Takarar 2023: Buhari ya umarci Gwamnan CBN ya ajiye aiki
Emefiele da akalla ministoci shida ne da sauran masu mukaman siyasa ne suka fito takara a zaben 2023
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin Hukumomi da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da ke son tsayawa takara a zaben 2023 su ajiye mukamansu.
Umarnin Buharin, ya shafi Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, da ke neman kujerar shugaban kasa, gami da jakadu da sauran masu rike da mukaman siyasa a matakin Gwamantin Tarayya.
- 2023: PDP ta jingine karba-karba a kujerar shugaban kasa
- Dole su Amaechi da Ngige su ajiye aiki cikin kwana 5 —Buhari
“Shugaban Kasa ya lura akwai mambobin Majalisar Zartarwa ta Kasa da Shugabannin Hukumomi da Ma’aikatun Gwamnatin Tarayya da Jakadu da sauran masu rike da mukaman siyasa da ke son tsayawa takarar shugaban kasa ko gwamna ko majalisar dokoki.
“Saboda haka yake umartar masu rike da irin wadannan mukaman da ke son yin takara da su mika takardunsu na ajiye aiki zuwa ranar Litinin 16 ga watan Mayun da muke ciki,” inji sanarwar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya fitar a safiyar Alhamis.
Tuni dai aka tura wa CBN da sauran hukumomin gwamnati kwafin takardar, wadda ta fito bayan umarnin Buhari na ranar Laraba ga duk ministocin da ke son tsayawa takara a zaben 2023 da su ajiye mukamansu, su fuskanci harkar siyasarsu.
Ministocin da wannan umarnin ya shafa sun hada da masu neman kujerar shugaban kasa irin su:
- Chris Ngigie – Ministan Kwadago
- Godswill Akpabio – Ministan Neja Delta.
- Emeka Nwjiuba – Minista a Ma’aikatar Ilimi.
- Ogbonnnaya Onu – Ministan Kimiyya da Fasaha
Akwai kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami, wanda ya fito takarar Gwaman Kebbi.