sarki  gargarɗi yana mai cewa da shi: “Ya Umaru, har yanzu kana son matar nan ma’abociyar yaudara, wacce masu hankali suka ƙi aurarta, da sannu ka ciji yatsarka a kanta, a lokacin da da-na-sani ba za ta yi amfani ba.” Sannan ya ci gaba da yi masa gargaɗi, ya tsoratar da shi duniya, ya kuma gargaɗe shi game da Lahira.

Bayan wasu ’yan kwanaki sai Sarki ya tara dukkan dogarai da  fadawa da duk wani mai ruwa-da-tsaki a fada ya karanta musu wasu baituka na waƙoƙi. Sannan ya sanar da su cewa shi daga yau ya sauka a kan kujerar mulki, zai koma gefe ya ci gaba da karantarwa. Hakan kuwa aka yi, Sarki Umaru ya bar kujerar sarautar Kano a shekarar 1421 Miladiyya. Lokacin yana da shekara arba’in da tara da haihuwa. Bayan shekara bakwai da barinsa gadon mulki, Allah ya karɓi abinSa. An binne shi a maƙabartar Wali Mai-Geza wanda wannan suna ya samo asali ne daga ƙabarinsa kasancewa bayan an binne shi a wannan maƙabarta da damina ta juyo sai geza ta fito ta kewaye kabarinsa. Wannan maƙabarta ita ce maƙabartar Ƙofar Mazugal a yau. Tana nan tana kallon Kasuwar Shanu ta Kano (Kara) wacce ke haɗe da mayanka. Ba nisa tsakaninta da tsohon Kamfanin Buga Jaridun Triumph daga Gabas, sannan  dab take da Ƙofar Mazugal daga Yamma. Ƙarshen katangarta daga Yamma mahaɗa ce (junction). Idan ka dawo Gabas za ka taho Kasuwar Canjin Kuɗi ta Wafa da ke Fagge. Idan kuma ka yi Yamma za ka shiga Ƙofar Mazugal zuwa Gwammaja. Idan Kudu ka ɗauka kuma za ka biyo ta gaban mayanka ka tsallaka zuwa Kasuwar Ƙofar Wambai. Idan kuwa ka yi Arewa za ka wuce ta gaban Filin Dalar Gyaɗa har zuwa Kasuwar Alhazai (Hajj Camp).

Dauda Abu-a-Sama dan Yaji (1776 – 1781 Miladiyya)

Dawuda shi ne Sarki na Goma Sha Biyar a jerin sarakunan Kano. Dauda ƙane ne ga Sarki  mai murabus. Wato Sarki Umaru. Sunan mahaifiyarsa Auta. Ana yi masa laƙabi da ‘Baƙin Damisa’.

A zamanin wannan Sarki aka fara cinikin bayi a Kano. A wancan lokaci ba wata kasuwa a cikin birnin Kano. Sai dai su masu bayin sukan zarga musu igiya suna yawo da su kwatankwacin yadda a yanzu masu sayar da raguna kan yi a lokacin Sallar Layya. Akan gan su suna yawo kwararo-kwararo suna kora ragunansu. Duk mai sha’awa idan suka gifta ta gabansa sai ya tsayar da su  a yi ciniki. To haka su ma masu sayar da bayin suka rika yi. Bambancin kawai shi ne cewa a wancan lokacin idan fataken bayi suka fito daga ƙasashe irin su Katsina, Zazzau, Damagaran, Daura, Hadeja da sauran wurare, sai su samu dillali ɗan gari. Sai su zarga wa bayin nan igiya mai ’yar tazara da juna da ake cewa ‘zarara’. Idan mai sha’awa ya gani sai a daidaita. A wancan lokacin ba kuɗi sai dai sukan yi cinikin nan ne da ake cewa ‘ban gishiri in ba ka manda’. Wato ka bada wani kaya kai ma a ba ka wani irin kayan daban. To a wancan lokacin a kan sayi bayi ne da dawaki, ko kuma wani abu daban. Akan karɓi dawaki uku ko huɗu a madadin bawa ko baiwa ɗaya.

Sannan a lokacinsa ne wani ƙasaitaccen hakimi ya yiwo ƙaura daga Borno zuwa Kano. Wannan hakimi sunansa Dagaci. Kuma a wancan lokaci ne aka sauya wa Ƙofar  Adama suna zuwa Ƙofar Dagaci saboda shigowar wannan hakimi ta wannan kofa. An yi wannan a 1425 Miladiyya.

Bayan shekara goma sha bakwai Sarki Dauda yana kan gadon mulki, sai Allah Ya saukar masa da wani zazzaɓi mai zafi wanda har ta kai ba ya iya fitowa. Sarki Dauda ya yi wannan zazzaɓi na tsawo mako biyu, inda daga ƙarshe ya rasu. Ya rasu yana da shekara sittin da uku a duniya.

Mun ciro wani sashi na wannan rubutu daga: Adamu M. U. (2007). Kano Ƙwaryar Ƙira Matattarar Alheri Littafi na Ɗaya. Kano Daga Dutsen Dala. Kano Gobernment Press, Kano.

Dokaji A. A. (1958). Kano ta Dabo Cigari. Published by The Northern Nigerian Publishing Company, Zaria. Printed at Oyeleke Jet-age Printers Limited, Kaduna. Da kuma shafin intanet.