Takara a tutar indifenda
Tsohon Shugaban kasa, marigayi Umar Musa ‘Yar’adua ya taba furtawa a shekarar 2007, cewa zaben da aka yi masa na cike da kura-kurai, kuma a sakamakon haka ne ya kafa wani kwamiti a karkashin tsohon Babban Jojin Najeriya, Mai Shari’a Muhammad Uwais don ya nazarci hanyoyin gudanar da zabubbuka a kasar nan da niyyar gano […]
Tsohon Shugaban kasa, marigayi Umar Musa ‘Yar’adua ya taba furtawa a shekarar 2007, cewa zaben da aka yi masa na cike da kura-kurai, kuma a sakamakon haka ne ya kafa wani kwamiti a karkashin tsohon Babban Jojin Najeriya, Mai Shari’a Muhammad Uwais don ya nazarci hanyoyin gudanar da zabubbuka a kasar nan da niyyar gano wurren da ke da tangarda ko cikas, ya kuma kawo shawarwarin warware su.
Wannan kwamitin ya kawo shawarwari da yawa, kuma masu ma’ana wadanda idan da an yi aiki da su a wancan lokacin da an kai ga nasarar yin muhimman gyrarrakin da za su sa zabubbuka a kasar nan yin armashi, duk kuwa da cewa an yi amfani da wasu wajen gyara kundin tsarin mulki a shekarar 2010. Shi ya sa har gobe a ke ta yin wadari cikin duhu a kasar nan game da gano dabarun gudanar da zabubbuka bisa ingantattun hanyoyi, sa’annan kuma sakamakonsu su ya zamanto karbabbu ga daukacin al’ummomin kasar nan.
To amma duk da haka nan ana iya cewa an kusa kai wa ga haka a wani yunkuri da Majalisun Dattijai da ta Wakilai suka yi wajen yin gyararraki ga kundin tsarin mulkin kasar nan, inda suka sanya wasu muhimman abubuwa guda biyu game da harkokin zabe cikin shawarwari fiye da talatin da uku da suke so a yi amfani da su don yin gyara ga kundin tsarin mulkin 1999. Wadannan batutuwan kuwa za su iya kawar da wasu al’amuran da ke janyo hayaniya a dukkan lokutan da aka zo zabubbukan cikin jam’iyyun siyasa don fitar da ‘yan takara a matakai daban-daban.
daya daga cikin batutuwan kuwa shi ne na rage yawan shekarun takarar shugabancin kasa da na gwamnoni da kuma na majalisu da shekaru biyar-biyar kamar yadda a yanzu haka suke kunshe cikin kundin tsatin mulkin 1999. Yin haka zai iya bayar da dama ga sabbin jini tsayawa takara maimakon wadanda suke cewa sun ga shekaranjiya waccan, aka kuma yi da su shekaran jiya, ake kuma damawa da su a yau, ba su kuma gaji ba da yin babakere a madafun iko ba. Matasa za su so su ma a ba su damar bayar da tasu ‘yar gudummawar wajen raya kasa da ciyar da harkokin siyasa gaba. To, idan har aka kai ga yin irin wannan gyaran a kundin tsarin mulki za su samu damar yin rawar gaban hantsi, a kuma ga irin kamun ludayinsu da kuma iyakar gudun ruwansu da yadda za su fafata da tsohon hannu maganin kurtu.
Batu na biyu kuwa shi ne amincewar da ake kokarin yi wa duk wani mai sha’awar tsayawa zabe fitowa a matsayin indifenda, watau ba a karkashin wata jam’iyyar siyasa ba don gwada farin-jininsa ko kuma a ce sa’arsa a wajen masu jefa kuri’a.
A halin yanzu jam’iyyjn siyasa ne dai ke da ikon gabatar da ‘yan takarar da za su fafata a dukkan zabubbuka, kuma jama’a na kuka da haka saboda ganin cewa shugabannin jam’iyyun na kama-karya ko kuma dauki-dora da biye son zukatansu yayin gudanar da zabubbukan fitar da ‘yan takara. Watau dai ba a ba talkawa wanda suke darjewa don tsaya masu takara, ko kuma a ce ana dakile dan siyasa mai farin jinin jama’a wanda ke da dimbin magoya baya, a hana shi tsayawa a karkashin jam’iyyar da yake so, ko kuma wacce ‘ya’yanta suka tsaya masa.
Wannan al’amarin ne ke gurbata tsarin dimokuradiyyar da ake aiki da ita a kasar nan, domin ta haka ne za a zazzabi shugabanni bara-gurbi, ko kuma je-ka-na-yi-ka, wadanda ba su iya sauke nauyin da za a dora masu. Shi ne kuma ke haddasa rikice-rikice a cikin jam’iyya har hakan su kai ga zaizayewar ‘ya’yanta idan an muzguna musu, ko kuma su yi abin da ake kira anti-party, watau su taimaka wajen kayar da dan takarar da shugabannin jam’iyya suka mayar dan lele.
Muddin za a kai ga amincewa da shawarar gyara ga kundin tsarin mulki domin nan gaba a cusa batun damar da ‘yan takara tsayawa ba a karkashin tutar wata jam’iyya ba sai dai ta kashin kansu, to za a yi maganin tashin-tashina da fitintinun da kan iya biyo bayan zabubbukan da jam’iyyun siyasa ke yi don firfitar da ‘yan takara, abin da ake danganta shi da barin da ba a iya kwashewa duka. Baicin haka nan kuma hakan zai ba wanda duk aka muzgunawa a zaben fitar da dan takara ya ja daga can a wani gefe, ya ce zai tsaya daga shi sai halinsa, idan har yana takama da jama’ar da ke nuna masa goyon baya. Ka ga idan aka kai ga haka sai a yi wasa irin na mai macijin tsumma: ‘yan kallo lafiya, mai wasa kuma lafiya.
Baicin haka nan kuma wannan tsarin zai yi maganin wani al’amarin da ke ci wa dukkan ‘yan siyasa tuwo a kwarya, domin kuwa shi ne masomin rashawa da cin hanci a dukkan al’amuran siyasa, watau zaben wakilan da ake kira delegates, wadanda su ne ke da ‘yancin zaben ‘yan takara, musamman ma na zaben gwamna ko kuma na shugaban kasa. Wadannan kuraye ne, baki bude, kuma sai wanda ya fi lale musu daloli ne za su ba kuri’arsu, ba ruwansu da ‘yanci sai dai Naira. Shi ya sa zabubbukan fitar da ‘yan takara ba su nuna ainihin yadda ra’ayin jama’ar gari yake sai dai na masu buhunan dukiyar da ke fitar da kudi, magana kuma ta kare nan take.
Idan kuma har an kai ga nasarar ba ‘yan takara tsayawa a tutar indefenda, sai kuma a kokarta a yi gyara a kundin dokokin zabe ta yadda za a kawar da batun zaben delegates a kanana da manyan tarurrukan jam’iyya don firfitar da ‘yan takara, a koma tsarin da ake gani zai fi kwantar da hankulan jama’a na yin zaben ‘yan takara bisa tsarin ‘yar-tinki, watau kato-bayan-kato, domin ta haka ne kawai za a ba jama’a damar darje wanda suke so ya tsaya musu a falle daya, ba wai sai su bi ta hawan-hawa ba, ana zaben wanda za su azurta kawunansu kawai ba tare da la’akari da abin da jama’a ke so ba. Bayar da dama ga ‘yan takarar indefenda ce kadai farar dabarar da za ta magance illolin ‘yan siyasar da ake kira delegates, domin kuwa wayo ma na san na-ki.