Takalma sun kayar da ’yar fim a dandamalin rawa

Wata ’yar fim a Ghana, Jocelyn Dumas ta sha kunya a gaban mutane, a yayin da ta fadi rica a dandamalin rawa a farkon makon nan.’Yar fim din, wacce kwararriyar ma’aikaciyar talabijin ce ta amsa gayyatar kalubalen da dan wasa Denrele ya yi wa mahalarta bikin kaddamar da kafar watsa labarai ta ‘Channel O News’ […]

Takalma sun kayar da ’yar fim a dandamalin rawa

A hagu, Derenle ne yake taimaka wa Jocelyn, jim kadan da sanya manyan takalman nasaWata ’yar fim a Ghana, Jocelyn Dumas ta sha kunya a gaban mutane, a yayin da ta fadi rica a dandamalin rawa a farkon makon nan.
’Yar fim din, wacce kwararriyar ma’aikaciyar talabijin ce ta amsa gayyatar kalubalen da dan wasa Denrele ya yi wa mahalarta bikin kaddamar da kafar watsa labarai ta ‘Channel O News’ da aka gabatar a Ghana a ranar Litinin da ta gabata.
Kamar yadda aka san shi da al’adar sanya manya-manyan takalma, masu nauyi, Derenle ya kalli ’yan wasan da ke zauren taron ne, ya kalubalance su da cewa, idan akwai wanda zai iya rawa da takalmansa, to ya fito ya gwada. Shi ne fa ita Jocelyn ta fito ta kakaba takalman, ta fara daga kafa da kyar. Sannan ta hau dandamali ta fara taka rawa. Kafin ka ce wani abu, sai ga ta rica a kasa, ta fadi.
“Kai Derenle, ta yaya kake tafiya da takalman nan?” Tambayar da ’yar wasan ta yi masa ke nan cikin mamaki, a yayin da ya tallafa mata ta tashi tsaye.