Takarar 2027 ta fi karfin Atiku —Bode George

Cif Bode George ya ce dan Kudu ne ya dace da takarar zaben shugaban kasa na 2027, amma irinsu Atiku Abubakar ba

Takarar 2027 ta fi karfin Atiku —Bode George

Tsohon Mataimakin Shugaban PDP na Kasa, Cif Bode George, ya bayyane cewa takarar Shugaban Kasan 2027 a Jam’iyyar ta fi karfin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Cif Bode George ya ce Atiku Abubakar bai dace ya fito a 2027 ba, kamata ya yi ya janye wa wani daga yankin Kudu mai jini a jika.

Wannan na cikin sanarwar da George ya fitar ranar Laraba, yana jaddada cewa wajibi ne dan takarar PDP a 2027 ya kasance daga yankin Kudu.

Dalili a cewarsa, shi ne, “saboda yanayin Najeriya da al’ummar kasar da kuma kundin tsarin mulkin PDP.

“A 2027 shekarun Atiku sun kai 81, don haka dole a lokacin dole ya yi koyi da Shugaba Joe Biden na Amurka, ya bar masu tasowa da jini a jika su shige ofishin shugaban kasa.

“Ba ni da wata matsala da Atiku, hasali ma abokina ne, amma idan gaskiya ta zole dole in fade ta; nan da 2027 shekarunsa sun haura 80.

“Ni dai da na haura shekaru 80, wane mulki ko mukami zan tsaya nema? Shi ma Atiku abin da ya kamace shi ke nan.

“Kwanan dai mun dai ga yadda Shugaba Joe Biden na Amurka ya janye wa mataimakiyarsa Kamala Harris, ta yi takarar shugaban kasa a babban zabe da ke tafe a watan Nuwamba.

“Hakan shi ne dattaku, kuma bin da ya kamata Alhaji Atiku Abubakar ya yi ke nan a 2027.

“Sai PDP ta tsayar da dan Kudu takarar kujerar shugaban kasa,” in ji George, wanda tsohon gwamnan Jihar Ondo ne a zamanin mulkin soja.