Takarar Janar Buhari alheri ne ga talaka – Karamba
Tsohon shugaban rusasshiyar Jam’iyyar CPC ta Jihar Bauchi Alhaji Karamba Ibrahim Misau ya ce takarar Janar Muhammadu Buhari alheri ga talakawan Najeriya, domin shi ne ake zaton idan ya karbi shugabancin Najeriya za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Alhaji Karamba Ibrahim ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Bauchi.Ya […]
Tsohon shugaban rusasshiyar Jam’iyyar CPC ta Jihar Bauchi Alhaji Karamba Ibrahim Misau ya ce takarar Janar Muhammadu Buhari alheri ga talakawan Najeriya, domin shi ne ake zaton idan ya karbi shugabancin Najeriya za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Alhaji Karamba Ibrahim ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a Bauchi.
Ya ce, a matsayinsa na sabon shugaban kungiyar (Buhari Support Group) reshen Jihar Bauchi tuni sun kafa kwamitoci daban-daban a kananan hukumomin jihar 20.
Dangane da takarar Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da tsohon Mataimakain Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar a Jam’iyyar APC tare da Janar Buhari, Alhaji Karamba ya ce yana da tabbacin cewa ’yan takarar uku za su mara baya ga duk wanda Allah Ya ba shi nasara a zaben fidda-gwani na jam’iyyar.
Ya ce kashi 85 cikin 100 na talakawan Najeriya sun gaji da Jam’iyyar PDP, don haka zaben shekara ta 2015, PDP za ta dandana kudarta a wajen talakawan kasar nan.
Ya bukaci magoya bayan Jam’iyyar APC su cigaba da hada kansu waje daya domin ciyar da jam’iyyar gaba.