Takarar Gwamnan Yobe: Alkali ya ki amincewa da maslaha

Alkali, ya shaida wa manema labarai cewa ya hadu da wasu abokan fafatawarsa, kuma hudu sun riga sun sayi fom din.

Takarar Gwamnan Yobe: Alkali ya ki amincewa da maslaha

Usman Baba Alkali

Tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya ki amincewa da batun maslaha ko dauki-dora wajen fitar da dan takarar Gwamnan Jihar Yobe.

Alkali, jim kadan da yanko fom dinsa na tsayawa takarar gwamna a APC, Alkali, ya shaida wa manema labarai cewa ya hadu da wasu abokan fafatawarsa, kuma hudu sun riga sun sayi fom din.

Ya jaddada cewa wannan yana nufin tayin yarjejeniyar da aka gabatar ta gaza, lura da cewar hakan ya ci karo da tsarin Jam’iyyar ta APC.

“Saboda haka na sayi fom din don tsayawa takara, domin dole ne in bi ka’idodin hukumar zabe wadda kuma na yi hakan.

“Babu wanda ya taba nuna mini inda zan sanya hannu ko ma ya nemi in yi magana. Shi ya sa nake gaya muku cewa yarjejeniyar amincewa ta gaza.

“Na fahimci abin da shugaban jam’iyyarmu na kasa ya ce, cewa yarjejeniya tana nufin ’yan takara su hadu su amince su goyi bayan daya daga cikinsu.

“Wannan shi ne ma’anar yarjejeniya, wannan shi ne abin da na ji shugaban kasa shi ma da kansa ya fada. Yanzu da wannan bai faru a Yobe ba, na yanke shawarar ci gaba da burina,” in ji Alkali.

Ya kara bayyana cewa magoya bayansa ya kamata su ci gaba da tsayawa tare da shi su taimaka masa har zuwa lokacin zaben fid-da-gwani, ko zai gudana kamar yadda aka tsara ko a’a.